Kusan rabin jikinta a nashi yake kuma wai duk a haka kallo take. Shi yake bata ice cream din wani lokacin da gangan zai dade bai bata ba sai ta tabashi ya duk'o yayi pecking lips dinta kafin ya bata. Tunda take Ramlah bata taba yarda cewar zataji abunda takeji yanzu ba game da Rayyan. Wata irin soyayyarshi takeji har kasan ranta, gata dai tare dashi amma ji take kamar basa tare. Karshe ma kwantar da kanta tayi saman cinyoyinshi ta dago tana kallonshi da murmushi kan fuskarta, "Ka gaji yau ko?" Da tambaya da yar karamar murya.
Aje ice cream din yayi kan side table ya karkato hankalinshi zuwa gareta, ya lura akwai wani banbanci tattare da ita. Dukda damar a cikin wata ukun da sukayi a matsayin matarshi sosai ta chanza ba kamar farko farkon aurensu ba da yau masifa gobe shiri. Amma yau dai kam akwai wani abu da tabbas shi yayi softening heart dinta. "Nagaji sosai ba kadan ba. Abba yazo yau, na fada maki kuwa?"
Dan zaro ido tayi a hankali, "Aa, amma shine Rayyan kaki koda kirani inje in gaida shi? Meya kawoshi?" Tunda sukayi aure basuje Lagos gidan iyayenshi ba amma Abba yazo sau daya shida Muhsin, Ramlah duk ta rude dan yanda taga halin Mommy ta dauka shima hakane amma yanda ya mata kai ka dauka ba shine mahaifin Rayyan ba.
"Meeting yazoyi da board of directors, mantawa nayi kuma har maganarki mukayi." Neman mikewa zaune take ya maida ita kwance yana dariyar mugunta, "Ah kafin ki tambaya baice komai ba, kawai lafiyarki ya tambaya nace kina lafiya, saura kadan nace munada juna biyu." Dariya suka fashe a tare tana maka mashi harara, "Wai kunada juna biyu, wannan cikin nawa ko kan zakara babu balle dan mutum. Ban shirya ba." Kyaleta yayi shikam, dan yanda suka faro abun nan cikin arziki gara an gamashi haka.
Dagowa ta karayi tana kallonshi sai tayi murmushi, "Na maka laifi, zaka hakura?"
Tsayawa yayi yana tunani, shidai tun bayan data tafi gida farkon aurensu bata taba mashi wani sahihin laifi ba. Saidai idan yan rigimarta sun tashi wanda kawo yanzu sarai yasan halin kayanshi. "Ai ba haka ake bada hakuri ba yan mata ko? Me kikayi?"
"Tuntuni na dauka kai kaje kacewa Lubnah baka santa ni kakeso. Naita jin haushinka, ashe I was wrong. Zaka yafe man?" Yanda tayi maganar with utmost sincerity yasa Rayyan tsayawa yana kallonta. Shi ganowar da tayi ba haka abunda yake ba ba shine damuwarshi ba, Aa, yanda tayi tunanin har ta bashi hakuri kan mganar. "To ya akai ta san ke din nakeso?"
Murmushi tayi jin yanda ya furta, 'ke din nakeso' irin ya nuna mata har yanzu dinma bata chanza zani ba, ita dindai yakeso. "Ina last maganan da mukayi a dakinka?" Daga mata kai yayi, "To ashe tazo kawo man wayata Dr na kira taji mu. Shine ma, wai a yanda tace wai taga alamar nima ina sanka to ita kuma tanasan na samu dukkan abunda nakeso a rayuwa, shine fah. Kayi hakuri kaji?" Shi bata hakurin yake ba, sai yanzu ma abun yazo mashi bata taba cewa tana sanshi ba duk wannan cibadadin da akayi.
"Oh wai ne ma? Ba da gasken ba kike sona kenan?" Yar hararar wasa ta mashi tana dauke fuska da murmushi kwance kan fuskarta. "Oho, nidai na aureka ne gani nan dai." Dan daure fuska yayi yana kokarin dagata daga jikinta ta makalkaleshi, "To wai bana baka hakuri ba?" Turbune fuska tayi shima ya bata rai, "Ai ban hakura ba. Ina amfanin hakurin tunda ba wai kina sona bane ba?" Gani tayi da gaske wai fuska yake ita sai abun ma ya burgeta, ba kasafai take ganin fushin Rayyan ba sai ta kaishi makura sosai da sosai. Akwai ranar data bashi haushi yace 'Ramlah sanki da nake yasa bana iya fushi dake, amma duk ranar da nace zanyi fushin gaske dake zamu dade bamu dawo daidai ba.'
"To wai fushin na menene? Ina sanka toh, shikenan?" Can kasan makoshi ta furta maganar, da hanzari ya juyo yana kallonta kafin wani irin kyakyawan murmushi ya bayyana akan labbanshi. "Banji ba, maimaita." Dariya sukayi a tare ya duko da kunnenshi saitin bakinta, "Ina sanka, mijina." Wani irin ihun dadi ya saki wanda duk yanda taso ta danne dariyarta kasawa tayi. Dagowa yayi ya rungumeta tsam cikin jikinshi yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi. Bai taba ba kuma bazai kara san wani mutum ba kamar yanda yake kaunar Ramlah.
YOU ARE READING
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...