Talatin Da Daya

1.4K 191 27
                                    

Wajen da Aasim ya tashi Rayyan ya koma ya zauna, saida ta dan muskuta dan yanda ya wani zauna irin ya nuna ma Aasim din shi bai isa ya zauna gefenta ba amma shi ko yayi hakan ba wani laifi bane ba. Duk wulakancin Mommy tana yinshi ne amma bata isa tama Rayyan ba, sai yasa koda ya gaisheta fuska dakile ta amsashi da yar fara'arta ita Maryam ma abun har mamaki yake bata.

Karshe ma da abun ya cika Aasim ganin yanda suke magana Mommy taki yin rashin mutunci yasa ya mike zai fita daga falon sai yaji Rayyan ya kira sunanshi. "Yanzu shi Mommy Aasim har yanzu bai gama school din ba ko me yake nufi?" Da hanzari Aasim yayi niyyar barin wajen dan duk duniya gara ma Abba ya mishi maganar makaranta akan Rayyan ya mishi. Shine yake bima Rayyan daga nan sai Maryam amma kuma har yanzu yak'i ya natsu yayi karatu. Dan Mommy ne na farko, sai yasa karshen soyayya ta nuna mashi kuma babu wanda ya isa ya fadi laifinshi gabanta in ba Rayyan ba.

"Kai ina zaka? Dawo nan." Wani turnuke fuska yayi ganin yanda ya wani kirashi a dizge. Satar kallon Ramlah yayi yaga amma ita sam hankalinta ma baya wajensu, wasa takeyi da yatsun hannunta dan da ka gani kasan a takure ma take tukunna ya koma ya zauna yana dan zungurin Mommy alamun ta shigar mashi. "Me kake nufi da ka baro makarantar ka dawo gida? Me zakaci a gidan? Ko yanzu ma course din wahala ya maka zaka chanza?" Da fada fada yake magana hakan yasa Mommy yin shiru dan tasan yanzu da tace zata shigar ma Aasim sai masifa iyaka su hau sama su fado kuma abunda beyi niyyar yi mashi din ba yayi.

"Mun samu matsala da supervisor na ne, shine sukayi suspending dina for the whole session." Muryarshi na rawa yayi magana. Shi maganar ma ko hadashi da Abba batayi ba dan yasan Mommy ta gama komai amma Rayyan yanda kasan dutsi, duk biye biyenta baya kamashi.

"Ka samu matsala da supervisor dinka ko kaje kayi abinda kaga dama sun koreka? Aasim ka san me? Dan ubanka university of lagos zan samo maka admission, bazaka dauki mutane sakarkaru ba, kaine daga waccan kasa zuwa waccan ka kusa seven years amma ace har yanzu baka gama degree ba? Zaka gane kurenka."

Mikewa yayi shima Aasim ya bishi a baya yana magana kasa kasa, "Dan Allah kayi hakuri..." ita dai Mommy binsu tayi da ido amma ranta wani tukukin bakin ciki yake. Tunani take wurin wane malamin zata kai Rayyan ne ya fita sabgarta data yaranta? Koda Maryam ta mike tana mata sallama kallon banza bata isheta ba, karshe ma tambayar data so yi akan wacece Ramlah takaici hanata yinta yayi.

Zaune suke a falon, Maryam sai video call take da mijinta wani sa'in har larabci suke hadawa dashi, daga ta hasko mashi fuskar waccan sai ta waccan yaran gashi sai wasa suke su kamar ma yanzu safiya tayi. Cike da burgewa Ramlah take kallonta har ta gama suna hada ido tayi murmushi tace, "Kunji dadi abunku yan gayu, ji magana da larabci wai hankalinku kwance." Ita Maryam ma dariya abun ya bata, saida ta gama dariya tukunna ta dawo ta zauna gefenta, yaran sai dariyar wasa suke ta kira Grace ta daukesu ta masu wankan dare.

Zama tayi gefenta suna yar hira sama sama kafin ta fara magana a hankali, "Wai nikam Ramlah inaso in tambayeki, ta ina kuka hadu da Ya Rayyan?" Tasan dai Rayyan ya mata kashedi akan Ramlah amma ita bazata iya barin abunnan cikin cikinta ba.

Iyakar abunda zata iya fada mata ta fada mata yanda suka hadu da Lubnah da kuma ganinshi da tayi gidansu bayan ta dawo. Kallonta take a natse har ta gama kafin tayi murmushi. "Tsaya, tare daku kuka taba zuwa wani biki Maiduguri ko?" Gulma ce dai ta sani, kuma idan Rayyan ya jita sai ya bata mata rai amma ita abunda ta gani tattare dashi tasan ba haka nan ba.

"Eh, kunyi maganar bikin ne dashi? Munje bikin kawar Lubnah dashi ai." A hankali ta rika bugun cikinta tanajin duk abubuwan da takeso taji. Ita ta san halin Rayyan, bai cika fara san mutum ba, ita bama zata taba cewa ga wadda yaso ba tun bayan budurwarshi a school itama Babanta aure ya mata daga nan kuma ya kulle babin mata to sai yanzu take ganin wadannan alamomin.

Firar duniya suka koma sunayi sai da Ramlah taga kiran Dr Aliyu tukunna ta tafi daki, tana jiyo wasan da Maryam take mata wai surikinsu. Da dariyar maganar ta amsa wayar tana har saida ya tambayeta lafiya? "Ah, nida Maryam daga ganin ka kirani wai ko surikinsu ne? Ko ta ina ka zama surikinsu?"

Murmushi yayi, "To ai fatan alkhairi tayi. Ko bakisan tsoho mai diya?" Ita maganar ma dariya ta bata.

"Waye tsohon? Idan ma maganar tsufa akeyi ai nice tsohuwa, har da diyata fa da yanzu Hanan ta kusa six years." Sautin daya fitar yasa ta fashe da dariya.

"Ba wata tsohuwa kina tsaleliyar budurwa dake. Wai halan baki taba haduwa da wanda yace maki kinada masifan kyau ba? Na tabbatar ni kaina in baccin halin da kikazo asibiti ciki da bazan taba yarda kinada diya ba. Yan mata ce ke sosai ma ba kadan ba."

Dariya Ramlah tayi, "Oh ni Ramlatu wai yan mata, to nagode yan samari, tunda abun ya zama haka."

Shima saida yayi dariyar tukunna ya bata amsa, "To yanzu yaushe zan turo? Dan wannan budurwa da sauri wani zai rigani biyan sadakin ta, na tabbata."

Wasa ta maida abun, duk yanda Dr Aliyu yaso ya lailayo maganar Ramlah kin yarda tayi, karshe dai sai ya kyaleta sukasha fira har saida ya fara bacci tukunna suka kashe da alkawarin gobe idan taje wajen zata mashi video dan shi bai yarda da mazan yarabawan nan ba.

Haka Ramlah tayi bacci sai murmushi take dan ita idan kanasan kaga zallar farin cikinta ta ko tana waya da Dr Aliyu ko ta gama ko hakanan ma idan ya fado mata a rai. Sai can ta samu tayi bacci, dan gobe wajen 11 na safe zasu fara taron dan haka dole ta bar gida wajen karfe 9 na safe.

Sunyi magana tun lokacin dayaje daukota jiya, hakan yasa tana tashi shiryawa kawai tayi ta fito falo, bataga Maryam ba hakan yasa ta tabbatar har yanzu tana bacci, da koda ta kwanta ta jiyo sautin muryarta kamar tana kallo har cikin dare. Fita tayi daga bangaren tanata addu'a Allah yasa kar tayi batan hanya, gashi ko Grace dinma bata gani ba. Saida ta isa bakin kofar bangarenshi tukunna tayi tsaye kasake sai kuma ta tuna cewar sunyi magana yace zaisa a hada mata breakfast data shirya kawai tazo nan.

Kwankwasa kofa tayi ta jita a bude, wanda hakan ma wata alama ce ta cewar ya san zatazo. Kai tsaye falon ta shiga ta zauna sai ta janyo wayarta tana latsawa. Ganin Lubnah online yasa ta mata message, 'Amaryar gobe har an tashi ko? Ko kina wajen aikin ma already ai.'

Ko minti daya ba'ayi ba taga Lubnah na typing, 'Hmm, amaryar gobe ciki ya duri ruwa. Jiya gabana Mama tayi waya da Baban Rayyan...'

Ko kafin messages din su ida shigowa Ramlah tayi hanzarin maida mata, 'Na sani, mutuwa zakiyi ko?' dariya ta fashe da ita, dan tana iya hango fuskar Lubnah a yanzu haka.'

Itama Lubnah emojin dariya ta turo mata, 'Ai nama mutu na dawo. Yanzu meeting zamu shiga, zan dai kiraki ai dole.' Daga haka taga ta sauka, batasan da mutum gefenta ba saida taji ya fizge wayar. "Wayyo Allah!" Da hanzari ta mike itama tana nufar wayarta.

"Gulmar wa ake haka naga tanata dariya?" Wayar yake neman dubawa amma Ramlah duk tunanin ta ya karkata akan wajen amsar wayar nan, dan babu yanda za'ayi ta bari yaga maganar da sukayi.

"Babu kyau leka sirri, Rayyan, dan girman Allah ka bani wayata." Saukinta daya wajen amsar wayar ya danna tayi locking sai ya miko mata wayar har ta mika hannu zata karba ya janye, "Zan baki amma sai kinman alkawari zaki fada man dawa kike chatting da anyin safiyar nan kinata dariya."

Batasan lokacin data balla mashi harara ba yana miko wayar ta karba, "To da dawa zanyi? Da mijina, voicenote diyata tamun shida ita sai naji duk nayi kewarsu." Da muryar shagwaba tayi maganar dan idan kaji sai ka dauka da gasken tanada mijin kuma tayi kewar tashi.

Da dariya yake amma baisan lokacin daya hade fuska ba, ita kam har ta tafi wajen dining table ta zauna ta dauka zai biyota ya zauna. "Akwai abunda zanyi, zan saka driver ya kaiki. Zai kawo motan ta nan wajen idan kin gama yana waje." Ko kallon inda take bai karayi ba ya fita waje, ita kuwa bin bayanshi tayi tana mamakin ikon Allah. Toh daga ita har shi dai sunsan bata da miji amma kuma kowa yasan idan tace mijinta da kuma diyarta to tabbas Dr Aliyu take nufi. Miye na fushin toh? Ita kuma miye na misali dashi? Kuma yanda tayi maganar har ga Allah abun ya kwanta mata a rai, sai taji dama maganar ya zamo gaskia.

Ganin yanayin yanda Rayyan din ya fita yana neman tsaya mata a rai yasa ta saki wani siririn tsaki ta fara tsakurar abinci. A hankali kuma maganganun Dr Aliyu na daren jiya suka fara dawo mata a rai bata san lokacin data tsinci kanta da yin wani kayataccen murmurshi ba.

An dawo💃🏼✨

MIJINA NE! ✅ Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang