Yanda yace din haka akayi, tana gamawa ta fito taga driver din ita yake jira. Motar ta shiga a dardare ta zaune, ko juyowa baiyi ba ya tada motar suka fara tafiya. A zuciyarta sai sake sake takeyi, haka kuma duk yanda taso ta kauda tunanin Rayyan a ranta kasawa tayi, dan dole ta fara tariyo abunda ya faru tsakaninsu yau. Haushinshi ta fara ji daga nan kuma bata san yanda akayi ba sai ta tsinci kanta da tunanin dukkan lokutan da suka kasance tare tun farkon zuwanta Abuja, koda ta tuno dramar su ta airport Ramlah bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba.
Sai kuma tayi guntun tsaki, message ma ta tura ma Dr Aliyu duk dan ta manta da Rayyan a haka har suka isa, daga gani drivern ya san hannunshi dan bata san ta inda sukabi ba amma babu yawan cunkoso a wurin. Suna isa wajen ta tsaya tana kallonshi kamar zata mashi godiya amma sai taga ya buga motar ya tafi. Me yake nufi to? Wa zata kira idan ta gama dan ita daga nan banda kofar shiga wajen to batasan wani wajen ba kuma. Ita kuma yanda suka rabu da Rayyan har ga Allah gara ta kwana wajen nan da ta kirashi ta ce mashi wai ta gama.
Shiga wajen tayi, haka zalika yanda tama Dr Aliyu alkawari tana shiga ta zauna ta fara mashi video din. Daga kashe snap ta shiga ta fara daukar hoto tanayi tana murmushi. Duka ta tura mashi tana fadin ya nuna ma diyarta, daya kuma daga cikin videos din tayi posting a status dinta, ba wasu uban contacts gareta ba inba yanzu da take tarasu ba, amma still tayi posting.
Har aka gama abun hankalinta yana kan maganganun dake wakana, sai wurin ukku na rana suka tashi, wata irin yunwa takeji ga dukda babu zafin rana sosai amma akwai rana. Koda suka fito Allah Allah takeyi Allah yasa taga driver din daya kawota amma taga shiru babu kowa. A dayan hall din taron dake kallon wanda sukeyi ga maganganu nan na fitowa alama akwai wasu masu taron a ciki. Zama ta danyi a kan kujera tana tunanin yanzu miye mafita?
Yunwar dake cikinta ba kadan bace ba tunda abincin ba wani ci tayi ba dan tsakura tayi, sannan gashi ko sallar azahar batayi ba ga la'asar na kunno kai. Lubnah ta kira dan ta bata labari amma bata dauka ba, zaune tayi tsuru tana kallon motocin dake shige da fice cikin wajen har taji muslim pro din dak wayarta ya kira salla alamar lokacin la'asar yayi. Dan zagayawa tayi ta samo fampo tayi alwallah, Allah ya sota dankwalinta babba ne, waje ta samu ta shimfida shi ta gabatar da sallolinta, amma zuwa yanzu karfin jikinta ya kusa karewa. Har biyar na yamma tana wajen zaune, tun tana tunanin zata jure sai taga alamun Rayyan dai nufinshi jira yake ta kira shi.
Da kunkunai ta fara kira wayarshi amma shiru bai dauka ba. Two missed calls ta mishi shiru, ganin har shida na yamma na neman yi yasa ta cigaba da kiranshi babu kakkautawa amma still bai dauki kiranta ba. Tsaki tayi tana mikewa tsaye, gashi ko sunan unguwar ma bata sani ba balle ace ta hau taxi taje gidan. Kuma tayi kuskuren rashin amsar number Maryam da yanzu sai ta kirata.
Hanyar fita daga wajen tayi, dan ita har ga Allah bazata iya zama har maghrib ba wajen nan har ga Allah, ko ba dan yunwar dake cinta ba, wanka takeso tayi kuma tayi bacci. Harabar wajen ta fita daidai lokacin da yan dayan hall din suka fita. Tana lura da wata mota da tazo fita ta dan tsaya kamar zata mata magana sai kuma ta kauda fuskarta gefe, dan ita dai babu wanda ta sani nan wajen balle ace. Tafiya ta farayi a hankali har tazo bakin wani atm, kudi ta cira dukda batasan ko zasu isheta ba ko bazasu isheta ba.
Wata yar budurwa ta gani a bakin atm din itama bayan ta gama cirar kudin, "Hey, good evening," ta fada da dan murmushin ta, dan ita batasan ta ina zata fara ba, gashi tsoronta kar ta fada hannun mugaye.
Da murmushi budurwar ta juyo ta ansata, "Good evening, are you hausa?" Da dariya Ramlah ta ansa mata tana daga mata kai.
Cikin harshen turanci suka fara magana, "Dan Allah nazo wani seminar ne, akwai hotel nan kusa da zanyi lodging? Kuma ko boutique haka wanda zan iya siyen kayan sakawa."
"Akwai, idan bazaki damu ba muje na kaiki." Saida Ramlah tayi yan addu'o'i a zuciyarta tukunna ta taka bakin dalleliyar motar wannan budurwar, daga ganinta kasan yar gayu ce. Suna tafe suna yar fira sama sama, a nan ne take shaida mata cewar lokacin da tana daliba Kano tayi bautar kasarta. Ko kafin su isa shagon siyar da kayan duhu yayi. Ramlah bata tsaya zaben kayan ba, guda aya ta dauka doguwar riga me wadataccen gyale tukunna nan kusa suka shiga hotel din. Daki ta kama har ciki matar ta rakata bayan ta gama nuna mata inda restaurant din hotel din yake zataci abinci. Amsar number juna sukayi tukunna ta tafi Ramlah nata zabga mata godiya.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
MIJINA NE! ✅
Любовные романыAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...