Talatin Da Shida

1.4K 206 13
                                    

Ihun Mommy ya tada shi, juyawa yayi yana tunanin meya faru wannan matar zata shigo mashi part haka? Tun bayan da ya tashi gab da asuba ya dawo bangarenshi, tanata bacci bata lura dashi ba, yanda take baccin kamar wata yar yayi ta harde kanta ya bashi dariya, sanda yayi a hankali har ya bar wajen. Kafin ya mike daga kan gadon saida ya duba lokaci yaga karfe 8:30am, ya akai ta tashi da wuri haka?

Yasan dai maganar bata wuce ta Aasim, fita yayi ya ganta falo sai yan girgize girgize take, shi abun ma dariya ya bashi. "Mommy ina kwana? An tashi lafiya?" Yanda yayi maganar zaka rantse da Allah dama ya saba tashi ya ganta bangarenshi karfe takwas na safe. Ruwa yaje yasha duk tana kallonshi sai kumfar baki take.

"Yanzu what's the meaning of that? Ya zaka saka a kulle yaro cikin daki bayan kasan jikinshi duk ya gama jin ciwo da kwalba? Kashe shi kake sanyi ne, Rayyan?" Bai kulata ba ya nufi hanyar fita, "Tukunna ma, meya maka da zaka mashi duka haka? Naga dai in makaranta ce ai bakai zai ma karatun ba idan yayi ko?"

"Ni bazance maki komai ba a nan, amma idan munje wajen Abba zan maku bayani ku duka. Wajenshi zanje, idan zaki iya biyoni can kiji abunda ya faru toh." Daga haka fita yayi bai kara ko kulata ba. Yanajin kunkunin ta, tafe yake a gaba tana binshi, ita burinta bai wuce ya bata makullin ba taje ta kai Aasim asibiti, tun cikin dare daya farka yake kuka.

Saida suka jira Abba ya sauko kasa, Mommy ce ma da kanta taje ta takura mashi har ya sauko kasan. Kallon Rayyan yayi wanda idonshi cike yake da bacci yana tambayarshi ko lafiya? Yaji Mommy tana fadin wai ya daki Aasim yaji mashi ciwo da kwalba kuma ya kulleshi. Saida Rayyan ya gaidashi cikin girmamawa tukunna ya fara magana, "Abba, ina yarinyar nan dana fada maka munzo zatayi wata seminar? Itafa na kamashi yana neman yi mata fyade. Kuma sai ya nemi yayi kokowa dani ni kuma na zaneshi, shine nace securities su kaishi dakinshi a bani makullin." Mikewa yayi yaje ya aje makullin gefenshi, "Amma ga makullin ma, dan ni yanzu in an hour zan tafi Abuja."

Wata irin kururuwa Mommy ta fasa, wai sharri zaima Aasim. Duka duka yarinyar guda nawa ce? Me ma Aasim zai tsinta jikinta in yace zai mata fyade? Ita ta tabbata karya ake. Abba dan guntun tsaki yaja, "Tashi ka tafi abunka, Rayyan, kaji? Allah ya maka albarka ya tsare hanya." Fita yayi yana jin banbotan da Mommy keyi, shi saiyasa sabgarta bata cika damunshi ba. Ita kuma babban takaicinta bai wuce a komai Abba yana jin maganarta amma banda magana in dai ta shafi Rayyan.

Baiyi tunanin komawa bacci ba dan jirgin karfe goma na safe ya masu booking. Kiranta waya yayi da bacci a bakinta ta amsashi tukunna ya shiga wanka. Zuwa karfe tara da yan mintuna sun gama abunda sukeyi sun dauki hanyar airport, koda ya mata magana akan ko ya tsaya su sayi wani cewa tayi Aa, ai bazai dade ba zasu isa gida sai suci a can.

Shiru sukayi sai can Rayyan ya juyo yaga yanda ta lafe kaman mai bacci amma daga gani kasan ba bacci take ba, tunani ne kawai ya isheta. "Tunanin me kikeyi? Allah yasa ba abun jiya bane yake damunki." Dagowa tayi idanunsu suka hadu kafin ta sakar mashi wani sanyayyan murmushi tana girgiza kai.

Abun ya dameta, tanaso tayi magana da wani. Basu samu sun kara magana da Dr Aliyu ba, ta tabbata aiki ne ya mishi yawa. "Jiya na hadu da Yassar, ka gane shi?" Tsayawa yayi yana tunani, "Abban Hanan..." sai kuma tayi saurin gyara kanta, "Yace dai kama sukeyi, amma ni na tabbata Mijina ne, Rayyan."

Babu alamar kuka a tattare da ita, amma ba sai ta fada ba zaka san cewar ba karamin kunci bane ke cin zuciyarta. Saida yayi yan mintuna yana tuki tukunna ya juya yana kallonta, "A ina kika ganshi? Me yace maki?"

Labarin ta fara bashi a hankali muryarta cike da natsuwa, dukda cewar akwai natsuwar da kunci yake samar da ita kasancewar rashin karfin jiki dana zuciya, wannan natsuwar tata natsuwace ta wanda abu ya faru dashi amma ya gama yarda da alamarin. "Ka tuna na taba fada maka cewar Abban Hanan yana ce man Ramlar Hajia wani lokacin kuma yace man Autar Hajia?" Daga mata kai yayi sai ta cigaba, "To fa har nazo zan shiga motar dan ya maida ni gida kawai sai cewa yayi yauwa Ramlar Hajia...bana neman wani karin bayani, Rayyan, Mijina ne."

MIJINA NE! ✅ Место, где живут истории. Откройте их для себя