Ko kafin ta kwankwasa sai taga kofar ma a bude take, shida tayi tana kaffa kaffa da tray din da yake hannunta har ta ajeshi saman tebur kafin ta dago tana kallon madaidaicin falon. Zata iya irga zuwanta bangaren Rayyan, kuma duk zuwan da zatayi zaman da take bai wuce na minti biyar. Tana shirin kiranshi a waya akan ya fito sai taji motsin mutum kila yaji alamun shigowarta.
Furkarshi har yanzu babu alamun annuri kwata kwata tattare da ita sai taji itama tatta duk ta kara rashin dadi. Mutane biyu da tafi so a rayuwarta duk da alamu suna cikin kunci. Zama yayi, wanda duk kokarin Rayyan akan yaga ya mata murmushi kasawa yayi, saidai itace ta mishi murmushin, "Abinci na kawo maka, kwana biyun nan ka saba kwana da yunwa, Rayyan."
"Allah sarki, kin kyauta kuwa." Tray din ya jawo gabanshi yana budewa, "Sannu kinji? Allah ya miki albarka." Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta. Tasan Mama kusan kullum sai tace mata Allah yayi mata albarka amma jin hakan daga bakin Rayyan ba karamin sanyaya mata rai yayi ba.
Murmushi tayi kafin tace 'Ameen.' Tana kallon yanda ya fara cin abincin cike da natsuwa dukda duk yanda yaso wajen ganin ya boye damuwarshi hakan ya gagara. Kasa jurewa tayi tace "Wai Rayyan me yake damunki? Na lura tun bayan dawowarku Lagos kake dawainiya da wani abu a ranka. Menene?" Kallonshi tayi taga ya tsaya ma da cin abincin nashi, "Dan Allah kar kace zaka boye man, kaji?"
A hankali Rayyan ya dago yana kallonta, shi yasan Lubnah ko tsufa tayi tabbas tana cikin jeran matan nan da suke mutuwa da kyawunsu. Shidai kawai bata mashi ba, Allah bai saka mashi santa ba. Baya ga kyaun da Allah ya mata sai kuma ya bata kyakyawar zuciya da halaye wanda zasuyi wuyar samu a zamanin nan, amma dukda haka baiji yana santa ba. Meyasa zuciyarshi zata mashi haka? Mai yasa zai fada soyayyar wacce bama ta san yanayi ba? Haram ne ma a yanzu yace yana san Ramlah tunda ko babu Yasir, an riga da an saka ranar aurenta da Aliyu.
Idan yace zai cigaba da dawainiya da soyayyar Ramlah tabbas ya cuci kanshi kuma zai cuci matar da zai aura, amma ta ina zai fara? Kullum cikin fada yake ma zuciyarshi akan ta daina wannan wahalalliyar soyayyar amma taki ta daina, karuwa ma san Ramlah yake kullum a ranshi. Da kyar ya samu ya kalato murmushin daya sakarwa Lubnah, "Nagaji ne, Lubnah. Hidindimu sunman yawa, ga shirin biki duk banda natsuwa." Baisan ta inda zai fara ba. Bama wannan ba, bazai taba gaya mata wai Ramlah yake mutuwar so ba koda kuwa ace zai mutu, ya gwammace ya mutu da abunshi a rai, dan koba komai Lubnah bata cancanci haka daga wajenshi ba.
"To stress ne duk zaisa ka zama haka, Rayyan? Kaga yanda ka koma kuwa? Ka rame, idanunka duk sun fada, har baki fa kayi. Ba wani stress Allah, indai da wani abun dan Allah ka fada man."
Yar dariya yayi kafin yasha drink din data kawo mashi, "Ciwon so yake damu na, na kosa a daura auren kowa ya huta." Cak! Zuciyarta ta tsaya, ya lura duk sanda ya mata magana makamanciya data soyayya rasa inda zata saka kanta tayi. Shi idan ba yanzu dayace hakan ba ya manta yaushe rabon da suyi magana irin ta masoya ko wanda suke da shirin yin aure nan da yan satika ba.
Yar dariya tayi da alamar jin kunya kafin ta daga mashi kai, "Naji, banda wannan kuma fah?"
Juyowa yayi yana kallonta, "Inaso na bar kasar nan, ina zamuje honeymoon? Zan duba ma naga idan zan samu aiki wata kasar, akwai mutanen da bansan gani yanzu." Dariya ta fashe da ita. "Ji dan Allah kamar wanda akewa wani mugun abu a nan din? Honeymoon kuma muje maldives, inaso naje amma ban taba zuwa ba. Naga ma suna tallar wani couple package, zan duba mana, ai passport dinka yana nan ko?"
Tsayawa yayi yana kallonta, ita batasan wai koda yaje honeymoon dinba so yake ya gudu daga garin nan dan kar yaga Ramlah da koma waye zata aura? Baiso ya kuntata ma Lubnah ko ya sanyata cikin kunci, hakan yasa yake zullumin auren nan. "Yana nan, idan kin tambayesu da visa da komai sai ki fada man. Nasan halinki yanzu kina iya ceman har ticket kin siya kinyi booking komai."
YOU ARE READING
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...