Allah ya kawo mu karshen Ramadan
Allah ya amsa mana ibadun mu, ya yafe mana kurakuranmu.
Yasa muna cikin bayi yantattu.Eidukum mubarak✨✨
Naso nayi nisa ko na gama typing din gaba daya kapin na fara posting maku amma na fahimci hakan bazeyu ba domin ku ne zaku karpapa mini guiwa domin na cigaba da typing, domin idan babu ku nima babu ni babu abinda zan iya typing, keep encouraging me... God bless y'all
Allah yasa mu amfana ♥♥♥
* * * * * *
Cikin Jihar Gano
Masarautar Gano itace sahun farko cikin manyan masarautu biyar dake kasar tana arewa maso gabas na cikin kasar, yawan arzikin da ke cikin masarautar ya shallake na duk sauran masarautun biyar, source na dukiyar ya samo asali ne daga kasuwanci da suka ta'allaka kai
Garin gano yapi kowanne yanki girma da yawan jama'a wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita (596,209), watau kwatankwacin kashi Arba'in da uku cikin dari na girman Kasar baki daya.
Mafi yawancin jama'ar Masarautar Hausa-Fulani ne; akwai kuma Buzaye da barebari. Kashi (90)cikin dari na jama'ar Gano Musulmai ne
Babbar sana'ar jamaar masarautar ta asali itace noma da kiwon dabbobi saboda kyan kasa sai kuma kasuwanci da yayi karpi a shekarun da suka gabata har ake masu laqabi da *cibiyar kasuwanci*MASARAUTAR GANO
Mai martaba sarki Muhammadu Auwalu shi ke rike da mulkin masarautar Gano a wannan lokaci, Sarki muhammadu Auwal ya karbi mulkin wannan masarauta ne daga hannun mahaifinshi marigayi Sarki Muhammad Nasiruddeen AALI, gadon sarautar Gano a ka'idar sarautar qasar tasu na babban d'an sarki Nasiruddeen ne (Haidar AALI) musamman yadda Haidar AALI keda mutane cikin talakawa gida da waje,
Yarima Haidar-AALI da yarima Auwal sun taso suna masu son junansu, akwai shakuwa mai karpi tsakaninsu, Yarima Haidar-AALI mutun ne mai son mulki tun tasowarshi yana kuma da burin mulkar masarautar tasu musamman dayasan shi ne yarima mai jiran gadon Gano, a daya bangaren kuwa yarima Auwal sam baida sha'awar sarauta musamman kuma dayasan baze samu dinba, sai hankalinshi ya sake kwanciya ya maida hankali gurn cimma burikanshi, babban burin nashi kuwa bai wice zama shararren dan kasuwa ya samu arzikinshi na kanshi.
A hankali yarima Auwal ya shigarwa mai martaba da maganar yanason kafa nashi kasuwancin, amma sai maimartaba yaqi amincewa, yace idan kasuwa yakeson shiga to yabi kasuwancin masarauta (family bussiness) da suka gada suke kuma sabuntashi daidai da zamani, abin be mashi dadi ba amma sai bai nuna ba ya maida hankali cikin kasuwanci, dayake abune dayake so sai abin ya dinga samun cigaba, Yarima Auwal sai ya dinga kafa nashi kasuwancin shima a hankali yana kulawa dashi, a lokacin da mai martaba ya gane bai nuna bacin rai ba saima Alfahari dayayi dashi, da taimakon Allah a lokacin garin ya samu wannan take /laqabi nashi na cibiyar kasuwanci ta kasa,Masarautar Haye itace ta biyu a kasuwanci bayan Gano hakan yasa suke fafatawa kowannensu burinshi ace shi ne a sama kayansu akapi bukata amma dukda haka Haye batai nasarar kamo Gano ba, ana sayan dukka kayansu amma anpi bukatar na Gano dan haka aka pi siyansu da yawa kuma akai akai.....
A sanda Yarima Auwalu keta kafa nashi kasuwancin shikuma yarima Haidar-AAli ya cusa kanshi cikin Al'amuran mulki saidai yayi bakinjini sosai gurin manyan masu mukamai musamman en siyasa da gwamnatin dake ci a wannan lokaci sakamakonshi na mutun mai gaskiya da bin ka'ida a komai, wannan sukuma suke kalla yana musu shisshigi ne a al'amuransu, wannan bakin jini da Haidar-Ali kedashi ya saka manya da masu mukamai a fada da hadin guiwar gwamnati suka yanke hukuncin sam bazeyi sarauta ba idan babu ran mai martaba, domin su lura zai bata abubuwa da dama ne, ana haka ne mai martaba ya matsa su fidda mata suyi aure ko ya zaba musu
Haidar-AAli yace shi baida wacce yakeso dan haka ya barwa mai martaba za6i, shikuma yarima Auwal yace yana da wadda yakeso diya ce ga wani attajiri a lokacin wanda sukanyi kasuwanci tare,
Dafarko mai martaba ya ja domin ba yadda za'ai ya auro bare ba jinin masarauta ba a cewar mai martaban amma daga baya sai ya amince da sharadin zai kara aure cikin masarauta
Tare akai shagalin bukuwansu
Yarima mai jiran gado Haidar AAli da Amaryarshi Saudatu diya ce gurin Galadiman masarautar da mai martaba ya zaba mishi
Shikuma yarima Auwal da Amaryarshi Hafsatu wacce sukai auren soyayya
YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...