Sultan ya juya ya koma cikin motar yanajin shi cikin wani yanayi mara dadi, yakai mintun ashirin cikin motar bai tadata ba, yana so sahiba ta sake fitowa yana saka ran zata dan leko koda ganinta ne ya sakeyi amma inaa babu ko alamun ta ya dan dora yatsun hannunshi kan gashin kanshi da babu hula, ya jima da cire hular daga kanshi,
Sahiba ta shige gidan ta kulla kofar da dukkan karpin ta da kuma saurin gaske, ta wuce falour da dan sassarfa Allah ma yasa babu kowa falourn ta haye sama ta shiga daki shima ta kulle kofar, tayi wa kanta matsuguni a kasan tiles din dakin
"Aure pa? Aure pa sultan yake ambata, yarima sultan pa?" Ta bubbuga kunnuwanta jin maganganunshi na yawo kamar yanxu ne yake sake jaddada mata gabadaya she's confuse kwakwalwarta ta toshe tama rasa mene zatai...
A hankali ta miqe ta nemi hanyar bandaki taje tayi alwala ta dawo ta soma nafilfilu, sai lokacin taji t samu nutsuwa amma pa maganganunshi suna zane acikin kwanyarta, bata manta koda harafi daya cikin abubuwan daya ce ba...
Sai ta samu kanta da zubar da hawaye tamkar an kunna famfo, taya ma yarima sultan zai fara wannan tunanin, shipa yarima ne kuma shi ne ke jiran gadon gano, kyau da kudi da class duk gidansu ne, amma ita pa? Who is she?, bazawara? Wadda ta taba auren d'an uwanshi? Mene ya sakashi ya fara wannan tunanin ma? To ko dama da ake cewa love is blind, dagaske love is blind din?, anya dagaske yarima sultan son ta yake?, anya ba wata boyayyar manufa ce ta sakashi fadi ba, yayi amfani da ita ya barta? Ya wulaqanta ta kamar yadda dan uwanshi yayi?, she's so so afraid of going back to palace, bata fata ta maimaita irin rayuwa da zaman da tai na palace, kyara da hantara ta samu daga kowanne bangare, in kuwa sahiba ta tuno fulani sai gabanta ya yanke ya fadi babu yadda za'ai taso sake haduwa da fulani koda kuwa a mafarkin ta ne balle a reality, palace shi ne gurin daya sake tabbatar mata da bata da gata sam, kuma yanxu ta koma? Ta maida kanta ga halaka kiri kiri tanaji tana gani?....."sahiba you are just the perfect definition of my perfect, mace irinki ita nake muradi, i love you, i like you, i like everything about you sahiba from the bottom of my heart, i will love to make you mine"
Sahiba ta farka daga daddadan mafarkin da takeyi tana mai murmushi da jin dadin kalaman da suke farautarta har a baccinta, bata taba jin kalma mai sanyaya zuciyar kamar wadannan kalmomi ba, bata taba ganin mutun mai kwarjini kamar yarima sultan ba..... Sahiba ta dan ankara da tunanin yarima pa takeyi, yariman da jiya tayi rejecting dinshi kuma a jiyan ta tabbatarwa kanta bazata koma palace ba, ta gama lissafo every reason da zai hanata komawa palace, amma meyasa daga farkawarta ta farka dashi, taji kamar zuciyarta na kokarin cin amanarta, kwarai kalamanshi sunyiwa kunnuwa da zuciyarta dadi amma meyasa bazata kalli dalilanta ba tana da dalilai masu karpi da zasu hanata komawa palace amma meyasa takeji zuciyarta na rinjayarta?
Sahiba ta dan rankwashi kanta, "kwarai ba mafarki pa takeyi ba sultan jiya yazo kuma yayi confessing love dinshi gareta?"
"To idan yana sona dagaske yaushe ne ya fara so na?, ko dama tun ina matar dan uwanshi yana sona.... Ta bude ido da baki cikin mamaki sai kuma ta samu kanta da yin dariya,
Sultan is the first person to say he loves her, hakan yasa abin yake mata dadi, she can't deny taji dadin magaanarshi amma kuma batajin zata iya accepting dinshi, tana hango so so many challenges cikin alaqar tasuSahiba bata sakko ba sai da taji yunwa sosai rana ma ta fito ta nemi Abinci , a nan taga momy
"Wai nikuwa jiya wanne sako ne kika karba da yarima yayi aike? Naga kin dade har na je kwanciya"
Sahiba tayi murmushi mai kama da blushing tana tunanin karyar dabincia zata kakalo a kanta ta hada sai taji sallama a sama kuma kamar muryar sultan
Ta ware ido a sanda take kai lomar bread da kwai a lokaci daya kuma gabanta yayi wata mummunar bugawa da saida tayi tunanin ko zuciyar ta huda kirjinta,Ta miqe a sukwane da gudu tayi sama, shikuma ya zuba mata ido yana dariya, rigar bacci ce a jikinta iya guiwa da wando dogo sai dankwali, momy ta bisu da kallo smelling something tsakaninsu
Sannu sultan" cewar momy ganin yadda yake nishadi
Ko ita momy zata iya cewa bata taba ganin wide murmushin sultan bama balle dariya har haka abin da mamaki, sultan ya tsuke bakinshi amma bai dena murmushi ba ya karasa ya gaida momy, ta amsashi tana cike da mugun mamaki
Yace "momy muhimmiyar magana ce ta kawoni" tace "to Allah yasa dai lafiya
"Lafiya qalau momy" so nake ki roka min mai martaba akan bikinmu da Amira sunata shirye shirye ne nikuma gaskiya yanxu na samu wadda nakeso, inaso a fasa bikin mu da Amira, dama mai martaba zabi ya bani"
Momy ta jinjima kai "bana jin wannan maganar taka akwai alamar gaskiya, sai kawai na dauki kafa naje gurin mai martaba nace ya fasa baka diyarshi, na wargaza auren diyarshi pa kenan, gaskiya bani da wannan kwarin guiwar sultan, ka dai sake tunani, da can baka samu wadda kakeso din ba sai yanxu da bikin ya zama saura kwanaki uku a daura aure"
Sultan yaji jikinshi yayi sanyi.... "Ita din daka samo kakeso a ina take", sultan yayi murmushi "dama ai wannan ce momy, dama sahiba ce"
Momy zuba hannayenta biyu tayi tagumi "sahiba? Matar marigayi yarima khalipa?, matar dan uwanka? Dama akan sahiba ne kakeson fasa auren amira? Sultan?"
Momy cike da confusion take mishi wannan tambayoyin, sultan ya fahimci gabadaya momy bata goyon bayan sahiba, shikuma ya kawo mata maganar ne dan yana tunanin ai sahiba kamar 'ya take gun momy din amma kuma yaga kamar ba hakan baneSahiba dake saurarem duka conversation dinsu ta danyi shiru tana jin dacin maraicinta, to tun daga nan gida ma kenan ba'ayi approving alaqarsu ba balle kuma akaiga fita waje?, ya mutane zasuyi reacting? Ya za'a dauki matsayin alaqarsu? Ta sauke numfashi ta koma daki ta samu tayi wanka, ita duk ta dauka i yanxu ma sultan ya tapi amma sai ga habiba tazo, ko habiba batace komai ba ta rigada tasan dalilin zuwan ta.......
Yana tsaye a farfajiyar gidan nasu ya jingina da motar daya zo da ita yayi folding hannunshi so deep in thought, saidai duk zurfin da yayi a tinanin bai kasa jin presence dinta tana tunkaro shi ba, ya dago idanunshi ya kalleta, baisan meyasa idan ya kalleta yakeso yayi murmushi ba, murmushin shi gareta is an involuntary action da shi kanshi bai iya controlling,,, ta mishi sallama fuskarta babu wata walwala, "barka da zuwa miftahul qalb" ya fada bayan ya amsa mata sallama, still bata ce mishi komai ba ta sunkui da kanta a hankali cikin voice kwantacciya yace "kinyi kyau" sahiba cikin ranta tace "kaine sanadi ai, cos cikin kayan daka sayo ne".... Jin ta kuma mishi shiru yasashi cewa "ban taba yin soyayya ba sahiba, you 're my first, shin kina ganin kinmin adalci kiyi rejecting dina without even atleast giving me a chance, sahiba ki bani dama, lemme prove my love to you, idan kina tunanin abinda mutane zasu ce ne akanmu ki bar zancen mutane sahiba, kimin alfarma idan har zuciyarki tana so na ki toshe kunnuwanki ki amsheni, duk wannan hayaniyar na dan lokaci ne, pls and pls sahiba dont disappoint me, ki bani dama sahiba"
Sahiba tayi sighing cikin confusion tace "zanyi tunani yarima" yayi murmushi a sanda idanunsu suka hadu, "don't stress yourself kinji? Kowanne fanni dama a rayuwa akwai obstacle musamman maganar aure, nasan zaki sha maganganu, saidai duk manta dasu ki tuna da soyayyar da kike min, trust me ki bani amanar kanki nikuma i promise to love you for the rest of my life" sahiba tayi dariya tanaji kamar mafarki take, ta juya ta koma ciki....Khalipa ya farka yana jin wani nauyi a kirjinshi kamar an dora mishi duwatsun dala da gwauron dutse baze iya jurewa ba, baze iya ba sam, milana keda maganinshi ita kadai a duk fadin duniya, baze saduda ba idan bazatazo inda yake ba shikam zaije gareta, ya dan miqe yana hada hanya yana dafa bango har ya fito daga bukkar jiri na dibanshi ya samu ya dan jingina a wajen bukkar, ta idanuwanshi dake gani bibbiyu ya hangeta tsugunne tana hura wuta, da alama sanwar dare zata dora, ya soma tafiya yana layi da tangadi kamar wanda ke maye, iskar dake busawa kamar zata daukeshi, ya karasa yana haki sosai ya zube gabanta, milana ta tsorata jin faduwar mutun a gabanta ta juyo da sauri ta ganshi, dukda a irin mawuyacin halin dayake ciki sai ya samu kanshi dayi mata murmushi, a idanun nashi da bai gani clear yaga itama tana maida mishi da martanin murmushin nashi yaji kuma zuciyar tana mishi sanyi sai lokacin yaji sanyin iskar dake busawa a gurin tana ratsa fatar jikinshi, ya soma rawar dari,
Milana data zuba mishi idanu tana kallonshi without emotions kan fuskarta ta juya ta nemo malullubi ta yafa mishi a jiki, da dumin wutar data hura suka taimaka gun dumama jikin nashi.... Ya tsugunna gaban wutar yana jin dadin dumin yana kuma kallon milanarshi,,, baida wani sauran buri bayan wannan yayi ta kallon fuskarta dake haske tamkar hasken farin wata, baze taba gajiya da kallonta ba... Milana ta kammala girkin ta sauke, tayi hanyar bukkarsu, khalipa ya miqe har yana tuntube ya bita, ta ajiye tukunyar kasar ta juyo tace "wai meke damunka ne?" Ko kana tunanin bi na da kakeyi shi zai saka na chanja ra'ayi na, to ka sani ina nan a kan baka ta inma zaka watsattsake gara ka wattsake ta shige bukkar su ya bi bayanta
Milana taga dai lallai shigowa zaiyi dan haka tasa hannu ta hankada shi, ya fadi ta bishi ta tsugunna tayi kasa da muryarta yadda mama bazataji ba "stop following me around yarima khalipa"
Khalipa bai gane ko muryar milana bace ko kuma ta wata baturiya ce ba saboda yadda accent na english din ya fito tarr a bakinta to kodai mafarki yakeyi.....Assalamu alaikum daukacin masoyana da suke bibiyar labarina, its a huge thank you from me i appreciate you all, dont forget to share and vote

KAMU SEDANG MEMBACA
WANI YANKI
Romansa"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...