Pls mistake ne inda na saka sahiba instead of milana, ban samu na zauna editing baneWata zabura milana tai kan kace me sai gata a gefen mama, ta riko hannunta,, mama ta dan tsorata tace "waye nan"
Milana ta dan murmusa tace "nice mama, milanarki ce"
"Assha milana kin bani tsoro ince dai komi lafiya" tace eh komi qalau mama me kikeyi a nan"
"Na aiki sidi ya dakko ruwa ne kuma sai nake neman kujera na zauna"
"To tsaya nan mama bari na dakko miki ai gata nan" ta jawo kujerar ta bawa mama ta zauna a kai sannan ta dakko littapin da malan ya bata ta kai dakin ta ajiye ta dubi bawan Allah n dake kwance tamkar matacce yanxu temperature n jikinshi ya soma dawowa amma dukda haka idan ya farka zaiyi fama da sanyi,,, milana tajiyo sallamar sidi a waje ta fita tana karban ruwan hannunshi ta tayashi ajiyewa dan ba karamin aikinshi bane ya fashe tulun garin ajiyewa,,
Sidi ya karbo ganyayyakin magani gurin malan dan basu da dayawansu a yankin hakan yasa idan malan yayi tafiya yake sayosu dayawan gaske yadda zasu dade musu batareda an nema ba, yau garin ya dan washe ranar batai zau ba amma da dan haske hakan yasa suka shasshanya ganyayyakin wasu a inuwa wasu kuma da ake buqatarsu a ranar
Haka ma saiwowin itaciya wadanda suke danyu aka samu inuwa aka barbazasu domin tanadin gabaSatin malan guda cir da dawowa kuma satin khalipa cir a dakin sahiba tana dawainiya dashi har ta soma fidda rai da ze farka sai jiya data taba bugun zuciyarshi taji karpinta ya karu yapi na da sannan sanyin jikinshi (temperature) tayi daidai har ma taji a jiyan jikin nashi yayi zapi kuma alamar zazzabi, babu karya milana da sidi sunyi dawainiya da khalipa domin kullun sai sidi ya canja mishi sutura ya wanke wadancan, wani lokacin ma kapin yazo zai tadda khalipan yayi fitsari kuma haka zai chanja ya gyara gurin, babu abinda milana ke durawa khalipa sai ruwa, ko ruwan magani zasu buda bakinshi su dura mishi, su gyara mishi kwanciya sannan su ma jikinshi tausa saboda jini ya warware, da sauransu....yau tun safe malan ke ta shiri hakan yasa milana da sidi suka gane abinda ke shirin faruwa, dama malan ba wani dadewa yake mafi dadewar dazaiyi shi ne yayi sati dako kwana daya ko sati da kwana biyu, saboda duk wata tafiya da za'ai a yankin dole sai da shi, malan ya tarasu duka su ukun ya tabbatar musu gobe da asussuba zai kama hanya, kuma yana saka ran zuwa da maganin da zai warkar da makantar mamantasu a wannan karan, don kuwa daga baya ne ta samu wannan makanta amma da ba haka take ba, sukaji dadi saidai kuma ya sanar musu tafiyar tashi ta wannan karan zatai tsayi, saida ya tabbatar ya ajiye musu komi da zasu buqata dama... Suka danyi yan koke koke na rabuwa wanda sidi yafi kowa zakewa dan kuwa ita milana abin ya zama jiki, shima sidin raguwar zuciya gareshi amma yaci ace ya saba, haka itama mama har yanxu ta kasa sabawa...
Bayan sunci tuwan dare ne anyi yan hirarraki dare yayi suka kama hanya zuwa bukkarsu domin ya da hakarkari, malan dake waje bai samu komawa daki ba yajiyo kamar tari, daga bukkar milana
Milana dake shimfida tayi azamar juyawa jin tarin sai kuma taji malan na fadin "milana milana mura kike yi, ta karasa kan gadon karan a sukwane ta saka hannu ta toshe mishi baki sannan tai gyaran murya tace "eh malan amma nasha jiko ga sauran ma a nan" yace to ki dinga kula dan Allah banda yawo babu takalmi ko dankwali a dinga rufe jiki" ya wuce yana cewa "har yanxu jikinki bai saba da yanayin yankin nan ba, bakya son sanyi..."
Har ya shige daki yana tadi da kanshi, a jigace khalipa ya tattara karpinshi ya buda idanunshi yanajin suna kokawa da numfashinshi da milana ta tare mishi, a kasalance ya dan daga hannunshi ya dora kan kafadarta,
Tayi saurin sakin bakinshi data toshe ta miqe ta ture hannunshi daga kafadarta, khalipa ya kalli rufin cikin bukkar yanajin juwa na dibanshi, milana ta tsugunno gaban gadon tace a hankali kamar tana rada"ina ke maka ciwo"
Ya lumshe idanunshi yana sakin numfarfashi sannan ya kalleta at once ya kuma kura mata idanu, sai ya samu kanshi da kasa dena kallonta a sanda ya bata cikin tunaninta, ta saka hannu ta duba pulse dinshi tajita daidai saidai mugun zazzabi dake jikinshi sannan ga tari da sanyi jikin nashi bayaga ciwuka dake jikinshi, dukda sunyi treating ciwuka kuma cikin satin duk sun kama jikinsu, wanda hakan ke nuna yana da lafiya kuma yana cin abinci masu gina jiki a baya
![](https://img.wattpad.com/cover/261597110-288-k51934.jpg)
YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...