Sidi cikin tsananin tausayawa yace "tayaa zamu barshi a nan ya mutu milana, yanxu dan Allah bai baki tausayi ba, dagani wani mummunan abu ne ya sameshi ga yadda kanshi ya fashe yake zubar da jini sannan kalli raunikan dake jikinshi"
"Idan ka kalli suturar dake jikinshi zata tabbatar maka ba namu bane"
"Nasan dama ba namu bane mana milana amma bawai hakan ke nupin muyi watsi dashi ba, kamar ba kece malamarmu ba, wayasan irin ladan da zamu samu idan muka taimakeshi"
"Bakai tunanin kuma irin hukuncin da zamu fuskanta ba idan muka taimakeshi? Ka manta dokar ne? Ko dan kana karami sanda wancan abin ya faru?"
"Muyi gaggawar barin gurin nan domin malan yana gab da karasowa na tabbata yanxu haka kwalekwalenshi ya iso" tayi gaba abinta sidi ya bita ya rikota hankalinshi a tashe
"Ki dubi girman Allah ki kuma dubi aikin taimakon da zakiyi kiyi aiki da iliminki kar mu wofantar dashi, shima yanada dangi da 'yan uwa ya kike tunanin zasuji idan akace musu ba'a ganshi ba, kuma ya mutu basuga gawarshi ba"
Milana ta kurawa sidi ido ta danyi zurfi cikin tunani sannan ta kalli khalipa ta juya tayi hanyar dazataje taro malan
Sidi ya rasa waze bi, ko ya bita su bar bawan Allah ya mutu ko kuma ya taimaka mishi a boye,, saidai inda matsalar take kuma daban ce
Sidi ya karasa kan khalipa ya dan tsugunna ya gyara mishi kwanciyarshi yasaka ganyayyaki ya lullubeshi yadda babu wanda zai lura dashiA hanya suka hadu da malan milana ta karasa gareshi da azama ta karbi kayan dake hannunshi cikin dan buhu irin na Algarara, sannan ta soma mishi barka da zuwa "ya amsata da yawwa
Malan kamar yadda su milana da sauran mutan yankin ke kiranshi dattijo ne sosai da Akalla yakai shekaru 60 a duniya, fari ne dukda hasken fatar tashi ta disashe saboda wahala baya zama guri guda yau yana nan gobe yana can, yanada matsakaicin tsayi da fuskarshi mai cikeda kwarjini, malami ne kuma mai magani ne milana ta kasance duk itama ta hada abu biyun dukda karancin shekarunta,, wanda malan ne ya ringa koya mata tun tana 'yar karama take gwagwarmaya sabodaa ta taso ta tadda mahaifiyarta cikin lalura, ga qaninta kuma bai fiya fahimtar karatun ba dukda yanayin duk wasu aikin karpi....
A hankali suka dinga tafiya har suka shiga cikin gari, duk inda sukayi duk wanda ya gansu zai tsugunna kasa ya gaida malan idan kuma dattijo ne kamar shi to zasui musabiha cikin girmama juna
Malan ne yace da sahiba "wai ina sidi ne?" Tace "na baroshi yana baza kayan wanki dan busarwa" malan yace "aiho shiyasa baizo nan tarbata ba ince dai ba fada kikai mishi ba" milana ta girgiza kanta a hankali tana tunanin ina sidi yaje, gidan shugabansu wanda yake a matsayin mai gari malan ya biya, sun jima suna tattaunawa har milaja tai magriba da isha'i a nan, ta dan fito kofar gidan ta zauna kan wani dutse tana jin sassanyar iskar daren na ratsata a hankali, kamar an jefoshi taga sidi a kanta ta kalleshi ta miqe tsaye "ina kaje?" Ya danyi murmushi yace "gun mama na koma na nemi wata rigar na saka mama tana ta jira y akayi baku taho ba, yau kun jima a gun mai gari, ana haka saiga malan ya fito yaji dadin ganin sidiSidin ya durkusa yakai gaisuwa tare da mishi sannu da hanya, suka kama hanya zuwa nasu gidan, can inda suke guri ne da babu jama'a sun dan fita daga cikin mutane saboda karatu dole suna buqatar gurin da babu jama'a yadda ko malami ko dalibai sun daga murya bazasu dami jama'ar ba haka suma jama'ar bazazu damesu da hayaniya ba.... A filin da shine matsayin tsakargida wato wajen bukkar suka tadda mama zaune hannunta rike da sandarta tana dan murmusawa domin taji takun sawayensu,
Sukai mata sallama ta amsa su sannan ta shiga gaida mai gidan nata shima ya amsa ta da annashuwa da jin dadin ganinta lafiya lafiya,Kowa ya shiga tashi bukkar domin kwanciya saboda dare da yayi milana taji motsi a bakin tata bukkar wacce suke kwana da mama amma yanxu tunda malan ya dawo zata koma kwana a bukkar malan dan haka milana ita daya zata na kwana,
Ta dan tashi zaune sannan ta karo hasken fitlar kwan dake ci, ya shigo dakin nata yana dan jijjiga jikinshi, milana ta lumshe idanu dan ta gane me hakan ke nupi,
Tace "muje muje" ta miqe ta nemi malullubi ta rufe jikinta sannan suka kama hanyar dawa domin sidi yayi bahaya suna tafe milana tace "kaidai ka banu da bahayar dare ga kuma shegen tsoro, yaci ace ka girma k dena tsoro nima na huta da rakiya"
Sidi ya juyo ya rike hannunta ta fizge hannunta da sauri "kinga milana ni babu wani bahaya so nake muje mu dakko wannan mutumin"
Ta hada idanunta dana sidi ta kasa fadan wata kalma "nasan kema kinason mu taimaka mishi dan haka ki cire duk wani tunanika karasa kyau ki sauya da na Alkhairi, muyi sauri kada mu makara"
Suka saka kai suna dan sauri sauri har suka karasa sidi ya cire ganyayyakin daya rufe khalipa milana tasa hannunta kan wuyanshi taji sanyi kalau kamar ta taba gawa saidai bugun zuciyarshi data ji ta kan jijiyarshi yasa tasan bai mutu ba amma zuciyar tashi ma tayi rauni domin bugun nata a raunane takeyi, tace "muyi azama sidi baida lokaci mai tsayi, idan har zuciyarshi ta bar bugawa shikkenan bamu da wata sauran hanyar cetonshi"Sukai azamar kamashi bashi da nauyi sosai amma daayake tafiyar na da dan tsayi yasa suka jima basu karasa ba kuma hakan yasa duk suka galabaita amma dukda haka basu fidda rai ba,
Bukkar milana suka sakashi bayan ja inja da suka tsaya yi kan lallai bukkar sidi ya kamata su kaishi a cewar milana shikuma sidi yace "me kike tunani idan bisa tsautsayi malan ya shigo bukkata ya ganshi ko kuma akai ruwa ya sake tabashi kuma ni ina na iya kula da marasa lafiya kekuwa mai taimakon majinyanta ce zakipi kula dashi kuma malan baze taba shigowa bukkarki ba saidai yayi kiranki" da wannan ya samu shawo kan milana amma sai tace to muyi yaya da mama kuma
"Idan malan ya tapi sai mu dawo dashi nan bukkata ko kuma idan ya farka, yanxu yana cikin buqatar kulawa sosai"Suka ciccibi khalipa suka sakashi cikin bukkar suka kwantar kan gadon kara, milana ta dan yarfe hannuwanta saboda gajiya, sidi ya juya zai tapi tace ka dakko mishi aron kaya a cire wannan na jikinshi"
Hakan akayi, sidi ya cire suturar jikin khalipa suka maida mishi da suturar sidin wankakku, milana tace akwai buqatar garwashi sidi zaka iya hada wuta yanxu, yace eh tace "amma ka zagaya baya yadda su malan bazasu lura da hayakin ko hasken wutar ba"
Itacen nasu duk danyu ne saboda basa rabo da ruwan sama, haka ya samu ya kunna dayake ma da sabo, yajira yayi garwashi ya diba a kaskon kasa mai dan fadi ya kaiwa milana data lullube khalipa da zannuwa kusan shidda , ta daga zannuwan ta nemi guda a ciki mai kyau ta kara a jikin kaskon wutar saida ta tabbatar yayi zapi sosai ba yadda zai kona fatar khalipa ba amma ta ringa gasa miahi jikinshi tun daga kan fuskarshi, kafafunshi, hannayemshi, haka dai tayi tabi tana gasashi,
Sun jima a haka kapin ta nemi wani magani ta dan kwaba ta shafamishi a kafafunahi da hannayenshi sannan ta lullubeshi kamar daxun...
A lokacin tace da sidi yaje ya kwanta zata cigaba da kulawa dashi.. Dama duk ya gaji ya mata sallama ya koma nashi dakin,Milana taji wani banbarakwai, ta kuma kallon fuskar khalipa dake kwance baisan inda kanshi yake bama, ko kadan kyawunshi bai wani birgeta ba amma bata isa tace bashi da kyau ba, ta rakuba gefe ta dan kwanta tana addu'ar Allah ya rufa musu asiri ya basu ladan kulawa da zasu cigaba da bashi...
Kashegari gidan su milana ya kasance akwai yawaitar jama'a saboda masu zuwa gurin malan domin kuwa malan mutun ne mai jama'a, ana ganin girmanshi, gabadaya hankalij milana da sidi ba a kwance yake ba babu ma kamar milana da take zaune a kofar dakin ta hana kowa shiga, tana danjin motsi kadan zata ji kamar zuciyarta aka motsa dan tsabar tsoro, akwai wata yarinya karama datake zuwa yin wasu aiyukan gidan idan malam baya nan saboda ayyukan na yiwa milana yawa tunda tana kula da marasa lafiya kuma tana bada karatu dukda ba kullun bane, yauma yarinyar mai suna shamsiyya ta karaso sahiba tai saurin cewa "shamsiyya ki koma kawai ai duk na gama ayyukan ma" shamsiyya ta dubi yadda take t faman gumi ta saka kujera a kofar daki ta karaso tace "ki koma daga can ya danpi sanyi mana" milana tace "dan Allah shamsiyya ki koma gida idan malan ya koma kya dawo" shamsiyya tace to...
Sidi ne yazo yace da milana "kije malan na kiranki zai baki tsarabarki bakin nashi duk sun wuce"
Milana tace sidi ka kula da kofar nan kar wanda ya shiga ai kadai gane yace eh ta wuce gurin malan ta bar sidi da mama a tsakar gidan, yana can daga nesa kasan wata bishiya yayi shimfida ta karasa ta gaidashi ya amsa yace "ga tsarabar dana taho miki da ita" ta amshi littafin da akai rubutun ajami a jiki tace nagode malan
Komawar da zatai ta nemi sidi ta rasa, ga mama tana ta lalube har ta lalubo kofar ta soma kokarin shiga dakin da khalipa ke kwance.....Not edited🙏🏻🙏🏻

ESTÁS LEYENDO
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...