Episode 31: A week to go

22 2 0
                                    


Sidi yazo kan khalipa dake fama da matsananci zazzabi "Khalipa ya jikin" khalipa ya gyada kai  kurum, shi kadai ne yake gane abinda ke faruwa dashi, tun lokacin da milana tai mishi wannan marin, ya kasa controlling emotions dinshi, ya kasa dena sonta, a duk lokacin da milana zata nuna bata qaunarshi to a wannan lokacin ne wutar sonta take sake huruwa a cikin zuciyarshi...
Sidi ya dan dagoshi ya bashi wani ruwan magani yana fadin, "ina ne ke maka ciwo khalipa ya kamata ka fadamin saboda nasan yadda zan mata bayani ta baka maganin daya dace"
Bakin khalipa na fidda huci yake fadin "sidi bansan mene ke damuna ba, jikina ba dadi kaina ma ba dadi amma na kasa gane ina ke min ciwo ko kuma mene ke damuna"
Sidi cikeda tausayawa yace da khalipa "kayi haquri khalipa, kayi haquri Allah ya sawwaqe maka"
Khalipa ya lumshe idanunshi hawaye suka sakko suka jika gashin idonshi sukabi gefen idanun nashi

Sidi yaje waje ya samu milana dake jiranshi yace "yace bai san mene ke damunshi ba milana, ina tsoron kar yaje ya mutun mana milana, kinga dama can ba wata isasshiyar lafiya ya cika ba, to gashi yanxu ko tashi zaune ma bai iyayi, kuma mun kasa gane wanne irin ciwo ne"

Milana ta dubi sidi emotionless tace "dani da kai dashi duk munsan meke damunshi, mu dena ma kanmu karya sidi, abinda zuciyarshi ke bida abu ne da bazata samu ba, zuciyarshi ta dakko da zapi, ta kinkimo abinda yapi karpinta, idan har ya takura to lallai zuciyar tashi zata fashe ne tayi bindiga, a lokacin kuma gangar jikinshi bazata iya jurewa bazata iya daukan ciwon zuciyar tashi ba"
Sidi ya kurawa milana ido a yayinda suke kai sakwanni wa junansu ta wannan kallon
Sai milana tayi murmushi ma sidi tace "kasan dai hakan bamai yuwuwa bane"
Sidi ya sauke idanunshi yace "ki gwada mana milana, kika sani ko in kika amshi soyayyarshi hakan zai sa ya samu sassauci, watakil daga baya ya fahimci bazaki taba sonshi ba"
Sai tasa dariya "ni kaji nace maka na tsaneshi ko bana sonshi?

"Idan baki fadamin ba ai shi kin fada mishi kuma Dama bance kin tsaneshi ba amma ki nuna baki sonshi ta sigar lallashi da kyautatawa yadda zai haqura dan kanshi"
Milana ta dan tako kusa da sidi sosai a hankali tace "sanin kanka ne, wannan yanki bana zuwan mutane bane, dan Adam irin Khalipa hadari ne zuwanshi wannan boyayyan yankin waya sani watakil baze bar nan da rai ba"
Sidi ya shafa sumar kanshi sannan yaja doguwar ajiyar zuciya "fitar yarima khalipa wannan yankin da rai abu ne mawuyacin gaske"
"Gara daka tuna wannnan Dan haka mu samu hanyar datake mafita gareshi yadda zai kubuta da ranshi ma tukunna kapin azo batun soyayya, tunda koda ya bar yankin nan, mu zamuje gareshi cikin hanya mai sauki"......

Khalipa dake bakin kofar bukkar yaja jiki ya koma ciki bayan ya kammala sauraran tattaunawar da sidi da milana suka gama, tsoro ne ya baibayeshi cikin ranshi yake fadin "where on earth am i?... Kodai yankin Aljanu na fado?" Jikinshi daba kwari ba ya dan dauki bari, yana relating abubuwan yankin
To inba yankin Aljanu ba, ya za'ace ba'a karban bako, babu me shigowa kuma babu mai fita sai malan ko da malan, tsaunikan da suka zagaye yankin Abin tsoro, haka ma tapka tapkan teku na, mutanen dake yankin kap basu wuce rai 20 ko 30 ba,, rayuwar kamar wanda yake a daure suke yinta babu mai damar barin yankin, babu mai gane kan tekun sai malan to shi malan waye shi?, khalipa na ji a ranshi malan ne kadai keda amsoshin tambayoyinshi kuma shi koda ace milana ba mutun bace yana sonta, tunda ya aminta har cikin ranshi bazata cutar dashi ba domin kuwa da zata cutar dashi da tuni tayi hakan tun sadda yake kwance baisan inda kanshi yake ba, da zata cutar dashi da tayi hakan ta hanyar magani da abincin dayake ci,

"milana da sidi sunada chances dayawa in har suna son batar dani....

X x x x x

Sahiba ta duba zobunan azurfan da ta siya tun kudin daya bata wancan karan, kudin da shine na farko da aka fara kyautata mata dasu, a lokacin data saye su ta siya ne as couple's ring (adjustable) domin ta faranta mishi ta kyautata mishi, a wancan lokacin bata taba kawowa wai zata bar hannun yarima khalipa ba, har wata mu'amula ta aure ta shiga tsakanin su, everything happens so quickly kamar a mafarki, bata kara yarda da kalmar life is so mysterious ba sai yanxu, rayuwa cike take da tarin boyayyun sirrika, wahalar fassaruwar wasu al'amuran, wahalar ganewa, wahalar yin bayani, you just can't predict the future....

Sahiba ta fito daga dakin tana preparing for their final class na girki domin lokacin zuwanta ya kusa, tana kitchen din ita daya sai ga hamma kamar an jefo shi, kallon yan sakanni sahiba tai mishi ta kauda kanta ta cigaba da abinda take, saedai cikin wannan kallon ta fahimci abubuwa, taga canji tare da hamma, tun daga kan launin fatarshi da tayi duhu sabanin da dayake tas, labbanshi ma sunyi baki kamar wanda ke shaye shaye, sumarshi tayi buzubuzu babu alamun gyara, gayun duk ya soma gushewa
Sahiba tace "hamma yau kaine a kitchen" yayi yar dariya yana shafa kai
Alfarma nazo nema my sister"
Ta dan juyo da mamaki "Alfarma kuma hamma? Nikuwa me gareni?" 
"My sister ai kece keda komai, bakiga yadda Abbah ke jin maganarki ba" so nake ki taimaka kice ya bani jari na biya kudin mutane dake kaina, wlh tsautsayi ne ya fadawa kayana, aka tafka ruwa kinsan kasashen waje ruwansu ba irin namu bane sai kiga ruwa ya tapi da unguwa guda"
Sahiba tayi ajiyar zuciya "Allah ya maida Alkhairi hamma" ya cigaba da fadin
A ranar dana hada ribar kasuwancin nan na karbi wasu kudin kayan mutane, na hada da uwar kudi da ribar dana mutane duk na siyo kaya, sae kuma ga wannan iftila'in"
Asara batta da dadi ....
Ya katseta da sauri yana cewa sam sam sam my sister, to amma abin sai da dangana, shikuma Abbah sam ya kasa gane hakan, yaqi saurara ta"
Sahiba tace "kayya, ai ita wannan rashin rabo ne ba laipinka bane"
Kamar ta sake zugashi ya cigaba da fadin "to nima dai abinda nagani kenaan my sister"....
Sallamar chef din da suka jiyo a falour ya katse sauran abinda zai fada
"Yayi concluding da "ki taimaka ki samu Abbah ki mishi maganar" sahiba tace to in shaa Allah
Sahiba ta fita ta taro chef din suka fara aikinsu

Sai yamma su hajara suka shigo gidan, tun safe ta fita makaranta haka suma sauran kannen nata, abin na bawa sahiba sha'awa sosai da sosai, abin yana ranta kuma data tare zataiwa yarima sultan maganar nata karatun...
A sanda taji alamun dawowar Abbah ta tuna maganar su da hamma dan haka ta shirya zuwa yiwa Abbah maganar kamar yadda tayi Alqawari, duk motsinta kan idon hamma ne... Yaji dadi dayaga tayi gurin Abbah
Shi Abbah duk zatonshi wata hidimar ce ta taso take buqatar kudi amma sai yaji sabanin nata hidimar tana rokawa wani ne... Sahiba ta gama duk rokonta da yan fadancinta duk kan abbah ya dubi lamarin saida ta gama yace "bakomi sahiba kije zan duba amma pa ki sani wannan maganar ba taki bace banaso ki sake zuwa min da makamancin ta" tayi godiya ta tapi,
Tana fita hamma ya tareta, ta dan tsorata da farko sai ta sanar mishi yadda sukai da Abbah da kashedin daya mata....

Da daddare sun zo kwanciya hajara taja sahiba daki ta bata wasu kaya cikin leda, ta karba tana bubbuda su baki a sake, ta ajiye ta dubi hajara "na mene?" Hajara ta hade rai naki ne siya zakiyi"
Sahiba ta danyi dariya "aini bana saka irin wadannan kayan"
Hajarah tace "karki bari na dura miki ashariya wlh sahiba, in baki sakama mijinki wadannan ba dame zaki jawo hankalinshi, kindai san maza da gane gane,kin kuma san inda zakije... Palace ba gurin wasa bane idan ba so kike ya likewa wadannaan cousins din nashi masu naci ba to ki gyara ah to, kudinsu gabadaya 30k, ta fada ta wuce abinta

Sahiba ta daga bomshort din tana jujjuya shi, ta zaro wata top bodycon da iyakarta under-burst ne ta ajiye ta zauna tana kallan kayan.....

Babu yadda ta iya saida ta fidda kudin kayan ta bawa hajara, saura sati daya tarewar sahiba, ciye ciye kala kala da kurbe kurbe da turare turare ba wanda sahiba bata gani ta ci tasha ba, duk wannan aikin momy ne itama Anty ta kawo nata gudunmuwar, komi daya kamata a siya an siya a nasu bangaren amare, shima bangaren uban gayya, mai martaba ya tsara mishi gini mai kyau kusada gidan khalipa dake a rufe, saidai baikai girman na yarima khalipa ba, saboda komi a sauri sauri akayi, 2 bedrooms ne da main falour a kasa da kitchen, store, backyard sai kuma falour da master bedroom a sama, toilet in each bedroom
Haka Abbah yayi bajinta ya cika ko ina da kaya, sultan da mai martaba sun ce Abbah yabar zancen kayan daki amma yace sam wancan baiyi ba a barshi yayi a wannan....

Fulani tayi nasarar lullube zafaffar wutar dake ruruwa a zuciyarta da murmushin dole datake shimfidawa kan fuskarta, ita kadai tasan abinda ke zane cikin ranta, tasha Alwashin lallai babu me auren sultan in ba jininta, domin bazatai biyu babu ba, danta beyi sarauta ba kuma diyarta ma bata zama fulani ba, inaaa to wanne zataji kenan,

Kamar yadda sahiba tai shirin bawa angon nata kyauta haka shima yayi nashi shirye shiryen dayasan zasu kawatar da ita su faranta mata, burinshi kenan faranta ran sahiba.

WANI YANKIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora