Kashegarin ranar Sultan (last page na saka khalipa its a mistake) ya tashi yanajin bugun zuciyar tashi na karuwa, tunda ya kwanta mafarki ne kala kala na sahiba yakeyi, how cute her lips are how innocent her face is, how beautiful and pretty she is naturally,,, ya kamata ya gwada sa'ar shi, amma he's too afraid so so afraid of rejection
.
.
.
Ranar da sahiba ta koma jin yadda sukai a ranar ta soma shiga aji dan koyar da dalibai domin kuwa har an bata aji, kuma duk sun tsara komi kamar yadda sukai da malan habibu... Ba karamin dadi sahiba taji ba domin burinta shi ne ta rage zaman kadai ta kuma rage zama cikin gidan dayake mata kama da makabarta ba, tunda babu wani mai sonta ko wani daya damu da ita kowa fama yake da nashi al'amuran.... Sahiba tayi sati guda tana yiwa dalibai karatu itama ana mata nata karin, malama salma ce malamar da suka pi sabawa da sahiba jininsu yapi haduwa domin su biyu ne kadai 'yan mata sauran duk manya ne masu aure kuma cikin ikon Allah sai ra'ayoyinsu yake zuwa daya, sahiba har ta fara sakin jikinta da malama salma domin kuwa malama salma bata taba nuna kyama kan halittar sahiba ba asali ma ita ko kadan bata ga aibun halittar ta ba waannan ya kara sakawa sahiba take jin dadin mu'amula da ita, suna zaune a ofishin malamai mata su biyu ne kadai cikin ofishin sahiba da salma sauran malamar duk sun shiga aji, salma dake duba hissoshinta a takarda ta dago ta dubi sahiba tace "wai nikam baki gajiya da rufe fuska ne, ki dinga cire niqab dinnan kina hutawa mana, ga wannan uban zapin da ake bayan la'asar ma amma rana zaki gani kwalleliya ki hutar da rayuwarki"
Ta cikin niqabin sahiba tayi murmushi, "baya damuna nafijin dadi cikinshi nafi jina comfortable idan ina sanye da niqabi" malama salma tace "idan dai har ba domin Allah kike sakashi ba to bashi da amfani, na lura baki son nunawa duniya kanki ne maybe baki da confidence na fitowa babu niqabi, da alama wani ya taba kushe ki ko kuma ince wasu har hakan yayi discouraging dinki"
Sahiba ta sunkui dakai domin dama tasan salma watarana sai ta gano ta, saboda ita din mutun ce mai kaifin basira... "Ni naga fuskarki kuma nima din ina gani ne idan munje Alwala, kuma ni zan fada miki fuskarki bata da wani matsala, sahiba ke mai kyau ce ki saka hakan a ranki duk wanda keda matsala da halittar da Allah ya miki to yazo ya chanja ki in zaya iya... Bari kiji akwai mata da kinfisu kyau amma saboda sun fiki confidence shiyasa duniya ta yarda suna da kyau, abinda kike buqata ba kyau bane ko hasken fata self confidence ne, ki gamsar da kanki kema mai kyau ce, inkuwa ba haka ba to kema kin yarda ke ba mai kyau din bace".... Sahiba ta gama sauraran jawaban Salma tasa hannu ta kwance niqabin fuskarta a hankali tamkar bata son kwancewa, fuskar sahiba ta bayyana... "Ko kefa, ko ni nan wlh bazan nuna miki asalin kyau ba sahiba, hasken fata kawai zan nuna miki, kalla hancinki mana kalla eyes dinki kinma taba kallan gashin idanunki, kin taba lura da irin tsawonsu da kyawunsu, kin taba tsayawa kin kalli kyawawan zanannun labbanki? Amma abu daya kika maida hankali akai shi ne kalar fatarki duk kika watsar da sauran blessings din kikai concentrating kan launin fatarki, kuma ma dan kina kallon kalar fatarki a sanda kin saka a ranki cewar bamai kyau bace amma da zaki ga how damage skin din wasu take zaki godewa Allah, babu kurji ko tabo a fatarki pa sahiba to me kuma kikeso, ai sai ki godewa Allah"
For the first time sahiba tace Alhamdulillh, fatabarakallahu Ahsanul khaleeqeen, tabbas salma nayi kuskuren kushewa kaina halittar da ni bazan iya yin koda makamanciyarta ba, amma ki sani nidin daban ce cikin jama'ar dake zagaye dani, im the different one, ni kadai ce mai irin wannan bakin mai irin wannan launin fatar"
Salma ta dafa sahiba, "shiyasa suke ganin kamar tunda ke ba irin su bace to ke ba mai kyau bace wanda ba haka bane, kuma kema kika kara basu dama domin su kara jaddada miki kika basu kofar da zasu tabbatar miki ke ba mai kyau bace tunda ke ba irinsu bace kedin daban ce kuma ke daban ce daban mai kyau"
Sahiba taji wasu hawayen dadi sun silalo mata, babu waanda ya taba zaunar da ita ya mata irin wadannan maganganu masu ratsa zuciya, ba iya zuciyar sahiba kalaman salma suka ratsa ba harda ruhin ta hakan yasa ta soma jin kamar salma ta bude mata wata kofa ne datake ta lalube bataga kofar bama balle mabudinta,"Abinda zan fada miki a karshe dan naga lokaci ya kusa shi ne.... ki dena damuwa da maganganun mutane har kina saka su a rai suna sauya miki tunani, focus on your self tell the world you are beautiful, shi ne lokacin da zakiji duniya ta amsheki matsayin mai kyau, dress nice look beautiful, and smell nice".... Sahiba taji kamar ta rungume malama salma saboda dadi da haka sukai sallama, bayan sahiba ta fito ne sai ta tuna tayi mantuwa tayi saurin komawa office din dayake dama akwai sauran malaman da basu tashi ba, hira taji tana tashi sama sama... Sunanta dataji an ambata ne yasa ta tsaaya tana jin hirar tasu
"Sahiban nan pa wannan baqar yarinyar" dayar tace "ohh nagane yanxu dan Allah wannan bazawara ce"
Dayar malamar tace "eh wlh nima haka naji daliban ajin sauka na fada, wai tayi aure ta fito"
"Ikon Allah da yarintarta amma tana zawarci, yanxu ita wanne namiji ne ma zai aureta a bazawara...." Sahiba tayi walking inside ta dauki littafin dazata dauka a sanda sukai tsit ta fito tana jin kamar ta koma ta gaggaaya musu baqar magana itama yanxu ta soma sanin ciwon kanta, ta dena faking murmushi, she will gather the confidence, taji din ita bazawara ce amma ai ba laifinta bane, mutane basu sanin labarin abinda ke faruwa ko ya faru ba they just judge according to yadda ya musu selfishly wasu ma sai sun kara da karya, which is not right ko kadan, mu dena judging mutun without walking in his shoes akwai daukan haqqi....Sahiba ta fito walking slowly akan titin cikin unguwar tana tunanin maganganunsu da salma, its true bata taba godewa ni'imomin da take dasu ba, a kullun bakincikinta shine launin fatarta wanda mutane suka maida hankali har hakan yasa mata tunanin farin mutun ne kadai mai kyau, kuma gaskiyar salma ne datace tana zagaye ne cikin fararen mutane ko kuma masu dan duhu kadan ita kadai ce launin fatarta daban, shi yasa bata taba zama tayi appreciating kanta ba, dukkuwa da ta tabbata akwai farare dayawa data kere su a kyau nesa ba kusa ba, dama idan mutun zai na kallon abinda bai dashi ko yayi lacking to zai tabbata mara godiya kuma baze taba sanin darajar inda baiyi lacking ba, dukkanmu dama we lack in one way or the other no one is peefect so accept your imperfections and thank the almighty for the blessing, baze taba zama mutun yayi lacking gabadaya ba, kuma bazai taba zama mutun yana komi perfect ba, Allah ya bamu ikon wadatuwa da ni'imar da muke dashi.....
Sultan dake cikin motar zaune thinking of yadda zai fara shiga gidan ya hangeta tun daga nesa ya ganeta, zai iya cewa tunda yake ganinta she's almost always deep in thought, wanda hakanne ke sakashi yaji tausayinta ya kamashi, yanayin yadda take tafiya a hankali a hankali yake kalla, tafiyartata ma sai ta birgeshi, baima san sadda ta matso ba har ta tura kofar gidan yayi saurin fita daga motar wanda itakuma bude motar dayayi yasa ta dan juya without expecting to see someone she knows kawai taga sultan kamar wanda aka hankado daga motar, tayiwa fuskarta ado da murmushi mai kyawun gaske, sultan ya dan diririce yasa hanky ya goge gumin goshinshi kamar wani mara gaskiya ta dan dawo da baya ta tsugunna ta gaidashi, ya Amsa ta cikin farinciki da tarin annashuwa da jinndadi, ta miahu jagora ya shiga har falourn yana cewa "kuma shikkenan sai baki zo kin duba jikin fulani ba" sahiba ta dan kalli sultan a sanda take tuna yadda suka kare da fulani itakuwa mene zai kaita palace ma balle gun fulani, ai duk abinda zai maidata palace to bata qaunarshi a yanxu not ever, bata fata Allah ya maimaita mata zamanta na palace... Sultan ya zauna tace "bari na kira momy" tayi gaba a ranshi yana cewa "gurinki nazo ba gurin momy ba" a zahiri kuma bai iya cewa komai ba sai binta yayi da kallo yana wondering yadda take harkokinta cikin katon hijab din dake mata kyau, saidai yana ji kamar tana takura saboda zapi, babu jimawa momy da sahiba suka dawo a tare ita sahiba da plate na su ruwa da kayan fruits, ta ajiye ta koma sama ya bita da kallo, momy taso lura da irin kallon dayake mata, tace "yau d'ana ya tuna dani, dadina dakai akwai zumunci" sultan yayi murmushi yana kurbar ruwan gorar
Suka dan taba hira da momyn tana tambayar jikin fulani...Sahiba kuwa tana shiga daki gaban mudubi tayi wa kanta matsuguni ta shiga karewa kanta kallo tana mai murmushi, salma ta cire mata mask, mask din dabai taba barinta ta kalli kanta da niyyar ita mai kyau ce ba saidai kullun focus dinta akan launin fatarta yake, ta samu kanta da murmushi cikeda annashuwa... Ita gabadaya tama mance da wani sultan, haka ya karaci zamanshi yana dakon jiran sake ganin sakkowarta amma hakan sam yaqi faruwa hardai ya haqura yayi wa momy sallama yana jira tace "bari a kira maka sahiba kuyi sallama amma itama momyn sai batace ba, ya bar gidan jiki duk a sabule
A daren ranar daya koma palace bayan sallar isha'i mai martaba yayi kiranshi, bayan sultan yaje yayi gaisuwa ne mai mrtava ya amsa ya dora da cewar, "Hutun Amira ya kare zata koma makaranta dan haka inaso a daura auren tunda dama an riga an gama sayayyar komi wannan iftila'i daya gifta shi ya tsaida komi da tuni ma yanxu watakila akwai rabo amma Allah shi ne mapi sani, dan haka kaje ka cigaba da shiri ranar juma'a za'a daura auren in yaso sai kake zuwa can time to time kana ganin matarka"
Tunda mai martaba ya fara wa sultan bayani yaji an ambaci amira kwakwalwar sultan ta toshe, bayaji kuma baya ganin komi a idanunshi sai sahiba daxun nan tana tafe, sai ji yayi mai martaba yace "zaka iya tafiya" ya miqe yana jin kamar ana sukan zuciyarshi da kayoyi, kaya yaje ya sauya yasha ado ya fita a mota, idan ya tsaya bata lokaci lallai za'a samu matsala, gara yaje ya sanar mata kawai ya huta shima... Ya tsaya a kofar gidan bai shiga ba, ya samu yaro ya aika ayi mishi kiran sahiba.....Iska mai dadi ke kadawa datasaka korayen bishiyun suke kadawa yayin da sararin samaniya tayi jaa, walkiya na fitowa lokaci zuwa lokaci
Khalipa ya tsaya enjoying wannan moment din, iskar daminar na kada er rigar dake jikinshi tana ratsa fatar jikinshi, milana ta karaso inda yake zaune yana jin dadin iskar ta zauna gefenshi tace "ka tashi ka koma cikin bukkar ruwa yana gab da sauka" Khalipa ya dubeta yaji wani sonta ya kara rufeshi yace "inaso ki bani dama milana, dan Allah ki bani dama na kula da zuciyarki, dukda nasan nima har yanxu ban iya kukawa da kaina da kyau ba balle na kula da wani amma na miki Alqawari zaki sameni mai rike amanarki mai kula da zuciyarki, ina matuqar kaunarki, it takes alot of courage kapin na samu na fadamiki wadannan kalmomi, karkiyi watsi da soyayyata milana na rokeki" milana ta miqe tsaye tana girgiza kanta a hankali still tana kallon khalipa wanda shima ita din yake kalla.....Not edited
An sassauya team ne kokuwa har yanxu kowa yayi maintaining nashi team din
#one love

YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...