Kamar yadda yake a al'adance cikin gidan sarautar, duk safiya sirikar gidan da sauran matan sarki zasuje su gaida fulani haka yau ma sahiba tayi shiri ta saka dogon hijabinta as always ta fita, 'yan matanta biyu (salima da abida) na take mataa baya, Abida ce ta soma tabo salima a hankali tace "mudai mun hadu da kashin tsiya wlh" ta dan harari bayan sahina "malamar hijabi" cewar salima tana dariya mara sautu, Abida ta bata rai cikin rada take cewa "ke nipa inaga guduwa zanyi daga wannan sashen wlh ace ita ko dan Alkhairin nan da a ke batai, dan abinda muke samu gun fulani ma yanxu shiru tunda muka faraiwa mai kashin tsiya hidima"
Sarai sahiba taji abinda Abida ke fada wani bakinciki ne ya turniketa ta hadiyi yawu mai daci
Ita kwa salima dariya kawae take yadda Abin ya kular da AbidaKoda sukaje sashen fulani tun daga harabar take lura da yadda hadiman fulani ke ja gefe suna gulmarta, wasu fadi suke "wai ita bata da wani hijabi daga wannan sai wannan jan a duniya" kowa in zatazo sashen fulani kwalliya takeci na bajinta amma banda ita, wasunsu kuma su ce "kai ai dole khalipa yaqita mna koni na fita iya wanka"
Sahiba ta dinga binsu da idanunta da suka taru da ruwa wasu taji abinda suke fadi wasu kuma bataji baSahiba ta karasa turakar fulani dake a bude saboda su masu gaisuwa, A farfajiyar falourn ta tadda fulanin zaune cikin wata doguwar riga ta Alfarma tasha aikin daya cika wuyan rigar, hannunta kunnenta wuyanta kuwa gwal ne ke magana, dankwali ne nannade a kanta sannan gyalen daya kwanta tun daga kanta zuwa kan kujerar datake
Sahiba ta zube ta kwashi gaisuwa, suma hadimanta sukabi bayanta, fulani bata amsa ba, hadimanta ne suka amsa sannan su sahiba suka tashi zasu koma, fulani tace "ku bamu guri"
Kan kace me duk hadiman sun fice sun bar fulani da sahiba, sahiba tayi zama na ladabi a gaban fulani kanta a kasa cike da girmamawa
Kamar fulani batason maganar tace "dan wata nawa kike dauke dashi?" Sahiba taji gabanta ya fadi gumi ya keto mata lokaci guda, ta fahimci abinda fulani take nupi tayi shiru cikin rashin sanin abin fada "ana ta yawo dake a baki cewar yarima juya ya aura, kinsan dai a cikin gidan sarauta kike kin kuma san yadda muke girmama tsatson mu dan haka inaso ki tabbatarwa duniya cewar kedin ba juya bace"
Jin fulani tayi shiru na wasu lokutan kuma da alama bata da niyyar dorawa yasa sahiba dan rissinawa ta tashi ta fita batace komi ba
Sauri sauri take tana tare kukan dake taho mata, a lokacin sultan ya fito ya dan hangeta daga nesa sai yabi bayanta dan yanason zuwa gun khalipa dama, tana shiga falournsu ta tadda mamalami tsaye tana jera cups a dining ta karasa ta fada jikinta tana sakin kukan datake ta rikewa,Su Abida suka kalli juna suka tabe baki suka wuce ciki, sultan yayi tsaye daga nesa yana kallon yadda take rera kukan daga cikin zuciyarta kamar zata fidda zuciyarta ta, iya dukkan karpin ta take rera kukan da alama ta dade tana rikeshi yau ta samu ta fidda shi,
Mama ta shiga bubbuga bayan ta a hankli cikin shigar lallashi, kiyi haquri kiyi haquri
Sai yanxu ta soma magana, still tana kukan tace "haqurin nakeyi mama, na fara gajiya da haqurin mama, kowa lapi na yake gani, su Abida ma fadi suke bani da sutura, mama bana aiki, karatun ma banayi mama, sai zaman kadaici babu aikin fari balle na baki, wallahi na gaji mama na gaji, zuciyata ciwo takemin"
Mama ta dan lallaba sahiba da nasiha da ban baki, har Allah yasa tai shiru tana ajiyar zuciya, Mama ta kaita sama daki
Duk abinda ya faru akan idanun sultan ne ya jinjina kai sannan ya fitaAbban su sahiba ya nemi loan na 10 million, dayake yana da hanya da kuma sanayya ya samu, ya damkawa hamma dukiyar domin yin kasuwanci kamar yadda suka tsara,,, hamma ya wuce kasar waje inda zai kafa nashi bussiness din a cewarshi, dadi duk ya ishi momy ganin makudan kudaden da aka bashi dan fara kafa kasuwancin da ake saka ran za'a samu linkin su sau 2 ko uku ma a cewar hamma ma har 4 za'a samu...
Fulani ta takurawa mai martaba da maganar Amira da sultan, dan gani take idan Amira ta auri sultan shi ne kadai zai sa fulani ta juya sultan din ta kuma kula da dukkan motsinshi ta hanyar Amira,
Mai martaba yayi kiran sultan kan maganar Amiran a karo na biyu wannaan karan sai mai martaba yace "na jika shiru akan maganar da mukai dakai kwanaki na ka fidda matar da zaka aura gashi shekaru gaba sukeyi ba baya ba, kara girma kakeyi ko har yanxu laluben akeyi?"
Yarima sultan ya gyada kanshi dake kasa
Mai martaba yace "to ga diyata amira na baka idan har kana ganin babu matsala, sultan yace babu wata matsala mai martaba Allah ya kara nisan kwana"
Wani sanyi mai martaba yaji dan bayason yi ma sultan dole dukda bai ga qaunar Amiran a idanun sultan ba amma yasan Amiranshi is in a safe hand, safest hand for that matter domin sultan mutunne kamili, mai hankali, nutsuwa da sanin yakamata wannan shaida ce da ba iya mai martaba ne ya shaida ba

KAMU SEDANG MEMBACA
WANI YANKI
Romansa"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...