Wattpad @AyshabNasir
A yanda sukai concluding a meeting din shi ne zasuyi aikin a sirrance sai su gwada sannan su fitar da shi ma duniya kowa ya sani,
Aiki ne dake buqatar lokaci da kuma nutsuwa, khalipa da sultan sun shiga busy sosai duk dan ganin komai ya tsaru yadda ya dace, a bangaren fulani itama ba karamin dadin abinda khalipa yazo dashi taji ba ko ba komai d'anta yana abin kirki zatai alfahari dashi...Imran ya shiga CCTV room din, mutun daya ya tadda duk sauran ma'aikatan dake kula da camerorin tsaron sunje gajeran hutu (break), sanin lokacin hutun su ne ya saka ya shiga domin ganin abinda yaketa so ya gani amma ya kasa ko da jin labarin
Ya karasa gurin mai kula da cameras din yace "Oga sultan yace kaje yana can harabar dake kallan ofishinshi, mutumin bai kawo komi ba ya fita abinshi, nan da nan imran ya soma searching na date da kuma cameran dake conference room, dayake ya kware a harkokin computer yasa nan da nan ya gani,
Ya saka headphone domin sauraran abinda suke tattaunawa, tsaf yaji shirin da kamfanin keyi domin kawo sabon hadin simunti wa kasar yayi azamar maida komi yadda yake sannan ya fita, shikuwa ma'aikacin da imran ya turashi gun sultan ya karaci bulayinshi bai ganshi ba ya koma yana tunanin ko ya bar companyn ne a lokacinAbinda su sultan basuso ba shi imran da hashin suka hada kai sukai wato sanarwa 'yan jarida,,
Kashe garin ranar da safe khalipa ya malalo motarshi a miliyan ya hangi taron jama'a a kofar companyn? Duk iya tunaninahi ya kasa tunanin meke faruwa, ya rage gudun motarshi sannan ya fitoAikuwa kamar kura taga nama, sukayo caaaaa a kanshi da tambayoyi, sai khalipa yaji kunnenshi yayi dif tsabar ihun da yawan surutun, shi a tunaninshi ma ya dena ji,
Securities ne suka samu da kyar suka shiga da khalipa sai bubbuga kunnenshi yake, sanda yaje inda babu hayaniyar tukunna yaji kunnen ya mishi daidai, ya saki ajiyar zuciya yana fadin AlhamdulillhYa dauki waya ya sanar da sultan abinda ke faruwa, bai jima ba shima sultan din yazo, ya dan samu yayi calming dinsu suka rage hayaniyar sannan yace "duk ku tapi zamuyi hira da gidan tv a nan zakuji duk amsoshinku mungode da kulawarku a garemu" daga haka shima ya samu aka buda mishi hanya ya wuce, khalipa yace a zafafe "amma duk dan iskan daya sanarwa dujiya aikin nan ya mana shigar wuri, naso nayi surprising mutane yadda zasuso abin sosai, amma yanxu ai sai ayi tarnishing image dinmu a kasuwa ace muna boye wata harkalla ne"
Sultan ya danyi kwafa " Allah ma ya kiyaye in shaa Allah hakan bazata faru ba amma da alama hakan shine burin duk wanda ya fitar da wannan maganar" "So hakan na nupin munada mugun iri cikin companynmu, someone is trying to do something we've got to be very careful daga yanxu" khalipa ya karkareTun kapin su khalipa ma su saka lokacin zuwa hirar gidan tv domin wanke kansu har jita jita ta fara yawo
"Kinji wai an bude wani kamfanin siminti suna sarrafa abinda ba'asani ba kuma sunqi fitowa suyiwa jama'a bayani
"Kinji labarin lauje cikin nadin da masarautar gano ke shiryawa Al'ummarta"
Ire iren wadannan zantuka suka yadu sukai nisan da bama iya gano har wasu garuruwan, da kuma guraren abokan kasuwancinsuBabu shiri sultan da khalipa suka shirya yin live a tv domin duk duniya ta gansu, dukkan su sukaci ado cikin fararen manyan kaya, kai kace en biyu ne in ba dan banbancin kama da suke danyi kadan ba,
Hirar tasu ta fara ne inda d'an jaridar ya tambyesu sunayensu.... Khalipa ya fara fada saboda yapi kusa da dan jaridar
"Khalipa Haidar AAli", "Sultan Nasiruddeen AAli"
Dan jaridar ya cigaba da tambyarsu suna amsa shi kamar haka
"Shekarunku nawa
"27 years both
"Mene matakin karatunku?
"First degree amma na dora" shikuma sultan "First degree
Wanne fanni kuka karanta
"Chemical engineering" "bussiness Admin"
Aure fa?
"Khalipa ya danyi jim yana so yace a'a amma duniya sunsan da bikinshi dukda bawai ansan wace ya aura din ba
"Eh " sultan: "a'a"Jita jita kala kala na yawo a duniya gameda kamfanin simintin ku wanda hakan har ya fara tava reputation na kasuwa cin wannan gari, wanda an kiyasta en kasuwa sun fara shan wahala saboda rashin samun ciniki daga mutane wadanda a da sune kan gaba gurin siyan kayan wannan masarauta ta gano
Khalipa ya danyi gyaran murya
"Duk wadannan jita jita karye ne bamu da wata kulalliyar agenda aiki ne kawai muka fara sabo domin inganta simintin mu inda a cikin kwabin sikintin zamu saka tokar tu6an rake"
Dan jaridar yace "toka kuma a cikin siminti ranka shi dade"
Khalipa yayi nodding
"Kwarai ma kuwa da gaske wannnan bincike ne da aka gavatar dashi kuma kasashen waje dayawa duk sun gwada sun kuma ji dadin hakan shiyasa ma basuyin yanxu siminti zalla ba tareda ita tuban rake a ciki ba
Yadda abin yake shine:
idan aka hada tuban rake da siminti mene result din da ze bada
Mun gano Yana rage yawan shan ruwan da siminti ze yi idan an hada da tokar tu6an rake
Sannan yana rage lokacin bushewarshi, idan an hada da tokan tu6an rake yapi saurin bushewa Sannan Soundness wato kumburin da siminti keyi idan an kwaba siminti anyi plasta, to idan an hada da tu6an rake baya kara kumburi sai ma rage wa dayakeyi kaga wannan babbar nasara ce
And lastly kuma mapi muhimmanci shi ne idan aka hada siminti da tokan tuban rake yana kara mishi karpi da inganci..."
Dan jaridar ya gamsu sosai ya dan tapa mishi sannan yace "masha Allah lallai wannan ba qaramin cigaba ne yazo mana ba, ko ba komai za'a yawaita in gantattun gininnuka bawai kaga gini da an soma rywan sama ko iska mai karpi ya fadi"
Daga haka tambayoyin suka kare sannan sukai sallama da masu kalloFulani dake dakin ta tana kallan duk abinda akeyi tayi wani kasaitaccen murmushi ta dauki tufa dake gabanta ta saka a baki, tun sanda aka fara sukar khalipanta hankalinta ya tashi, ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kasa cin abincin kirki sam, amma yanxu taji hankalinta ya kwanta domin tasan khalipa ya samu daukaka da soyayyar jama'a daga wann firar kuma tasan ya goge duk wani tabo na baya dayakee dashi, ya kulla bakin masu surutu
"Li'ilafi quraish, aniyar kowa ta bishi, kapi karpinsu basu da yadda zasui dakai yarima magajin sarki"Wannan hira ce ta kulle baku nan jama'a ta kuma jawowa Khalipa soyayyar talakawa da masu kudin masarautar harma waje, wadanda ma basu sanshi ba sun sanshi wadanda kuma sun mance kamarshi yanxu sun tuna,
Hashim yayi dariya bayan ya gama kallan firar da akai da khalipa, ya fice kawai yana murmushi,
"Wannan soyayyar da talakawa ke maka itace zata juye ta koma kiyayya"
Ya kira wayar imran yace aikin ka ya kare a kamfanin simintin GanoKomi ya wuce suka kammala hadin farko da zasui trial suka sa aka gina katangar masallacin dake palace aka sauke waccan aka zagayeshi da sabuwar katanga sannan aka bita da ado na gani na fada,
Masu aikin ne sukai ta yabawa da yadda simintin ya musu dadin aiki sosai wannan karon ma sai akai er gajerar fira da masu aikin aka nunawa duniya hoton katangar sannan khalipa yayiwa jama'a albishir na fitowar sabon hadin simintin...Khalioa na zaune a falour bai dade da dawowa ba, kusan karpe 11 na dare ya kunna tv yana dan kallan wani fashion show, sahiba ta fito falourn neman ruwan sha
Ya kalleta da alama bata kula dashi ba, ya kashe tvn ta juya ta kalleshi, har zata dauje kai kuma sai tace "barka da hutawa"
Yasa hannu ya yafitota ta karasa yace "wai dan Allah sai yausshe zaki waye ne what the heck are you wearing this late"
Sahiba ta kalla jikinta, riga ce ta danyi mata yawa ta atampa sai zani single (jaka a tsaye) da daurinshi ya dan karkace
Bata tanka shi dayaga bata da alaman magana ko tafiya sai ya kunna tvn yana cigaba da kalla, itama ta juya ta kalla tvn a ranta tana ayyana
"Saka matsattsun kaya ko kaya masu nuna jikin mutun sune wayewa kenan"?
Ta koma sama dakinta ta bude wadrobe din kayanta tana kallan su, bata da wasu kaya masu yawa, wasu daga cikinsu ma sun jima mata sosai, kuma duk dinkunanta kusan iri daya ne, ita rabonda ma ai mata sabon dinki har ta manta bayan na biki suma kala biyu ne sai kuwa wanda jakadiya ta taba bata ta saka,
Babu wanda ya tabayi mata dinki babu wanda ya taba cewa sahiba man sshafawarki ya kare babu wanda ya taba tunanin ko tana da kayan kwalliya, wanda a zahiri lokacin da sahiba ke gurin fulani duk wata mai martaba yana badawa amma ba'a taba bata ba,
Yanxu kuma data dawo hannun khalipa hakan bai taba zuwa kanshi ba, ta koma ta lumshe idanunta ta kwanta kan tamfatsetsan gadonA bangaren khalipa kuma tunda sahiba ta wuce ya bi bayanta da harara, shi bai tabajin aure irin wannan ba, ace ka dan kalli matarka kaji dadi ma bakai saidai kaji takaici da haushi sun turnike ka,, inama yana da wadda yakeso da kara aure zaiyi, saidai shi har yau baiga macen datai mishi ba, duk zagayenshi ko sai yaushe zai ganta?
itama sahiba a nata bangaren haka ne, batayin wani farincikin idan ta kalli mijin nata saidai taji tsoro ma, taji rashin confidence domin bata san da wacce mummunar kalma zai tunkareta ba
Sorry for the typing errors

ESTÁS LEYENDO
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...