Ashe dai anyi missing sahiba
Tambayoyi milana da sidi sukeyiwa khalipa shikuma ya zuba musu ido dan baisan amsar basu ba... Milana a dan fusace takuma tambayarshi bayan irinta da sidi ya mishi duk dan ta tabbbatar "ya sunanka?" Yace "khalipa" da sauri domin bayason ganin yadda ranta ke baci, gashi dai baisani ba ko hakanne sunanshi ko kuma ba hakanne ba all he can recall is khalipa and sultan a cikin sunayen dake kanshi (memorynshi) suma din tamkar ya tsince su ne dukda yasan yana da alaqa dasu amma yana da strong feeling na cewar khalipa is his name...
To malan khalipa daga ina kake kuma su waye danginka? Domin zaman ka a nan bamai yawa bane munyi namu kokarin gurin taimakon ka dan haka gobe a asubahin fari zaka koma inda ka fito yayi shiru yana sauraren jawabanta can kuma sai yace "im sorry to say is like i ve got some memory loss"
Sidi da milana suka kalli juna, milana dama can haushin shi takeji dan ji take suna cikin hadari duk saboda shi ta bata rai a zafafe tace "malan ka mana da yaren da zamu gane" ganin yadda ta dau dumi lokaci daya yasa shi cewa a sanyaye "na kasa tuno komi daya danganci rayuwata, waye ni dan wanne yanki ne ni, wane mahaifi na wacce rayuwa nayi a baya, na kasa tuno komi sai sunan sultan da khalipa"
Milana ta miqe ta fice sidi ya bita da sauri yana kiran sunanta "sai da ta danyi nisa sannan ta juyo ta tsaya tace "sidi ka sallami mutumin nan tun yanxu ya kama hanyarshi"
"Amma Milana kema kinsan jikinshi ba wani kwari yayi ba, ke kika ce babu ishasshen jini a jikin kalli yadda fatar shi tayi dau saboda rashin jini, gashi jikin babu kwari ga....." Milana ta dagawa sidi hannu "duk kai ka sani ni babu ruwana ta wuceshi ta shige bukkarta yayi tsaye shidai Allah ya sani baze iya korar khalipa ba, musamman yadda khalipan yake fada musu bai tuna komai ba dayayi a baya hakan na nupin ko hanyar garinsu bai sani ba,
Tabbas shigowar shi yankin Naghar akwai zanen kaddara domin yanki ne dake cike da tarin boyayyun sirrika.....Milana's Point of view (POV)
Nafi sidi son mu taimakawa wannan bakon, tun a ranar dana fara ganinshi na fahimci daga wanne yanki yake, kuma kamar naso na fahimci dan wanne gida ne, sanda na ganshi a kwance a yashe na kare mishi kallo a cikin wannan kallon nayi zargin shi ne yarima khalipa, daga yanayin yadda aka siffanta mini shi da yanayin sutura da fatar jikinshi,, sai gashi ya kuma tabbatar min daa cewar shi dinne...
Na sa hannu na dakko littafin dake ajiye a sama cikin jerin littafan dake cikin dakin, suke a shirye a ajiye daga gefe, na dade ina karanta wannan littafi, littafi ne daya kunshi duk tarihin yankin arewa a yankin da masarautar Gano da Haye suke, babu masarautar danafi maimaita tarihinta kamar masarautar Gano, a hankali na dakko sabon littafin da malan ya taho mini dashi, rubutun ajami ne domin shi ne kadai rubutun da yankinmu suke fahimta,, littafi ne daya kunshi sabbin abubuwan da suke faruwa a masarautun yankin Arewa, na buda shafin ina cigaba da karantawa cikeda annashuwa domin ni mutun ce mai son karatu......End of Milana's POV
Yankin Masarautar Gano
Saida fulani Hamida tayi sati biyu cir a gadon asibiti kapin ta farfado ta soma gane mutane, su kansu likitocin sun soma fidda rai da ita sun ce saidai miracle ne kadai zai tada ta, aikuwa sai gashi ta farka din, tun da ta farka kuwa babu abinda take sai kuka, yini take tana kuka saidai in bacci ya dauke ta, su Amira sunyi lallashin duniya amma inaa bata kulasu, ita kadai tasan irin ciwon da zuciyarta keyi mata, kashegarin ranar da fulani ta farka ne Sultan yaji labari, dan haka ya shirya zuwa dubata, saidai tunda yaje ko kallon inda yake fulani bataiba balle yasa ran zata koda amsa sallamarshi ne, tun yana ganin kamar wasa har ya haqura ya tafiyarshi, sultan ji yake a ranshi yafi fulani jin mutuwar khalipa, kuma haka dinne domin indai kasan sultan kuma ka ganshi yanxu sai ka dan girgiza saboda yadda ya chanja lokaci daya, ya wani rame ya kara tsayi, fuskarshi ta zama kamar babu nama, sultan gani yake kamar barin jikinshi guda aka cire aka yar,,, matsayin khalipa a ranshi yapi tunani mai tunani
Koda ya koma fada sai ya wuce bangaren khalipa, babu kowa a falourn direct ya hau sama zuwa dakin khalipa, yana murdawa ya jishi a bude babu ma wanda yazo bangaren kenan inba tsirarun mutane da sukazo wa sahiba gaisuwa ba, wasu ma mantawa suke yanada mata, Sultan ya shiga dakin yana kallon yadda bedsheet din yake a gyare, sai ya samu kamshi da tsugunnawa gaban bedsheet din zuciyarshi a raunane, so yake yayi kuka amma hawayen sunqi zuwa sai zapi da zuciyarshi keyi anya ba hawayenshi suka kare ba dan bai taba tunanin zai iya zirga zirga ba a wannan jimami daya shiga, a nan a tsugunnne yana saka da warwara wani bacci mai nauyi ya daukeshi, ya dora kanshi a kan gadon jikinshi kuma yana kasa....

ВЫ ЧИТАЕТЕ
WANI YANKI
Любовные романы"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...