Bismillahir Rahmanir rahim
Birnin Gano (modern estate)
(10 years)
Ta fito daga kofar makarantar islamiyar hasken jar ranar dake yamma tana shirn faduwa ya haska bakar fatarta, tasaka tapin hannunta ta dan kare ranar tana sanye da coffee din uniform riga doguwa sakakka sai wando a ciki sannan hijab wanda ya kai guiwarta duka coffee sai suka sake mayar da bakar fatarta tai duhu.
Hannu taji an sakala a kafadarta, ta sauke hannuta data kare fuskarta tana juyowa ta kalli kawartata.Yau ma suka jero kamar kullum idan aka tashi daga makarantar islamiyar yamma da suke zuwa suka karasa bakin titin dake estate din wanda baida nisa daga islamiyar, daya fara ce amma ba tas ba tanada kyan fusska daidai gwargwado, dayar kuma baka ce sosai fuskarta har shining take dukkansu dogaye ne la'akari da shekarunsu,
Farar cikin bacin rai tace "kepa Sahiba ba er fari ba amma sai rashin wayo da wayewa suka miki katutu"
Wacce aka kira sahiba tayi shiruu tana kallon dayar da fararen manyan idanunta
Jin tayi shiru yasa farar tadora "duk wani wulaqanci kece kike jawomin shi,, shiyasa duk dalibai ke kallonki kamar mujiya cikinsu"
ta fara kiciniyar dakko abu cikin jakarta, babu jimawa ta ciro wani mai a tub ta mika mata
"Ki fara shafa wannan, nan da kwanaki uku ma zaki ga kin fara haske"
Sahiba ta kurawa man dake kan tafin hannunta ido tana jujjuyashi ta furta fumbact A bayan ta harhada dan english din ta
Farar tace "eh haka sunanshi yake"
Sahiba ta sauke ajiyar zuciya "amma hanan kin manta wa'azin da malan Salihu ke mana kullum, Allah fa ya hana mutun ya chanja halittarshi, bakya tsoron na shiga wuta"
Hanan tayi guntun murmushi, nidai na baki kwana uku idan baki canja wannan mummunar fuskar taki ba babu ni babu ke dan bazaki dinga ja min raini ba"
Idanun Sahiba suka kawo ruwa "yanxu kan wannan abin zaki rabu dani aminiyarki" sahiba tayi furcin tana jujjuya man dake hannunta
Cikin sigar lallashi Hanan ke fadin
"Kowa ya waye yanxu Sahiba, kowa ci gaba yake nema, kuma idan kika shafa gyara miki fata zaiyi tayi sumul ai gyaran jiki ba haram bane"
Chanja kalar fatar kuma fa?" Cewar Sahiba
Wannan ma cikin gyaran jiki ne ai, karki manta kefa mace ce itakuwa mace sae da gyara, mace kowa yasan 'yar kwalliya ce d ado
Hanan ta dafa kafadar sahiba
"Kinga mutuniyar ki shafa kema sai kiga kin fito tas cikin kawaye, duk wannan hantarar da ake miki zaki ga an dena babu mai kyamarki har a gida ma"
Sahiba ta maimaita kalmomin karshe "har a gida ma?
"Eh mana ke bakiga banbancin da ake nuna miki ba ai saboda ke mummuna ce shiyasa"
Hanan tasa hannu ta tare mai napep ta shige tana dagawa sahiba hannuMummuna, shi ne kalmar data tsaya a labban Sahiba, ta juya a hankali ta soma bin cikin estate din, gaban wani tafkeken gida ta karasa, kato ne, tasa hannu ta tura katuwar kofar ta shige gidan, cikin drive in din taga motoci da dan dama, nan da nan ta nemi damuwarta ta rasa ta ayyana a ranta yau Hamma ya dawo kenan, ta dan sa gudu tayi main hanyar shiga gidan, a falour ta tadda momy na fitowa daga kitchen tayi ado, hakan ya sake tabbatr mata da cewar ba iya hamma bane harda Abbah.
Ta gaisa da momy sannan ta tapi sama da dan gudunta take hawa stairs din, Sahiba karamar yarinya ce da dududu batapi shekaru goma sha biyu a duniya ba, ta taso a gidan arziki, mahaifinta Alhaji Aminullah sani mai kaba dan kasuwa ne kuma yana hulda da en siyasa sosai dukda shi bai taba fitowa takara ba amma idan gwamnatinsu taci zabe shima yana samun Alkhairin hakan, matanshi uku hajiya Samira (momy) itace matarshi ta biyu wacce yanxu itace matsayin uwargidanshi sakamakon rasuwa da mahaifiyar Sahiba (uwargidanshi) tayi bayan ta haifi sahiba da watanni shida
Momy jinin sarauta ce domin cousin ce gurin mai martaba sarkin Gano,
sai kuma Amaryarshi wacce bata taba samun haihuwa ba mai suna Salma suke kiranta Anty
Sahiba Bata rasa ci ko sha ko sutura ba saidai ta rasa shaquwar mahaifiya ta taso cikin kadaici dan kowa a gidan harkarshi yakeyi, momy bata taba kyamarta ba amma bata jawota a jiki ba, sahiba ta jima da sanin mamanta bata da rai sai ta alaqanta kadaicinta da rashin qanne da bata dasu yayanta kwalli daya kuma Hamma Anas bata ganinshi itadai bazata tuna yaushe ta ganshi cikin gidan nan ba,
Ko yaushe yana makaranta in anyi hutu kuma baya zama kullum yawo ko main house ma bai shigowa, takan ganshi a hoton dake ajiye a falour, wani sa'in ita kanta har tmbyar kanta take anya itada Hamma en uwa ne domin ita dashi ko kama basayi, she's black shikuma fari ne tas.... Abbanta ma bata taba zama gata gashi ba kullum yana sararin samaniya saboda kasuwancinshi duk sanda ya dawo kuwa shima bai nemanta batasan dalili ba amma ta yarda a ranta bashi da lokaci ne, hakan yasa bata da abokin hira batada kuma abokin shawara kowa nashi harkar yakeyi a cikin gidan,
Ta cire uniform dinta ta shiga tayi wanka ta fito, ta tadda daya daga cikin masu aikin momy ta kawo wasu kaya itama yarinya ce kamarta saidai ta dan girme mata da shekaru 3 zuwa 4
"Gashi ki chanja momy tace in kawo miki"
Da murna ta karbi kayan dake hannun Habiba
En kanti ne purple da akayi ado da cream flower ta warware rigar tana kalla a mirror tana dorawa a jikinta sai ta ajiye ta dubi habiba da itama sai murmushi take
"Habiba biki akeyi ne?" tace "ya aakayi baki sani ba, Alhajinku ne ya hadawa Hamma Anas lifayar cin abinci na murnar haihuwarshi" murmushin kan fuskar Sahiba ya dan ragu ta shiga tunani, itakam ko birth date dinta ma bata sani ba,
Habiba ta katse ta da fadin "karfe 8 za'a fara kiyi maza ki shirya kafin lokacin"
Ta zauna jiki a sanyaye a yadda tunaninta yakeson kaita "kamar Abbah yapison Hamma akaina" tayi furucin a fili batareda tasan ya fito ba
"Ai ba kamar bane Wannan hakan take" taji muryar kishiyar momy amaryar Alhaji kenan wacce bata taba haihuwa ba a gidan
Ta dago da sauri ta kalleta, da alama wucewa tazo yi ta kofar dakin nata dan hannunta rike yake da wasu kaya,
Ta dan zauna kan gadon Sahiba, Sahiba ta maida hankali tana son jin abinda Anty zata fada
"Ba ke bama har mu matanshi har dukiyarshi yapison Anas a kansu, abanza ne ya daukeshi ya zabi makarantar datapi kowacce ya sakashi ke kuma ya barki a makarantar unguwa ko driver be ajiye miki ba balle mota, sai dai ki taka da kafa kije, ai ko uwar data kawoshi duniya ma anpi fifita ta akaina akan uwarki kuma"
Sahiba taji maganar ta Anty kamar zagi, taji zuciyarta tana mata baki
Anty tayi kamar zata tapi sai kuma ta ce "the earlier u believe baki da wani amfani a gidan nan the better"
Tana karashe fada ta fita. Sahiba ta girgiza kanta, a ranta tana karyata maganar anty amma zuciyarta na son ta yarda da abinda anty ta fada, "kishi ne kawai anty keyi dan Abbah yapison momy"tayi concluding tanason kwantrwa kanta hankali amma sai ta kasa samun nutsuwar, tun before 8 sahiba ta gama shiryawa dan tanason zuwa gurin Abbanta, tanaso ta fadamishi ta kusa saukar Al'qurani tana so taji irin tanadin da zaiyi da farincikin da ze bayyana gareshi idan ta sanar mishi tana gab da sauka kuma zata juya hadda idan batayi amfani da wannan damar ba tasan ba lallai ya dawo kafin saukar tasu ba, tunda akan nemi iyayen yara amma Abbanta bai taba zuwa taron iyaye da akeyi ba"Da zumudinta ta bar main house ta wuce da sauri inda tafkeken falournshi yake, ta shiga, babu kowa a falourn tsit sai ta jiyo kamar motsi ta dubi kofar dakinshi inda taji motsin
Momy ce da Abbanta suke fitowa Sahiba ta wangale baki tana dariya ganin Abban nata, ta tapi da gudu ta daneshi, gif taji ta fadi kasa kamar wani kayan wanki, a gigice ta dago kanta daya bugu da tiles din kasan,
Bata fahimci abinda ya faru ba, dagaske Abbanta ne ya yakice ta ajikinshi ya ture da karpi haka batareda tsoron zata ji mummunan rauni ba, ko momy ce, ta girgza kanta momy a gefe take ma. "Ke baki da nutsuwa ko" sai ya kalli momy "kin gani ko shiyasa fa ni sam banason 'YA'YA MATA gaba dayansu liability ne bassu da wani amfani"...
A take murmushi ya bayyana fuskar dady sakamakon shigowar Hamma Anas,
Come here my Son ya fada yana tunkararshi yana buda mishi hannunshi suka danyi side hug sai suka fara hirar school.
A wajen Abbah ya zaro wata takarda daga aljihunshi ya miqa ma Hamma "my birthday gift" cewar Abbah
Hamma ya buda takardar yana son fahimtar abinda aka rubuta dan harga Allah ba wai ya iya karatu bane duk kuwa tsayin zaman dayake a makaranta
"Ur admission to london" Abbah ya sawwaqe mishi karantawar.
Dukda maganar Abbah data daki zuciyar Sahiba wacce bata taba tsammaninta ba sai taji tayiwa d'an uwan nata murna,
Hamma yace "thank you dady"
Abbah ya dan daki kafadar hamma sannan yace " u re welcome my son"
A hankali sahiba tace "congrat Hamma" sanda ta miqe tsaye
Sai a lokacin ya lura da ita cikin falourn, ya tsina fuska kamar ya ga kashi, " u re too black, i mean u re ugly" sai duk suka sa dariya su uku banda Sahiba da sam maganar tashi batai mata kama da zolaya ba tapi kama da cin fuska kuma gaskiyar daya fada tun daga cikin zuciyarshi
"Are u still here"? Cewar Abbah cikin kyama
Sai taji hawaye sun zubo mata ta juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki walking slowly har ta fita a falourn direct dakinta ta koma wondering anya Abbah ne mahaifintaMaganganun Hanan suka dawo mata suka tsaya cak a kirjin Sahiba,, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, she's kinda tall, black in complexion, so black, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin mummunar bakar fatarta, manyan fararen idanunta suka kawo ruwa ta shafa fuskarta a cikin ranta ta ayyana "ni mummuna ce", kalman suka huda zuciyarta tamkar ta saka mashi mai tsini ta tsikari naman zuciyarta da kanta, duka taji wani confidence dinta yana bin iska yana guduwa yana barinta. Nan kan mirror dinta ta bar man da hanan ta bata ta kuma cire kayan data saka ta koma kan gadonta ta kwanta tana jin kadaici mai tsanani tamkar ita kadai tai saura a duniya.
Bacci takeso tayi amma tunani sunyiwa kanta yawa
"ni sam banason 'YA'YA MATA gaba dayansu liability ne bassu da wani amfani"
Maganganun dady suka dawo mata "liability" ta fada tanajin zuciyarta na karyewa "I'm i that worthless cikin gidan mahaifina?" Tambayar da take so ta samu amsarta kenan
"Eh mana ke bakiga banbancin da ake nuna miki ba ai saboda ke mummuna ce shiyasa"
Sai taji kamar wadancan kalmomin na Hanan sun amsa tambayarta "saboda ni bak'a ce kuma saboda ni macece shiyasa Abbah baya sona kawayena suke kyamata kamar mujiya cikin tsuntsaye"
Tayi juyi tana tunanin mafita a haka bacci mai nauyi ya dauke ta yayinda a can kasa kuma aketa shagalin birthday party din hamma Anas na cikarshi shekaru Ashirin a duniyaKashegari data tashi bata fita ba sai datayi wanka tayi shirin makaranta purple uniform ne riga da wando ta warware gashin ta dake cikin ribbon, baki sidik mai santsi wanda ya kwanta har a goshinta, dogo ne daya wuce tsayin wuyanta, ta saka comb ta tajeshi ta maida ribbon tana ji kamar ta yankeshi, ita kanta tasan tana da gashi mai kyau amma who cares, mene amfaninshi tunda rufewa za'ayi?
Ta daura dankwalinta white sannan ta sauka kasa duk ranta bai mata dadi yau tun abinda ya faru jiya bai bar zuciyarta ba, a dining din main falour kamar yadda ta saba ta zuba nata abincin taci sannan ta koma ta saka hijab ta dauki jakarta tayi hanyar fita dan tasan duk matan gidan babu wadda ta tashi as always,
Saida ta fita harabar gidan sai ta lura da yawan motocin dake gidan, nan take taji wani tunani yazo mata, ta kalli hanyar part din Abbah ta kuma kalli hanyar part din Hamma, sai ta rasa wanne zataje atlast tai concluding ta tura kofar mai nauyi a hankali, ta saka kafa cikin katon falourn, babu kowa shiru sai karar na'urori, tayi hanyar bedroom din datake zargin nashi ne, ba kamar yadda tai tsammani yana bacci ba, taa rike handle din kenan shikuma ya fito.. Ta danyi murmushi shikuma ya yatsina fuska
"Hamma tunda ka shirya dan Allah ka saukeni a makaranta"

VOCÊ ESTÁ LENDO
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...