Takardar da mai martaba ya wulla musu, takardar karatunsu ce, daya ta khalipa dayar ta Sultan, gwamnati ta dauki nauyin karatun kowanne d'a guda a kowacce masarauta dake kasar, da saka ran matasan da ake tunanin sune manyan gobe masu jiran gado zasu zama masu ilimi domin samun jagorori na gari..
A masarautar Gano yarima Khaleepa suka za6a shikuma mai martaba sai ya biyawa Sultan dan su tapi tare suyi karatun.Khaleepa na zaune kan tsakiyar katon gadonshi gabadaya ya tapi tunani, hadiminshi kuma na gefe yana ta deba mishi kayan da zai bukata har yama rasa wanne ze dauka mashi wanne zai bari saboda tsabar yawan kayayyakin yarima,
Sultan ya shigo dakin bakinshi dauke da sallama, ya buda idanu ganin kato barar da hadimin ke ma khaleepa, ya dubi khaleepan yaga ya tsunduma duniyar tunani, sultan yayi ma hadimin alamu da hannu ya je kawai,
Sultan da kanshi ya hadama khaleepa kaya, kadan ya dibar mashi cikin kayan masu muhimmanci, duk abinda su Sultan suke khalipa yana jin su. Sultan ya dan juya ya dubi khaleep gabadaya he's not himself sai kace ba Khaleepa ba, its unlike khaleepa ya zauna haka yayi shiru,
Sultan ya taaba kafadarshi, shikuma khaleepa ya daga ido ya dubeshi yana mai sauke ajiyar zuciya, "dan za'a maka aure shi ne kake ta damuwa haka, aure pa ni'ima ce ka godewa Allah tun kana karaminka zaka samu wannan ni'ima" khaleepa ya harareshi "ni bana son wani ni'ima" ya fada yana ture hannun sultan dake kafadarshi,
Sultan ya rike baki "Ahh lallai yaro ka habaka, wake gudun ni'ima to" khaleepa ya harareshi,, sultan ya fita yana murmushi, da wuya ne ya shiga gurin khalifa be fito yana murmushi ba, a haka samarin suka kama hanya bayan sunyi sallama da iyayensu, koda sukaje sallama da fulani, sam taki fitowa dan tayi fushi da yariman nata, ta hana a barshi ya shiga, a nan bakin kofar turakarta ya tsugunna yadda yasan zata jishi yace "Albarkarki nake nema ummi na, addu'arki nake buqata ummi na, ni ban isa komi ba bazan aikata komi ba sai da support dinki ummi na, kiyimin aikin gafara ko na samu nasarar karatun da zanje yi" Fulani dake dakinta tana jinshi ta goge hawayenta, tana so ta fita amma baqar zuciyarta bazata barta ba in ta tuno abinda yayi
Haka ya karaci tsugunnonshi ya tashi ya shafa kofar dakin ya juya ya tapi cikin sanyin jiki, tunda taji alamun ya soma tafiya tace "kaje Allah ya maka Albarka addu'ata kuma tana gareka yarimana, make me proud"
Ita fulani gani take idan ta nuna mishi bakomai zaije ya sakeyin abinda yapi wannan nema gara ta nuna mishi mistake dinshi domin ya gyara batason taji ko kadan ance khalipanta yayi wani kuskure domin hakan na rage mishi daraja ne matsayinshi na mai jiran gadon GanoSanda suka je airport suka gane kusan su kadai ne suka makara domin ga sauran 'ya'yan sarakunan duk sun hallara, kasancewar Gano na gaba da kowacce masarauta yasa airport na Gano yazama meeting point. Hashim ya cikaa ya batse ya hade girar sama da kasa, khalipa ya daga musu hannu shikuma sultan ya bisu daya bayan daya sukai musabiha, su shidda ne gaba dayansu and the journey begins
Kamar yadda mai martaba yayi Alkawari haka ya daurama d'anshi khaleepa aure da yarinyar da sam khaleepa besan wacece ba.
Sahiba na cikin kuryar daki tana tunanin wannan saurayin daya sauketa kwanakin baya, daga dukkan alamu yasanta tunda har ya ambaci asalin sunan hamma kuma ya kawo ta har gida ba tareda ta kwatanta mishi ba, amma ita sam bata sanshi ba, kodayake dangin nasu yawa gareshisakon kiran Abbah ya isketa, ta nemi hijab da niqab dinta ta daure fuskarta, a dakin momy ta sameshi suna hira da momyn, bata rai yayi yace "mene wannan a fuskarki sahiba, maza cireshi" ya bata umarni tun bata amsa mashi tambayar tashi ba. Babu musu ta cire fuskarta ta bayyana.
Daddy yace "to ki zauna ki nutsu ki saurari abinda momy zata sanar miki
Sahiba ta gyada kai a hankali, daga haka Abbah ya fita ya barsu su biyu sahiba da momy
Momy ta kamo kafadar sahiba ta zaunar da ita kusa da ita kan gadon, sahiba taji wani banbarakwai tunda hakan bai taba faruwa ba
Momy tace
"Sahiba ke kamar diya ce a gurina, baki da banbanci da Anas duk daya na daukeku, dan haka kisani ni da mahaifinki babu wanda ze maki abin da ze cuceki,,
Sahiba ta gyada kai tanajin gabanta na dukan tara tara, tabbas akwai wani abu da momy ke buqata ita da Abbah dan babu wanda cikinsu ya taba mata kalamai masu dadi haka hadda zaunar da ita kan gado, dakin ma idan ba aikene ba ba shiga take ba aiken ma dududu sau nawa ne.
Ta tsinkayo muryar momy na fadin "a yau Abbanki ya bada aurenki" sahiba taji kamar bata gane ba, ta kalli momy da sauri tana so taga ko daga bakin momy taji kalaman ko kuma kunnenta ya soma jiye jiye,
Momy ta gyada mata kai, sahiba ta kurawa momy idanu ko kiftawa batai, tanason momy tace mata bataji daidai ba,
Momy ta kama hannayen sahiba ta rike, hakika ke diya ce ta Albarka, wannan aure kuma biyayya ce zaki mana ki nunawa duniya ke diyace da iyayenta ke Alfahari dasu
Sai hawaye suka sakko bisa idanun sahiba a lokacin data dauke idanunta daga kallon datake ma momy
"Ubangiji Allah ya maki Albarka," sahiba bata iya amsawa ba saboda kukan datake me ciwo wanda beda sauti
Tambayoyi ne fal ranta
"Dama ana yiwa yarinya kamar ita aure?" Ko dai Abbah ya gaji da ganina yayimin aure? Ko na zame mishi liability ne dama kamar yadda yake fade"?...

YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...