A sanda sultan ya ida parking ruwan saman ya tsagaita sai dan yayyafi shima irin jepi jepi ne gari yayi sanyi, sararin samaniya tayi wasai,
Sahiba tasa kafafunta wajen motar mama lami ta dan kamata suka fito, shima sultan ya ida kashe motar ya fito ya musu jagora, suka bishi a baya, Hashim da tun shigowarsu ya zuba masu na mujiya daga windown apartment dinshi yayi murmushi dan babu wanda baisan labarin auren khalipa da aka daura tun shekaru 5 da suka gabata ba.
Babu kowa cikin gidan, sahiba ta samu guri ta zauna tana sake jera atishawa, kayan da suka jike a jikinta ma sun bushe a jikin nata,
Sultan ya kalleta cikeda tausayawa, he's never seen an innocent soul kamar ta, bala'in tausayinta yake haka nan, da alama sultan ne mutun na farko yaga farin sahiba batareda judging da skin colour dinta ba (launin fatarta)Sultan ya nunawa mama lami dakin da zasu kai kayansu, dakine da babu komai a cikinshi sai carpet dake nannade a jingine dan madaidaici, cikin kankanin lokaci mama lami ta share dakin ta goge ta wanke bandakin sannan sahiba ta samu ta shiga tayi wanka, shikuma sultan ya fita nema musu duk abinda yasan zasu bukata
Ta gidanshi ya biya dan dakko katin bankinshi, can ya tadda khalipa a kwance a dakinshi yana ta ayyukanshi da system, bai kulashi ba ya kama hanyarshi bayan ya dauki abinda yazo nema,Sultan ya tabbatar su sahiba bazasu nemi komai ba dan saida ya bar musu komai a gidan ya kuma nunawa mama lami ko ina a cikin gidan harda d'akin khalipa dake a garqame, tareda mata dukkan bayanai sannan ya tapi zuwa nashi harkokin daya katse saboda su
Sahiba dake kwance kan kujerar falourn tanaji wani zazzabi na sake kokarin rufeta, danma Allah yasa sultan ya taimaka mata da magunguna, ta dubi mama lami tace "a cikin su biyun wane yarima khalipan?"
Mamalami tace "a cikin su wa da suwa?
Sahiba ta aza idanunta kan hoton dayake ta dauke mata ido tun shigowarsu ta kasa dena kalla tace "tsakanin wancan ta nuna hoton khalipa jikin wani frame da akaiwa ado da design na sarauta, yasha manyan kayan da suka kawatu da aikin hannu na sarauta white and green, kanshi sanye da hula green kalar aikin kayan da wani rufaffen takalmi a kafarshi na sarauta mai azabar kyau shima green, dukda kyawun da kayan sukai sai sahiba taga sam basuyi kyau ba domin wanda ke sanye da kayan yapi kayan kyau, wani sheki yake a cikin hoton da sahiba take gani kamar yana barazanar kashe mata idanunta da basuda cikakkiyar lafiya saboda dukan ruwan saman daya samesu amma dukda haka bata fata ta dena kallon wannan halittar "tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu"
"Da kuma wanda ya kawomu"
Sahiba ta karashe maganar ta tana mai kasa janye idanunta daga kallon hoton khalipa domin a sanda take kara kallon hoton nashi tanaji kamar yana sake kara kyau ne,Mama lami tai murmushi ganin sahiba na kallon hoton khalipa tana murmushin da bata ma san tanai ba,
Mama lami ta dafa sahiba wanda hakan ya katse mata jin dadin datake ciki
"Wancan shi ne yarima khalipa"
Sahiba ta kuma aza idanunta kan hoton sai taji duk zapin da idon ke mata ya dena....
Shi ne yarima Khalipa, shi ne wanda aka daura mata aurr dashi kenan, shi ne angonta na shekaru biyar,
Daga gani zai dakko halayya daa dattaku irin na mai martaba ne,
Da alama karamci a jikinshi yake, fara'a da nutsuwa kawai take hanga in ta kalli bright picturen shi,
Ko sultan ma ya kasance ma'abocin kirki da hankali ga tarin karamci da nutsuwar datagani tattare dashi to inaga yarima mai jiran gadon gano, babban d'a a gurin mai martaba,A yadda khalipa yayi niyya shi ne yayi zamanshi a gidan sultan har sanda su sahiba zasu gaji su kama hanyar su, amma kuma sai yaga to mene ma na buyan ita wacece da baze tunkareta ba shida gidanshi...
Wayar khalipa ta soma kiran sallah ya miqe yana ayyana "zanje gidan muyita ta kare"
Har ya fito sultan kuma na kokarin shiga kamar bazasu kula juna ba kuma sai sultan ya dan tsaya gaban khalipa yace "diya ce gurin momyn su Anas kuma kasan matsayin momy gun mai martaba, ka kula da ita she's so innocent... i mean the girl" ya karashe maganar yana shafa dan sajenshi dayayiwa fuskarshi ado da cikon kamala,Khalipa ya dubi idanun sultan ya tabbatar bada wasa yakee mishi maganar ba sai yaji a ranshi zata iya cin Albarkacin sultan
A hankali fuskar sultan dake a hade ta soma smiling slowly, murmushin sultan ya ratsa zafaffiyar zuciyar khalipa sai yaji yayi sanyi tamkar an zubawa garwashi ruwan sanyi ya zama toka shima a hankali tashi fuskar ta bada lallausan murmushi, sultan ya dan daddaki kafadar khalipa sannan yasaka hannu a aljihu ya dakko car key ya bashi yace goodnight... khalipa ya dan lumshe idanu sannan ya wuce
![](https://img.wattpad.com/cover/261597110-288-k51934.jpg)
VOUS LISEZ
WANI YANKI
Roman d'amour"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...