Sahiba ta koma daki jiki a mace, "mene dalilin dayasa ake boyeta daga dangin mamanta tabbas akwai alamar tambaya, sai Kuma ta tuna abinda Abban yace a cikin zancenshi "Ai ni banso ma kika yi gaggawar dawowa ba, danma sultan din ya matsa ne,....." Ita bata ma san sultan ne ya matsa ba inba yanxu dataji daga bakin Abbah ba.... Kashegari sahiba ta shirya kamar yadda sukai da Abbah ta bishi ya saka ta a bayan motarshi momy na gaba, shikuma yana tukawa kamar a mafarki sahiba a motar Abbah chab ashe za'ai ruwa da kankara, suka je asibiti aka turasu lab, akayi gwaje gwajen da za'ai sannan aka ce su dawo da yamma karban result sabida akwai mutane, suka tapi sahiba na mamakin wannan lamari haka nan Abbah ya matsa sai an mata gwajin ciki,
Can da magariba abbah yasa ayi mishi kiran sahiba, tasan dalilin kiran tana shiga falourn kuwa sai fada ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,
Duk ina amfanin zamanki a gidan yadda kikaje a babu haka kika dawomin a tutar babu, kawai tuwo kikaje ci ma kenan
Yaja wani dogon tsaki cike da jin haushin diyar tashi, momy ta sallameta sahiba taa tapi jiki a ssanyaye...Yankin Naghar
Milana tai kwance a cikin bukkar kusa da mama bayan gyaran bukkar malan da sukai suka kimtsa komai suka rufe mishi bukkar,, sidi ya cigaba da zarya gaban bukkar su milana tun jiya da yamma yake rokonta Allah annabi ta duba jikin khalipa ya rikice amma tayi banza dashi kmar bata san yanayi ba.. Haka yau ma jikin nashi babu dadi magana ma dakyar yakeyi,
Tana ta tunanin shin ta taimakeshi ko ta barshi yasha wahala ya mutu su huta? Amma in ya mutu kuma akwai Alhaki a kanta domin mutuwar tashi a haka yapi karpin tsautsayi, ta tashi ta bar mama dake bacci a lokacin da gari yayi duhu, ta fito sidi ya karasa gareta a sukwane, tace "ya jikin nashi yake" yace "muje ki gani"
Suka wuce bukkar tare da sauri yana kwance yama kasa kwakkwaran motsi sai idanunshi daketa tsiyayar da hawaye, ta durqusa kusa dashi "ina ke maka ciwo?" Bai iya mata magana baka sai hawaye dake fita daga idanunshi babu kwakkwautawa, ta kalli ruwan magungunan tace sidi baisha ko daya ba dama sidi yace yace bai iya sha wai babu dadi
Milana tayi tsaki "kuma shi ne ka biye mishi ai gashi nan jikin yadda ya zama" ta dakko jikon ta buda mishi baki da taimakon sidi ta zuba mishi yayi ta hadiya kuwa sannan tace da sidi ga wannan anjima kadan ka sake bashi daga haka ta fita ta barsu tana jimami domin harda yunwa ma data soma kama khalipn gashi jikin ya sake rikicewa dama warkewarshi sai a hankali dan yanada tsawon rai a gaba....Khalipa ya kumayin sati a kwance yana jin azabar ciwo batareda yana fahimtar wasu aabubuwan ba, da taimakon Allah da kuma taimakon da milana ke mishi da kulawar sidi a kanshi ya samu ya dan farfado har yake iya dan zama amma jikin babu dadi, dole ce kadai ke saka khalipa shan wadan nan ruwan magungunan tunda yaga suna taimakawa jikin nashi, gashi bayanshi sai ciwo yake mishi saboda kwanciya kwanciyar ma kan gadon kara, sam abin is not easy a gareshi...
Ganin da milana tayi ya soma samun dama dama jikin yana samun progress yasa yau ta kawo mishi abincin dare shima kuma yunwa yakeji kamar yaci babu, tuwo ne baki yasha miyar kuka da man shanu sai kifi (dayake yanki ne mai wadatar kifaye saboda ruwan da suke dashi) ta taho mishi da yajin daddawa dan yaji dadin ciYana zaune babu riga a jikinshi sai wani wando na sidi ya miqe kafarshi jikin babu dadi ko kadan yana tari lokaci lokaci ta karaso ta ajiye mishi tuwon ya dubeta kadan tace "ga abinci ka samu kaci shi ne zai sa jikin naka ya kuma yin kwari".... Ya kalli kwanon abincin ya saka hannunshi na hagu ya buda haka nan yaji ranshi ya baci yace "wannan kuma mene" tace in ka gama ci na fada maka" ya girgiza kanshi yana tabe baki "banjin zan iya cin wannan ya ajiye murfin ya juyar da kanshi
Milana tace "ita yunwa ai ba qanwar uban mutun bace" ta sa kai ta fice abinta ya bita da kallo yanaji bazai taba cin wannan abin ba...Can cikin dare wata azababbiyar yunwa ta rufe khalipa jikinshi har rawa yake tun yana tunanin zai iya jurewa yaga kaiiii inaaaaa baima sa sadda ya jawo kwanon ba jiki na bari ko gani baiyi duk tuwon ma ya rigadaya huce ya dinga kai lomomi hannu baka hannu kwarya, sidi dake kwance yana kallonshi yaji dariya ta subuce mishi, saida yaji cikinshi yayi nak ya sude hannu ya ajiye kwanon gefe ba dadewa bacci mai dadin gaske ya daukeshi,
Kashegarin ranar da yamma khalipa ya jawo sidi yace kashi naakeji ka rakani bayi, sidi yace to ka jira sai yamma tayi gari ya fara duhu karmu fita a ganka, shi khalipa ya dauka mutan gidan da daliban milana sidi ke nupi
Da gari yayi duhu suka kama hanyar dawa, tafiya suke kamar basu dainawa, khalipa ya samu dutse ya zauna yace kafafuna zasu cire idan na cigaba da wannan tafiyar, na gaji sidi ya dubi yar karamar tafiyar da sukai yace to ai ko rabi bamuyi ba
A hankali muryar sidi ta koma muryar sultan a kunnen khalipa sai flash na memoryn sanda sukai wannan tafiyar a school ya dan hasko cikin kwakwalwarshi ya gano sanda sultan ke jefa mishi mukulli, sai kuma yaji dimm ya kasa tuno komi daga wannan ya dubi sidi yace "nipa bayi nace ka kaini ba mubar gari ba" hmm lallai ma inji sidi ya dawo ya zauna kusa da khalipa "shikkenan sai mu cigaba da zama har sanda zaka huta mu karasa
Sun dan jima sun tadi khalipa na tambayar sidi wai nan wanne yanki ne kuma cikin watta kasar
Sidi yace "bani da tarihi sosai nasan sunan wannan yankin Naghar" ka tambayi milana zakasha labari....Suka karasa cikin dan jeji sidi yace "inka gama kayi tsarki, ya bashi ruwa"
Khalipa yace bangane ba ina masai? Ai a mantuwar ban manta cewar a masai ake bahaya ba" sidi ya ggirgiza kai bansan wani masai ba kaidai kawai kayi a nan ina jiranka kayi sauri"
Khalipa ya girgiza kai inaaaa yace da sidi na fasa kalli pa gurin babu ko tsafta sidi yace amma bazaka tadani tsakar dare ba ko? Khalipa yace ai na fasa sun soma komawa kenan kuma khalipa yace sidi jirani ya dan koma da dan gudu sidi yasa dariya.
.
.Sati biyu bayan nan
A hankali a hankali jikin khalipa ya dinga yin kyau dayake milana kwararriya ce tasan takan magungunan gargajiya su sassake iri iri, murar ce ta rage a jikin shi sai kuma rashin kwari jiki da baida shi, to dama khalipa ko da can ma jikin ina yaga wani kwarin arziki, kusan kullun sai milana da khalipa sunyi fada tana kulawa dashi kawai saboda ihsani a yadda take ce mishi kullun,
Fadan nasu baya wuce akan rashin jin magana irin ta khalipa da rana kwalleliya in tana shirin zuwa gun dalibanta suyi karatu sai ya fitittike shima fita zaiyi baya zama a daka ya gaji wani sa'in sun dinga musu kenan wani sa'in kuma hararshi kawai takeyi ta wuce idan ta harareshi sai yayi murmushi domin yanajin hararar tata na shiga har cikin zuciyarshi komi nata so yake
He can't lie anymore yana sonta yana kaunarta amma zai dan jinkirta fada mata zuwa sanda zai tuna wasu parts na memorynshiYankin Gano
Sahiba ta gaji da zaman gidan zaman takabar da tasan bayi take ba zaman kadaici da rashin abinyi zaman kadai zai iya saka mata cuta koma tace ya saka mata domin she feels depressed as always, amma bazata yarda sam da wannan zaman gidan ba domin idan tace sai ta jira har ta gama takabar hakan na nupin zata kara zaman wata biyu da kwanaki kenan gaskiya batai wa kanta wannan fatan kuma tana buqatar cigaba
Saida tasan sanda Abbah ya dawo ta dauki yan kafafunta ta karasa turakarshi tayi sa'a ta sameshi shi kadai yana kallo ta tsugunna ta gaidashi kamar baze amsata ba har ta gaji tana shirin fada mishi dalilin zuwant yace ya akayi
Tace "Abbah dama inaso na koma makaranta ne, inaso na sake jamb na gwada applying admission ko zan samu"
Ya ajiye remote din hannunshi ya kalleta tana cigaba da jawabinta "inason karatun computer Abbah kuma tunda yanxu ba inda nake zuwa zepi idan na cigaba da karatun".... Ki dena mafarki
Kalaman Abbah suka katse mata hanzari "in banda shashanci irin naki me akeyi da karatun mata mene amfaninshi, ke mace ai gidan miji ne inda ya dace dake dama to balle ke kina bazarawa kije jami'a kina jawomin magana kikeso ko, to ni a gidana budurwa ma bata wuce sakandiri balle bazawara"Kalmar bazawara dataji daga bakin mahaifinta yapi kowacce kalma yi mata ciwo da zapi,,, ashe itapa yanxu ta koma bazawara innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ashe haka wannan kalma ke da zapi da kuna, ashe haka wadanda ake fadawa sukeji....muryar Abbah ta dawo da ita hayyacinta a sanda yake cewa "ki tashi ki barmin nan shakara kawai" Ta tashi tana gani bibbiyu tana hada hanya Allah ne kadai ya kaita dakinta ta zauna kan tiles dij ta saki kuka...
Na tsani mahaifi na banason mahaifinaA cikin masarauta kuwa
Fulani duk ta rikice kamar wadda ta zauce, bata da aiki sai bala'i da hadimai babu mai iya mata kullun masifa, ko mai martaba dena mishi magana tayi Amira ce kadai take iya controlling dinta itama sai ta sha fama, duk ta rame ta lalace cikin lokaci kadan,
Galadima yasa akai mishi kiran jikan nashi Sultan, yaje ya amsa kiran galadima yana cikin wani falournshi mai kyau, sultan ya miqa gaisuwa gun dattijon nashi kafin galadima ya soma mishi bayanin dalilin kiranshi
"Haba yarima sultan dubi yadda ka rame ka lalace kamar wanda ake cinye naamanshi kullun" sultan ya sake dukar dakai domin baida amsar da zai bashi shi kadai yasan me yakeji a zuciyarshi shi kadai yasan yadda mutuwar yarima ke dawo mishi a kullun, shi kadai yasan yadda yake tsananin son yabi khalipa,
"Ka dena damuwa dan Allah ka rage ka rage, ka rasa mahaifinka da mahaifiyarka ma ka rayu da maraici, shima zai zama tarihi dukkanmu nan lokaci muke jira, ka zama mai tawakkali, ka yawaita sadaka gareshi ka yawaita addu'a sune abinda yakeso bawai damuwarka ba"...
Sultan a ranshi yace tabbas ya rasa iyayenshi kuma ya rayu, ya rayu saboda khalipa bai taba sakawa yaji cewan shi maraya bane he's always by his side sun shaqu ne iya shaquwa
Amma in shaa Allah zai dage da yin abubuwanda khalipan zai zama Alkhairi a gareshi kamar yadda galadima da sahiba sukace din sadaka da addu'a zai dage kwarai
Zan dage ranka shi dade Allah ya kara nisan kwana" sultan ya Amsashi
Ya gyara zama yace "to magana nakeso muyi kan maganar aurenka da Amira wanda nasan sun jinkirta ne saboda wannan mutuwar tunda an gama komi, inaso ka nuna bakason Amira kanada wadda kakeso nasan mai martaba baze matsa ba in kayi hakan kuma akwai diyar Alkali sunanta Khadija, kaje ku sasanta kafin su tado da maganarku da Amira dan bazeyu ka auri amira ba indai nine na haifi uwarka..... Sultan ya dago ya kalli cikin idon galadima suka hada ido#not edited
#team khalipa
#team sultan
#team milana
#team sahiba
#team Amira
#team khadija lol

YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...