Tun lokacin da sultan ya kira wayar sahiba yaji switched off yaji gabanshi ya yanke ya fadi, ya samu ya karanto hasbunallahu wa ni'imal wakeel... Yana kokarin kwantarwa da kanshi hankali, gabadaya ba'a ankara babu amarya ba motar amarya ba sai da kowa ya gama zuwa aka nemi motar amarya aka rasa, lokacin kuwa har anyi kiran magariba, sultan baisan da hakan ba yana tsaye jikin dokinshi hadimin daya aika ya taho da gudu ya zube yana haki.. Cikin muryarshi da bata fita sosai saboda haki yake sanarwa da yarima sultan lallai pa ba'aga gimbiyar tashi ba, innalillahi wa inna ilaihi raji'un shi ne abu na farko yazo kan labbanshi, zuciyarshi tayi rauni yana mai jin tsoro, yasan lallai sahiba cikin makiya zata shigo, ta kowanne bangare domin wadanda basu son auren nasu suna da yawa, amma harda kidnapping, bai taba zata abin har yayi zurfin haka ba, bai san kiyayyar da akewa zamansu ya kai girman hakan ba, saidai ya rigada yasha alwashi he's more than ready to fight the world for her, he will protect his wife in shaa Allah,
Yasa hannu ya maza ya ciro wayarshi a Aljihu ya kira wannan security agent din da sukai survey din motar, a sanda yayi survey din yayi ne bada tunanin za'a sace mishi mata ba saidan tsaro, da kuma samun nutsuwar zuciyarshi ya dinga jin motsinta a koda yaushe amma tunda abin ya kai har haka lallai ana farautar rayuwar matarshi ne, ko a ina take yasan she needs him yanajin haka a zuciyarshi, he can feel her heart calling, calling only him
Agent kamar yadda sultan ke fadama security din da sultan ya kirashi ya mishi bayanin abinda ke faruwa sannan yace yayi tracking inda motar take shima gashi nan zuwa
Babu wata cikakkiyar nutsuwa haka sultan yayi sallah ya fita da dan sauri ya sanarwa mai martaba inda zaije ta waya, yaja mota ya karasa gurin agent daketa faman aiki a office, yana da kayan aiki kuma kwararre ne, amma dukda haka sun danyi searching na wasu lokuta saboda network kapin location din motar ya bayyana.... Sultan kamar yayi tsuntsuwa haaka yakeji duk ya kasa zaune ya kasa tsaye burinshi ya karasa ga masoyiyarshi,
Ya karanci location din yasa a wayarshi navigator ya mishi kwatance filla filla, agent yace sultan ka jira yanxu xan gama hada securities sai mu tapi gabadaya, sultan ya girgiza kanshi.... Ko jiran second daya bazan iya ba" shine reply din sultan ya fita da sauri saidai yana fita yayi rashin sa'a motarshi taqi tashi
Bakincikin daya tsaya mishi a makogwaro ji yake kamar yasa kuka, kawai sai ga wani hadiminshi ya karaso tareda doki
Yayi gaisuwa gun sultan sannan yace "mai martaba ne yace nazo na kula dakai, bayason fitarka kai daya" sultan yace "ka jirani a nan" ya karbi linzamin dokin nan da nan ya haye yayi gaba da gudu kan dokin, Yana godewa Allah cikin ranshi, ko kadan baiganin zunkudar da dokin keyi dashi burinshi ya karasa gareta a haka ya shafe wannan tafiyar.. Cikin sa'a a daidai sanda ya karaso suma motocin securities din suka karaso, and a lokacin ne ya hangeta a kofar gidan baisan sadda ma yayi wata muguwar dirowa daga kan dokin ba tun bai ida tsayawa ba dokin yayi haniniya sultan da dukkan karpin shi yasa gudu ya taho gareta ganin yadda take jan jiki a hankali tanason karasowa gareshi bai san sadda wasu hawaye suka wanke mishi fuska ba ganin halin da take ciki, ya riketa gam a jikinshi sannan yayi commanding securities din su kare matarshi,
Kidnappers din da suka fito sukaga tulin securities sun zagaye ko ina da bindigogin su fully armed sai suka farayin ta kansu nan da nan suka nema back exit suka bar gidan ta boyayyar hanya... Sultan bai san da Anty ba baima yi wani tunani ba, all he cares about a lokacin shi ne matarshi amaryarshi ta suma.... Agent ya hadashi da wasu securities uku da mota dan kai ta asibiti ta samu taimakon gaggawa.... Nan da nan aka karbi sahiba akayi treating ciwukanta likitan ya sanarwa da sultan in shaa Allah babu wani abu shock ne kawai, yanxu ta samu bacci nan da wasu awanni kadan zata farka... Sultan ya shiga dakin yana kallonta sleeping peacefully da dan guntun hawaye a gefen idanunta ya karasa bakin gadon yaja kujera ya zauna yana jin tausayinta, yanxu ta shigo cikin sabuwar rayuwa, rayuwa mai cikeda kalubale, zata fuskanci abubuwa duk saboda matsayin da yake dashi a fada da kuma son da yake mata, saidai zaiyi iyakar kokarinshi ganin koma wanne hali ne batai fighting ita daya ba, zai kasance a tareda ita duk rintsi duk wuya in shaa Allah, that will be his promise... Agent ne ya kirashi ya sanar dashi sun samu anty amma basuyi nasarar kama ko mutun daya ba, suma gasu nan zuwa asibitin,,, sultan ya ajiye wayar sannan ya kira mai martaba Ya sanar dashi, duk yadda akai yace basai kowa yazo ba yana tare da securities, gobe da safe zasu dawo in shaa Allah idan aka tabbatar da lafiyarsu....

ESTÁS LEYENDO
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...