Episode 23: Sahiba

26 3 0
                                    

Ranar haka khalipa ya kwana yana tunanin yankin nasu da milana ta bashi labari yana ta iya kokarinshi ya tuno kalmar naghar ko wani abu daya danganceta daya sani amma inaa ya kasa tuna komai kamar an toshe kwakwalwar tashi....
Yau ma su milana suka zauna karatu da khalipa shima sidi ya shigo cikin karatun na yau, saboda duk ayyukan nashi na yau bassu da yawa, milana tana bi dalla dalla tana karanta mishi amma duk iya kokarinta kamar baya gaane komi ma, takaici ne ya kama mioana ta rufe Alqur'anin tace "wai nikam izifin ka nawa ne" khalipa ya danyi shiru yana tunani kamin yace "mene ma izifi?" Ta harareshi cikin jin takaici, nikam wacce irin rayuwa kayi a baya ne kodai kaidin ba musulmi bane"..... "Auzubillahi... Koda na manta wasu parta na memory na ai bazan kasa tuna ubangiji na da addini na ba, ni musulmi ne tunda kin sha ganina inaa sallah, kuma kema kin gani ai na kawo miki surorin kasan nan duka" milana tace "ka dai biya izu biyu shima da qur'ani da tarin gyare gyare, manzon Allah yayi gaskiya dayace shi karatun yaro karami kamar rubutu ne akan dutse shikuwa na babba kamar rubutu ne akan ruwa... Da ace ka daki bita sanda kana yaro da duk haka bata faru ba, mene amfanin rayuwar musulmi idan bai san ubangijin da yake bautawa ba balle kuma yasan hakkokin musulmi yan uwanshi a kanshi ya iya zama dasu batareda ya shiga hakkinsu ba... Ina mai baka shawara khalipa ka guara yanayin lafazinka, mu'amularka da mahaliccinka da kuma mutanen dake tare dakai, yadda musulmi zasu kubuta daga harshenka da hannunka ka zamto mafi alkhairin musulmi fadin manzo Allah SAW, ka maida hankali ka samu ilimi a iya dan zaman naan da zamuyi dan na tabbata zamanka a nan ba na tsayin lokaci bane domin a ko yaushe aka gano ka zamanka ya kare inkuwa ba haka ba to nasan duk randa malan ya dawo zai gano da zamanka kuma shima zamanmu tare ya kare kenan"
Khalipa yaji duk ranshi babu dadi, he feel ashamed of his lack of education a sound islamic education, tabbas shi ilimi haske ne na rayuwa musamman na addini domin shine zai haska duniyarka da lahirar when used in the proper way and manner Allah ya bamu ikon aikata daidai Amin abu na biyu daya sake tadama khalipa hankali shi ne furucin milana na cewar zamansu tare ba dawwamamme bane, how can she says that a yanda yakeji cikin zuciyarshi baze taba iya rabuwa da ita ba, its love from first sight amma harr yanxu ya kasa gathering courage and confidence ya tunkareta da maganar, a niyyarshi shine ya sanar mata kwana kusa amma zaiyi kokari ya samu ilimi mai yawa yadda zatai alfahari dashi in yaso sai ya sanar mata.... yana tsoron rejection..... Tun daga wannan ranar Khalipa pa sai ya dage, safe rana dare karatu, allunan shi har biyu ne yanxu bayan karatu ma harda rubutu yakeyi wanda hakan yayi wa milana matuqar dadi,,,, yanxu basa wani fada da milana, babu irin abincin kauye na gargajiya da bai iya ci ba, skin din da khalipa ke ji da ita yanxu wanka ma ba kullun yakeyi ba, tunda su maza sai sunje can gurin ruwa sannan suyi wanka shikuwa dama khalipa da tsoron ruwa bai iya swimming ba tun da... Sai in milanna ta zo mishi karatu taga alamun baiyi wanka bane tace to yau babu karatu, hakan ne yasaka yake dan zuwa ya wawwatsa shima baya shiga cikin ruwa, tun yana fama da mura ma har ya saba da kuma taimakon shayin da milanan ke hada musu duk dare saboda itama ma'abociyar muran ce domin yanki ne mai wadatar sanyi da damshi
Turaren wutan da milana ta tsuma ne ta tuno dashi yau tashinta taji muradin konawa ta debi wuta cikin garwashin sanwar karin safe da aka sauke ta zuba abin turaren sidi da khalipa basu tashi ba suna baccin safe babu yadda milana batai dasu ba amma ta haqura ta kyalesu dan sidi duk randa baiyi baccin safen nan ba to baze moru ba shikuwa gogan dama ba wani moruwar arziki yake ba

Baccin shi yake mai dadi kan shimfidar buzun da yayi sallar Asubahin safe, hancinshi ya jiyo kamshin hayakin da ya shiga har cikin kwakwalwarshi, a hankali wasu memories suka soma dawo mishi na hargitsi kamar a cikin bacci,, gida ne kato ya ganshi a ciki dukda hoton gidan baiyi haske ba amma hakan baze hanashi gane irin girma da tsari da gidan kedashi ba, anyi kwalliya a tsakar babban dakin da kujeru still ga matattakala, ya shigo gidan yana tari yana jin shigen kaurin turaren sai ga wata yar doguwar budurwa da baze iya tantance fuskarta ba amma jikinta samye yake da oversize doguwar rigar da baze iya tantance colourta ba... A cikin kanshi yake jin murya irin tashi tana dakawa budurwar tsawa inda itakuma fuskarta ta nuna bataji dadin hakan ba... Sai yaji mafarkin ya kare amma muryoyi kala kala sun cika mishi kunne kuma dukka suna daya suke ambata
Sahiba sahiba sahiba...... Who is sahiba
Wace sahiba yayi saurin budaa idanunshi bakinshi na ambaton Sahiba, khalipa ya sunkui da kanshi dayaji kamar zai dare biyu, still bakinshi na motsi yana furta sahiba, wace sahiba, mene hadinshi da sahiba dayayi mafarki da ita...
Ciwon kan ya matsawa khalipa haka yayi wunin ranae a kwamce da ciwon kai yanaji zucoyarshi na mishi daci duk sanda ya furta sunan sahiba, he's pretty sure koma wace sahiba to lallai akwai wani bad abu tsakaninsu....

Yankin Gano
Sahiba ta kammala takabarta takabar da ita kadai tasan yinta baida amfani domin babu takaba a kanta... rayuwar ta sahiba gabadaya babu canji kuma babu cigaba tayi magiyar gun Abbah amma sam yace bazai taba barinta zuwa wata jami'a ba balle ma tana bazawara, yayi asarar kudi kuma yayi asarar mutunci jama'a su zageshi shikam baze dauka ba, data matsa ma zagi ya bita dashi hadda kafa, momy bata saka baki ba balle kuma anty da ba jin tata ake ba... Choice biyu sahiba take dashi, na farko kodai ta gudu ta shiga duniya ko kuma tayi haquri ta cigaba da wannan bakin zaman tayi addu'a... Kyakkyawar zuciyar sahiba bata barta ta zabi zabin farko ba sai ta haqura dana biyu, tana zaune tana rera karatun qur'anin tana kuma zubda hawaye sai kawai wata idea ta fado mata, aikuwa tana ida karatun ta rufe Alqur'anin ta shafa addu'o'inta ta miqe dama tana sanye da hijab ta dauki niqabinta ta lullube fuskarta karma wani ya aibanta mata halitta ta sakko ta fita a gidan,, already Abbah ya bar kasar ya shiga harkokinshi shida dawowa kuma sai sun ganshi,, makarantar islamiyarsu data baro ta karasa tana tuna ko bikin sauka abbah bai barta tayi ba ya aurar da ita, ta karasa makarantar ta samu ba abinda ya chanja duk malaman data sani dayawansu suna nan sai ma karin wasu malaman da aka samu, wasu daliban kuma data sani suna yara duk sun girma ita dinma ai ta girma shekaru kusan bakwai ai ba wasa ba, malamin su ta samu a ofishin malaman makarantar ta karasa ta gaidashi, dayake shi kadai ne cikin ofishin, ya amsa ta cikeda jin dadin sake a ganinta a sanda ta yaye niqab din fuskarta
"Sahiba ashe zan sake ganinki" tayi dariyar data fito da dogon hancinta, "malam habibu ashe baka mance dani ba ashe zaka ganeni"
Yace ai ko tsufa kikai sahiba zan ganeki gaki nan kamarki bata sauya ba ai"
Ta gyara zama tace "malan ina zaune babu abinda nake a gida, inda hali inaso nazo na dinga koyar da qur'ani da wasu littafan dana koya kuma idan da lokaci nima sai na kawo hadda tunda bamuyi hadda ba lokacin a biya min wasu littafan, malan habibu yce masha Allah to meze hana kuwa sahiba wannan tsarawa zamuyi sai muga ajin da zamu baki sannan sai a samu malamin dake da free time sanda baki da aji shima baida aji a miki naki karatun, anjima zamu tattauna idan aka tashi in shaa Allah duk baze gagara ba, ki bani zuwa gobe sai ki dawo kiji yadda aka tsara, mu dama ai munfiso muga tsofaffin dalibanmu sun zama malamai, akan mu dakko sabbin malamai"
"Alhamdulillh nagode sosai malan"  bayan sahiba ta gaggaisa da wasu malaman da daliban ne ta fito ta kalli titin sai takeji kamar jiya ne sanda suke fitowa tare da hanan aminiyarta ta hau napep ita kuma ta koma cikin estate din a kafa, da ace tana da kudin napep da ta hau taje gidansu hanan bata san gidan exactly ba amma tasan unguwarsu kuma hanan tace mata gidansu ba boyayye bane, sun tsara zata je gidan nasu da bikin saukarsu ne amma Allah baiyi hakan zata faru ba......


A cikin palace kuwa bayan faman zaryar asibiti da addu'a da mai martaba ya sa aka tashi tsaye anai fulani ta dan fara samun sauki, jiki yana kyau yanxu tana samu taci abinci ta kuma dena rigingimu kawai dai ta zama so silent kamar ba fulani ba, haka nan sai kuna zaune kuga tana zubda hawaye,,, sai Amira tazo tayi lallashi tukunna ta dena kukan ita kadai ce tasan yadda abin keyi mata ciwo, son duniya ne kadai ya hanata kashe kanta...
Sultan yayi tsaye gaban calendar jiyace ranar daya zagaye a calendar rannar dayake saaka ran sahiba zata gama takabarta dukda deep down yanaji a ranshi cewar babu takaba a kanta cos ya san khalipa kamar yunwar cikinshi, yasan yadda yake kushe sahiba baze taba tunkararta da sunan wata mu'amula ba makamanciyar wannan,,,, zuciyarshi na fuzgarshi yaje yaga sahiban amma gabanshi na faduwa akai akai, yanaso yaje yaga halim datake ciki ya sanar mata itace zabinshi amma ya kasa duk confidence da jarumta irin na sultan shikam ya gaza a wannan fannin, bai taba soyayya da wata yarinya ba bai taba jin son wata cikin ranshi haka ba, har ya damu da duk wani motsinta ya damu da damuwarta, shi baima san sadda tausayinta ya juye ya koma soyayya ba, soyayya kuma irin wannan mai karpin gaske, tamkar iskar guguwa mai karpi na tafiya dashi yana tangadi haka yake layi a cikin begen sahiba amma taya zai soma sanar mata da hakan batareda tayi wani tunani ba, batareda taji tsoron kada abinda khalipa ya mata ya sake faruwa ba, how?

Kashegarin ranar khalipa ya tashi yanajin bugun zuciyar tashi na karuwa, tunda ya kwanta mafarki ne kala kala na sahiba yakeyi, how cute her lips are how innocent her face is, how beautiful and pretty she is naturally,,, ya kamata ya gwada sa'ar shi, amma he's too afraid so so afraid of rejection

Not edited
One love

WANI YANKIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt