Episode 16: MILANA

33 8 0
                                        

Wattpad @ AyshabNasir


Fulani tai kiran su ciroma a waya tace "ku aiwatar da abinda mukai magana akai kar ya wuce daren yau" ciroma yace to amma a inda matsalar take shi ne mai martaba ya hana fita..... aikin lallai hazeyu cikin gidan nan ba
"Duk hanyar da zaku bi nidai kawai kubi, ko bakaga yadda talakawa ke zagi da cin mutuncin yarima khalipa ba, kai a haka kana ganin zai samu support koda ya hau mulkin ne? Dole mu nunawa duniya basu da wani za6i idan ba yarima khalipa ba"
To amma bikin su da Amira kuma pa? Hakan zai...."
Dakata ni ba wani dogon hira nake so ko jin ra'ayinka ba, dama ni ce na hada wannan aure yanxu kuma barinshi duniya yapi auren muhimmanci"  fulani ta katse kiran tana mai huci da jin zapin abinda taga anaiwa khalipan nata, nan pa ciroma da dan iya suka soma aiwatar da aikin fulani amma duk jikkunan su sunyi sanyi domin ji suke kamar abin bazeyu ba amma dai haka suka samu suka tsiyaye ruwan batirin motarshi a dole sai yayi kalar mutuwar da ubanshi yayi inma bai mutu ba sun ajiye wasu da zasu karasa shi, kuma sun tsiyaye ruwan ne a yadda bazai fahimta da wuri ba har sai yayi nisan da bazeji kira ba....

Khalipa ya shigo gidan nasu feeling lonely and devastated, shikuwa mene yayiwa wanda ya mishi wannan abin, shi mutun ne mai son farinciki a ko yaushe baya son abinda zai taba farinciki da kwanciyar hankalinshi, sai gashi bai dami farincikin kowa ba shi ana farautar komi nashi har Carrier din da bai gama building bama, people are just too cruel, sahiba ta fito ta ganshi zaune yayi nisa cikin tunani so deep, har yana zubda hawaye ma bai sani ba, ta karaso ta dan tsugunna gefenshi tana cire mishi takalman karfarshi, baiyi realizing ba saida hannunta suka dan gogi kafarshi sanda ta daga kafar zata cire takalmin ya dan kalli inda take yaji wani takaici, yasa hannu ya tureta yana galla mata harara, sahiba taja gefe tana tunanin "anya akwai wani abu da zatayi a duniya ta birgeshi kamar yasan tunanin da take yace "ki dena wani shisshige min malama kina wani yin kwalliya kinje an shafa miki wani abu kamr dorawa a jiki, fatarki daban shi daban, ko zaki na lashe kafata bazaki birgeni ba u are just not my type" ya tashi yai gaba fuuuuu

Ta bishi da kallo a sanda taji dumin hawaye kan kuncinta, sai ta maida idanunta kan hannayenta, kurkur dinne dorawa, kuma ina ma yellon kurkur din ya fito zau da zai mata wannan bakar maganar, kodai dagaske yake dama haka kowa ke kallonta?..... Gurin sultan ya wuce ya tadda sultan din ya shiga wanka, ya hau kan gadonshi sai kuma yaji baya ma son ganin sultan din for the first time in his life yaji he just need to be alone, har y fita kuma yaji ya rasa gurin zuwa ya koma inda yaga car key kusa da wayar shi khalipa yasaka haannu ya dauki car key din ya bar bangaren sultan

Sultan yayi sauri yana shiryawa saboda sako dayazo mishi cewar yaje ya karbowa mai martaba wani sako kuma kar yaje da khalipa saboda abinda ke faruwa, ya gama shiri sai ya nemi car key ko sama ko kasa, ha'a shidai ya tabbata tare ya ciresu da wayarshi daga Aljihu amma me? Sai waya babu car key, a hankali ya kalla dakin nashi yana assessing yanayin canjin dakin, sanda ya shiga wanka gadonshi a gyare yake tsaf babu komai kan gadon amma yanzu yaga kamar alamun an hau, yaji gabanshi yayi mummunar faduwa tabbas khalipa ya shigo, kuma dama tun daxu yake ce mishi ya kyaleshi he wants to be alone, khalipa ya dau car key amma ina yaje,,, Gossssshhhh
Sultan ya fita da sauri cikin wani yanayi, ya tadda babu motarshi da dan gudu ya karasa gurin su sahiba ya tambaya tace ai ya jima da fita, ya nemi mukullin motar khalipan shima ya dauka yayi hanyar fita aikuwa yana zuwa gurin gate suka sanar mishi sunga fitarshi amma basu ma gane ba sultan ne cikin motar ba dan ko tsayawa baiyi ba ya wuce da gudu, suma ganin speed dinshi yasa sukai azamar bude gate harma ya kusa shot da dayan mai gadin suka nunawa sultan hanyar  nidayabi ba bata lokaci sultan ya bishi


Khalipa yayi nisa sosai kawai dama burinshi ya bar cikin garin, cikin hayaniyar da yake ganin kamar bazata taba qarewa ba ya dan sha iska, batareda wata damuwa ko wani suka ba, a hankali ya soma kokarin slowing down dan yana ganin yayi nisan daya kamata ya tsaya amma sai kuma me? Sam brake yaqi ci, tun bai gane ba har ya gane y dinga takawa akai akai yana zage karpinshi amma sam ya gane bafa karpi ne abin ba....
Ya hadiyi wani yawu mai dacin gaske yana jin wani fitsari na taho mishi, sai kuma ya sami kanshi da zubda hawayenshi, so shikkenan a haka zan mutu?, lokaci na har ya kare a duniya babu d'a ko jika without achieving all of my big dreams without making mai martaba and ummi proud, sultan,, sultan,,, sultan!! Ya samu kanshi yana maimaita sunan sultan din a bakinshi
Mugun gudu motar takeyi wanda gabadaya ya kasa controlling ma, sai yake ji kamar ya saki sitiyarin ya kalla har sanda zai mutu amma kuma sai yaji daddadar muryar sultan a kunneshi na mishi rada "never give up khalipa".... Sai yaji wasu zafafan hawaye sun zubo mishi, how will sultan live without khalipa amma maybe is for the better tunda yasan sultan gwarzo ne zai iya jurewa maybe inda sultan dinne ya mutu shi baze jure ba,
"Be safe sultan" muryarshi na rawa ya furta hakan,,,
Motace ta tunkaro shi kuma still ga wata a gabanshi duk yadda yake lissafin ya zaiyi ya kauce amma ya kasa, kawai sai wata kwana ta bayyana without a second thought ya fada kwanar har tsalle motar tayi, ya cigaba da tsula gudu bai ma san ina yake zuwa ba dan gabadaya ya sauka a kan kwalta duk inda yaga kwana fadawa yake haka ya fito wani katon titi kamar ma ya bar kasar a yadda yake lissafi, batareda ya lura ba yaganshi cikin tsaunika baisan lokacin da motar ta bigi wata bishiya ba, kamar an fiddo shi a motar yayi tsalle ya fada cikin wani tafki dake cannn gaba da motar a lokacin khalipa baisan inda kanshi yake ba.......

Sultan kuwa hankalinshi ya gama tashi yayi neman duniya amma sam ya kasa samun khalipa, a bangaren su ciroma kuwa kira yaje musu daga gurij masu gadi cewar fa lallai yarima khalipa ne ya fita ba wai sultan ba a cikin motar, domin dama sunyi communicating dasu sanda suka shirya tuggun, sai suka zauna suka dau carbi domin basu isa su kaiwa fulani wannan labarin ba,,, sultan ya koma gida yaga ko khalipa ya koma bayan ya gaji da yawo amma sai baiga khalipa ba yaga dai abin na neman zama babba ya je bangaren fulani da kanshi, bawai gaisuwa ce ta kaishi ba kaamar yadda ya zama baya shiga gurinta inba gaisuwa ba ranar daya taddata gun mai martaba ma shikkenan amma yau ya zama dole ya je gareta

Tana falour tana jiran jin labari mai dadi dan su ciroma sun sanar mata da fitar sultan a sanda khalipa ya fita suka dauka sultan ne amma bisa ga mamaki sai taga shigowar sultan gurinta ta miqe a zabure tana rarraba idanu,,, daga ina kake? Inace ka fita? Sai sultan ya danyi jimm ta ina tasan ya fita? Ko dama tana bibiyarshi ne? amma kuma shi duk ba wannan ba ya shiga sanar mata abinda ya kawoshi ta tsugunna ta dago sultan "kai ban gane me kake cewa ba a wacce motar khalipan ya fita?" Yace a motata ne ranki ya dade sai ta daga hannayenta ta sauke mishi mummunan mari a fuska da dukkan iya karpin sannan ta tureshi ta fita ta barshi a nan
Sultan ya razana da jin saukar mari ya rike fuskarshi amma ganin fulani ta fita da sauri sai ya zauna yana kara neman layin khalipan dukda ba yanxu ne karan farko ko na biyu ko na uku dayake kira ana sanar mishi layin a rufe yake ba amma ya kasa haqura gani yake idan bai dena nema ba zaiyi nasara amma inaaa



Fukani tafiya kawai take batareda ma ta lura ko takalmi babu a kafarta ba burinta kawai takai gun mai martaba a ceto mata d'anta dan in khalipa ya mutu to tabbas itama bazata rayuwa ba kaiiiii inaaa bama zai taba mutuwa ba ba mutuwa sai yayi mulkin gano sai ya nunawa duniya shi mai iko ne shi mai mulki ne,, direct turakar mai martaba ta wuce bata ko tsaya sauraran dogaran dake fada mata dayar matar sarki na ciki, da alama ko ji ma fulani batai, ta hankada kofar ta taddasu zaune su biyun suna dan tattaunawa, idanun fulani ma da alama basu gani da kyau domin bataga kowa ba sai mai martaba, ya miqe tsaye ganin yadda ta shigo kawai sai ta zube a kasa tana mai rusa kuka "yarima khalipa yarima khalipa" shi ne abinda take fada, sultan daya biyo bayanta daga baya ya karaso da gudu ya tsugunna ya ma mai martaba bayani, kamar mai martaba zai basar yace karku damu zai dawo ne amma ganin yadda fulani ke kuka haiqan yasa yace to me kikeso ayi? Inace yadda ya fita da kafafunshi da kanshi zai dawo ai dare ba wai ya tsala bane sosai"
Fulani ta shiga girgiza kai a sanda take rage sautin kukanta, ka taimaka a gano inda yake mai martaba ka baza jami'an tsaro nasan wani abu ya sami yarima na nasani, sultan ma yace "mai martaba kaji rokon mu nima inajin wani abu ya sami dan uwa na"
Shikkenan cewar mai martaba kapin kace me an shiga duban yarima khalipa abin baiyiwa fulani ba dan haka sai ta saka aka hada hadda helicopter amma me duka yankin gano an rasa yarima khalipa
An dauki tsawon kwanaki uku ana nema amma babu yarima khalipa cikin yankin........


Ta saka hannayenta cikin ruwan ta debo ta watsa a fuskarta, "dan Allah MILANA ki bar wasa kiyi mu gama wankin nan".....
Ta dago fuskarta ta juya ta harareshi da manyan idanunta, a sanda ta dago fuskarta nayi tunanin ko ita ce ake ce musu 'yan matan Aljanna domin kuwa siffarta gabadaya is flawless bata da wani abu na aibantawa da zaka kalla a kushe a tare da ita,
"Kai sidi ni ba yayarka bace" yayi mata gwalo amma ai na fiki tsayi gajera kawai" bari mu karasa na kamaka kaga yadda zanyi dakai.....

Mu hadu domin jin ya zata kaya mun samu sabon team #team milana
Nagode kwarai da kulawarku
Naso nayi typing din yapi haka tsayi sosai amma na makara
Not edited

WANI YANKIOnde histórias criam vida. Descubra agora