EPISODE 06: Ganin farko; Haduwa ta biyu

58 6 0
                                    


Matar ta fahimci wani abu dama kuma tana zargin hakan a ranta,
Me da me kika koya a tsawon zamanki gun fulani?" Sahiba ta girgiza kanta
Magana zakiyi kamar yadda nake miki

"babu abinda aka koya min amma ina zuwa makaranta....
Nan matar ta fita ta barta babu jimawa ta dawo sahiba na nan inda ta barta da kwalliyarta, tace "muje" basu tsaya ko ina ba sai fadar mai martaba, wata farfajiya ce mai tsananin kyau anyi ma ko ina ado tun daga bango, zuwa su kansu ababen zama an shinfida carpet n Alfarma, gurine da mai martaba kan zauna ya huta bayan anyi zaman fada
Nan pa matar ta zube tana mai kwasar gaisuwa, a nan ne sahiba ta fahimci jakadiyar sarki ce, itama sahiba ta zube kamar yadda taga matar tayi, sarki dake kishingide da dogaranshi biyu a tsaye suka amsa gaisuwar tasu,
Sahiba ta daga idanunta a lokacin da aka basu umarnin zama, ta dubi fuskar sarki, kwarjini da yayi mata ya sa ta sauke idanunta da sauri amma hakan bai hanata fahimtar abu daya ba, wato kallo daya tak zakaima mai martaba ka tabbatar shidin bafulatani ne na usuli hakama kallo daya zaka mishi ka gane ba karamin kyakkyawan yarima akai ba lokacin kuruciyarshi... sai yau ne ta yarda a cikin gidan sarauta take tunda wai ita ce yau gata ga sarki
Suna nan zaune sai ga zuwan fulani, tun ranar da aka kai sahiba gun fulani bata ganta ba sai yau, tasha ado cikin silke mai matuqar kyau da jan hankali, ga gwala gwalai na dauka ido ta ko ina a jikinta, farar fatarta ta sake sheqi, sai yau sahiba ta ga kama irinta jini tsakanin fulani da mai martaba,, sai take gani  kyau ya kare a gun mai martaba da Fulani,
Ko kallon inda sahiba fulani batai ba, tayi gaisuwa ga mai martaba sannan ta koma bangaren haannunshi na dama ta nemi guri tayi zama na girma ta lankwashe kafa,
Mai martaba ya nunawa fulani rashin jin dadinshi gameda abinda tai kan sahiba, saboda a ka'ida zata koya mata al'amuran masarautar ne da kuma sirrin zaman gidan aure tunda itadin yarinya ce, shi ne dabarar kawota gun fulanin a matsayin fulanin na babba kuma mahaifiya ga yarima khalipa,
Daga karshe me martaba ya yanke shawarar a maida sahiba bangarenta da aka tanada mata in zata tare, wanda gurin khalipa da Sultan ne amma sai aka gyara, da daki biyu ne da living room a tsakiya sai aka dora stairs cikin living room din aka mata daki and it looks wonderful,

Karamar liyafa mai martaba ya shiryawa sahiba ya saka fulani da kanta ta kaita dakinta, ita sahiba ma ta kasa gane wacce irin rayuwa takeyi haka, komi is so complicated, komi baya mata yadda takeso, komi a duniya na farinciki is parallel to her, kodai tana da wani kashin tsiya ne a jininta,
Buh still bazata iya kashe kanta ba tunda ta karanta tasan hukuncin wanda ya dauki ranshi, itakuwa bazata iya yin two zero ba, babu duniya babu lahira,
Hadimai mata mutun shida aka barwa sahiba, biyar en mata ne daya kuma dattijuwa ce suna kiranta da mama lami, itace mai martaba da kanshi ya dauki amanar sahiba ya bata ya kuma hadata da jakadiya ta sanar mata duk abinda zata koyawa sahiban yadda kafin yariman ya dawo ta dan sassan abubuwa daidai gwargwado,

Tun sanda aka kawowa sahiba mama lami take jin dadin zama da ita, its been a while da sahiba ta buda baki da sunan dariya sosai, amma zama da mama lami ba karamin dadi yake mata ba, macece mai kirkin gaske, zuciyarta a wanke take tsakani da Allah, tana kuma yin aikinta bisa doron gaskiya,
Tun daga kan girki suka fara, girkuna iri iri wasu ma sahiba bata taba jin sunansu ba na al'ada duk mama ta sansu kuma zata koya mata, haka fannin su tuwo, kunu, da dai nau'ikan girkunan gargajiya, A hankali take koya mata su bi da bi, bangaren, kwalliya iya tafiya, magana mai dadi
Wani lokacin ita mama da kanta zata tashi tana rangwada wai yadda sahiba zataiwa yarima duk sai su kwashe da dariya
A hankali sahiba ta koyi ado da sutura mai kyau kuma taga in tayi tana yin kyau,

An tabbatarwa da mai martaba su khalipa sun kammala kusan komi saboda wasu daga cikin 'ya'yan sarakuna sun fara dawowa gida hakan yasa mai martaba yasan su khalipan ma suna dab da dawowa ne, amma kwatsam wata rana yana cikin lambunshi yana duba wasu takardu na kasuwancinsu dake gudana a wasu yankunan kasar sai kiran waya ya katse mishi abinda yakeyi, ya dubi wayar ya tabbatr kiran daga gun su khalipa ne saboda number bata kasarsu bace its international,
Ya dauki wayar yayinda wani bature yasoma gaidashi da yaren nasara shima mai martaba ya maida mashi, bayan sun gama gaisawa ne ya soma mishi bayanin dalilin kiranshi, a hankali bacin rai ya soma bayyana a fuskar mai martaba daga bayanin da mutumin ke mai, amma sai ya danne ya amsa mishi da 'its alright'
A haka wayar tasu ta kare, mai martaba ya ajiye wayar dan yasan wannan plan ne kawai na khalipa ya danyi murmushi irin nasu na manya

WANI YANKIWhere stories live. Discover now