Ya kalleta yaja dogon tsaki sannan ya fice, ta tsaya nan a daskare da dana sani tun farko ma meya jawo mata zuwa, sai kuma ta jiyo muryarshi yace "Zo muje" ta washe baki tana dan jin dadi a ranta tana jin "yau dai itama burinta zaincika a kaita makaranta kamar yadda ake kai kawayenta, babu mai mata gorin babansu baya sonta, tunda akwae motoci a gidan kuma saidai ta taka a kafa,
Ta bishi a baya tana ta washe baki, ya nupi wata baqar range rover ya shiga ya tada, itama ta zagaya ta shiga katuwar motar wacce yau ne rana ta farko data shiga wannan motar da sunan kaita makaranta.
Mai gadi ya bude musu gate a maimakon yabi dama sai taga yayi hagu
"Hamma can ne pa hanyar makarantar tamu" ta fada tana nuna hanyar da yatsanta
Ya mata banza ya figi motar a guje ta rintse idanunta saboda rough driving din da yakeyi dan idan ta bar idanunta a bude tabbas zuciyarta zata iya bugawa, sunyi mintuna 20 a haka, sannan batareda tayi tsammani ba taji ya taka wani mugun birki da saida fuskarta ta daki dashbord din motar ta dawo baya. Sai a sannan ta bude idanunta tana mai sauke ajiyar zuciya akai akai, ta bude idanunta tana kallon inda suke tanason ganin school amma sai taga dogayen bishiyu bangaren hagu da dama na titin, babu alamun gida balle makaranta, sai motoci da kan wuce lokaci lokaci kuma da gudu (highway), ji tayi an bude kofar bangaren datake, a tsorace take kallon Hamma daya zagayo gurinta, tana kokarin magana ya sa hannu ya cafko damtsen hannunta at once kuma ya cillo ta waje, dayake motar mai tudu ce yasa taji jiki data fadi kasan kan duwatsun, har gefen hannunta na hagu ya kurje, guiwar hannuntaa na dama kuma ta fara jini alamun taji ciwo, ta daga idanunta da suka yi ja suka cika da kwalla a hankali labbanta suka furta "hamma"
A tsawace yace "dont ever call me that, ni ba d'an uwanki bane ko kinga muna kama....
Ta dubeshi tsaf itama ta fara kokonton anya dan uwanta ne, tunda basu kama din
"now im warning you ko hanya nabi naga kinbi kin shiga uku wlh balle har ki shigo part dina this is ur punishment"
A fusace ya zagaya ya figi motar a guje ya bar wajeen, sauran hawayen da suka maqale a idanunta suka gangaro tana bin motar da kallo har ta kule
Zugi taji a ankle din kafarta, ta rike wajen tana mai kokarin mikewa tsaye, dakyar ta miqe sai taji gabadaya duniyar tayi mata zapi, sai a yanxu ta sake fahimci bata da gata, ta dada tabbatar da bata da wani wanda yake sonta, taji hawaye masu zapi sun biyo kumatunta, batada courage din share su dan haka ta barsu sukai ta kwaranya
"All she need is some sibling love, bata bukatar wani abu mai yawa"
Ta nuna wa kawayenta itama tana da gata, ta fadamusu yau hamma ne ya kawota a motarshi, ashe duk wannan mafarki ne.
Tayi tsaye tana kallon gabas da yamma kudu da arewa ita sam bata san inda zata dosa bama yanxu, batasan me zatai ba, motocin dake wucewa kuwa da bala'in gudu suke zuwa su wuce saboda high way ne, ashe rashin imanin hamma ya kai ya ajiyeni a nan? Wato nama mutu kenan!
Ta soma jan kafarta tana yin hanyar dataga hamma ya juya kan motarshi tare da kyautata zaton nan ne hanya, batai nisa ba sam taji bata iya cigaba da taka kafarta ba ta zube kan guiwarta cikin kunar zuci
Iska mai karpi ta soma kadawa, ta daga kanta ka kalli sararin samaniya da yayi duhu hadari ya hadu, ta ji gabanta ya buga dan tabbas idan ruwan sama ya duketa akwae matsala...A hankali yayyafi ya soma sauka taja hijab dinta gaba tana rufe fuskarta saboda lalurar ciwon ido datake fama dashi duk sanda ruwan sama ya daketa, a hankali a hankali ruwan ya soma karfi, taji tsaiwar mota kusa da ita, ta daga ido da hanzari ta kalli motar cike da jin dadi a ranta tace "nasan hamma baze barni a nan ba" bata bude fuskarta ba and without a second thought ta bude motar da sauri ta shiga tana ajiyar zuciya hawaye jin dadi suka zubo daga idanunta suna jika hijab dinta daya rufe fuskarta,
"En mata me kikeyi a guri irin wannan" a tsorace ta daga idanunta ta cikin hijab din taga fuskarshi"
Ta sauke idanunta tana rabbasu cike da jin tsoro zuciyarta na bugawa akai akai , ita duk tunaninta hamma ne ya dawo daukanta tunda kalar motar daya ne, be samu damar ganin fuskarta ba amma yana hangen lips dinta masu kyau, sahiba ta kuma jan hijab dinta sosai ta rufe fuskar, taji ya soma tapiya itakuma bata iya ce mishi komi ba har ya kaita kofar gida, taga maigadi yazo ya budemishi har suka gaisa
Cikin sassanyar murya a lokacin daya tsaida motar tace "nagode" a ranta tanaso tasan waye
Yace "be very careful with Anas, karki sake shiga motarshi ki kula daa kanki"
This is the first time da wani dan adam ya damu da ita har ya fadamata ta kula da kanta,
Ta fita daga motar tashi tayi cikin gida sai dataje bakin kofar main house sannan a hankali ta juyo ta dube shi har lokacin bata bude fuskarta ba sai ya sakar mata murmushi amma sam taji murmushin nashi be mata dadi ba taji murmushin nata kamar barkono akan ciwo, ta juya tayi ciki har tana tuntube a kofar falourn nan ta tadda baki da dan dama,
A nashi bangaren kuma baima san ya mata murmushi ba hakan nan ya tsinci kanshi yana mata murmushin which shi murmushi be cikin dabi'unshi na yau da kullum she's the second person bayan Khaleepa data sa shi murmushi dukda dai ita nata murmushin bawai yayi ne don farincikin shi ba sai dan ya kwantar mata da hankali da fatan murmushin shi zai sama mata jin dadi amma sai aka samu akasin haka...
ta janye hijab din fuskarta tana kakalo murmushi ta tsugunna a sanda taji ciwon dake kafarta yana kara zapi
Daya daga cikin kannen Abbanta tace "ahhh wannan sahiba ce an girma" momy tace eh ita ce " ya makaranta" cewar qanwar Abban sai yayar Abbah tace "ni sahiba wannan bakin naki na rasa a wanne dangi kika samoshi, anya kedin tamu ce kuwa, anya Aminu ba diyar wani yake kiwo ba" sai sukai dariya tare da shiga wata hirar
A hankali sahiba ta miqe taja jiki tai sama kalaman hajiya umma suna sukar rarrauniyar zuciyarta
Ta zauna tsakiyar gadon tana mai rera kuka cikin kadaici da zafin zuciya.. Nan take wata idea ta fado mata (Niqab)

YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...