Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, karin magana ta hausawa, gashi ranar tarewar sahiba tazo duk abinda akeyiwa kowacce amarya anyiwa sahiba, kamar 'yar gata, iyayen nata sun nuna bajinta kamar auren fari
Kamar yadda tsarin yake angwaye sun aiko da motoci domin daukan yan kai amarya da amarya gidanta....Wani direban dake tuka khalipa da sultan tun suna yara basu da wasu qanne lokacin... Shi sultan ya bawa mukullin motar da amarya zata shiga yace ka tabbatar kaine ka dauketa dan Allah
Dattijon direban da suke cewa magaji yace angama ranka ya dade.... Hatta ita kanta motar da za'a dakko mishi amaryarshi saida yayi mata survey na kwanaki biyu shida mechanic dinshi da wani security agent,, ya tabbatar komai lafiya... akan idon sultan yana kallo motocin sukai convoy dayawansu ana ta busar Algaita ana sha'aninnikan fada suka fita, ya zauna yanajin zuciyarshi babu dadi shikam inama yaje da kanshi ya dakko amaryar tashi, amma babu hali tunda haka al'adar gidan take, saidai koma mene he's ready he's more than ready to protect his bride... To be her shield....Fulani wadda ita ce tamkar uwa gun sultan itama tayi nata shirin na tarbar amaryar yarima sultan, shirin hawan angonci da yake a tsarin al'adar fadar shi sukayi, mai martaba da sultan ne suka karpapa guiwar ayi din tunda abu ne na Al'ada
Fulani bacin rai ne tare a ranta, ji take kamar mai martaba yama manta da mutuwar dansu ne, badan badan bama da tace anya shi ne uban khalipa, saidai tasan shidinne amma yadda yake nuna halin ko in kula kan mataccen dan nasu abin na sosa mata raiFulani na dakin ta domin shirya kanta, duk ta kori hadiman da zasuyi mata kwalliya, ta dakko wayarta dake kara a sanda tayi murmushin kasaita tun kapin tace wani Abu ciroma yace "mun sameta fulani" fulani ta miqe tsaye a kasaice tace "madallah ciroma" cikin ranta yayi fari tass kamar madara
Yarima sultan yayi shirinshi domin an tabbatar mishi wasu daga cikin masu kawo amaryar sun soma zuwa, yasha ado cikin kaya irin na sarauta launin baki da silver, hakama dokinshi yasha ado launin baki da silver tun daga sama har kasa sheki kawai yakeyi, ya kagu amaryar tashi ta karaso, ya zaro wayarshi yana danna number ta amma sai yaji wayar ta switched off....
Few minutes back
Gud'a ke tashi da kamshi a ko ina cikin gidan tun zuwan masu daukan amarya, sahiba ta yarda tana da gata rigar confidence ta sake lullube ta, yadda taga irin hidimar da ake sha duk saboda ita, haqiqa salma ta cire mata mask, amma yarima sultan shine confidence dinta, shi ya lulluba mata wannan rigar mutunci da ake ta ji da ita ana kambamata, tasan shi ya kankaro mata wannan mutuncin... Tasha kwalliya ta shirya cikin lace white sai kuma Alkyabba da aka dora mata white and golden, sarka dan kunne, awarwaro agogo zobuna duka golden ta saka masu kyau da tsada,
Saida yan daukan amarya sukai kyauta ta bajinta kapin aka fito da amarya wadda fuskarta ke lullube, anty ce rike da ita... Uwargidan galadima wadda itace kaka gurin sultan ta gurin uwa itace tazo daukan amarya da kanta... Saidai abin yaso ya zama rigima domin
Kamar yadda galadima ya aiko hajiya daukan amarya haka itama fulani ta aiko da danginshi baban sultan daukan amarya, amma hajiya dake macece mara son rigima sai tace kawai mutanen fulani suje da amaryar...
A motar da tasha survey din sultan aka saka sahiba, driver a gaba,,, a baya kuma Anty da wata dattijuwa suka saka amarya a tsakiya... Gaban sahiba sai faduwa yake domin itakam ko irin kukan da amare keyi kasawa tayi saboda wata fargaba da faduwar gaba dake samunta akai akaiTafiya suke tayi kamar bazasu daina ba, sahiba taga tsayin tafiyar tasu kwarai, a sanda suka tsaya a wani junction suna shirin tafiya dattijuwar ta wullo waya har ta daki kafar sahiba ta wuce gurin Anty
Tace "bismillahi dan Allah miqomin wayar nan" anty ta tsugunna domin dakko wayar a yayinda motar tayi wani fizga da saida sahiba tayi gaba ta dawo baya hakama Anty data sunkuya ta bubbuge kanta, cikin dakikai da basu da yawa aka toshe wa sahiba hanci, taji wani kamshi mara dadi na yan dakikai bata ko iya kokawa dame toshe mata hancinba ta fita hayyacinta, dagowar anty keda wuya itama nata handkyn ya sameta, saidai itakam sun dan sha kokawa har saida dattijuwar ta buge mata kanta tukunna ta shaqa chloroform hakanne yasa tapi shaqa dayawa and in no time itama ta fadi.... Kan kace me magaji ya shiga filfila gudu

YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...