Episode 27: #Obsession... Karma

28 3 0
                                    

*WANI YANKI* 🍂🍂

#family #royalty
#love #politics #familybusiness
#obsession
#mystery #conspiracy

Na Aysha b. Naseer
.
.
.
Wattpad @ AyshabNasir

#notedited

Cikin dan rikicewa khalipa yace "my milana turanci naji kinyi ko kuma kunne na ne" ta danyi gajeran murmushi ta kuma lumshe idanunta "kwarai i spoke English, mind you i'm not ur milana"... Khalipa ya dan miqe yace "to kodai mafarki nakeyi ne..." Babu mafarki yarima gaske ne babu ko tantama... Ta juya ta shige bukkar ta barshi nan kasa cikin rikicewa..
Ya bude idanunshi a hankali, ya ganshi kwance kan shimfidarshi, yana tuno abinda ya gani cikin mafarkinshi, milana ce take turanci cikin accent mai bala'in dadi, ya zauna ya rike kanshi feeling kamar abin ba'a mafarki ya faru ba, wani strong feeling nace mishi gaske ne amma dole yayi denying tunda dukkan Alamu sun nuna a mafarki ne, kuma yapiso shima ya yarda a mafarkin ne, but what if ba mafarkin bane, khalipa yayi murmushi bayan jin tmbayar dayayiwa kanshi....
Garin ya danyi haske sidi ya taimakawa khalipa ya tashi yayi Alwala yayi sallah daya idar da sallah sidi ya kawo mishi farfesun kifi mai zapi yace "ka samu kaci saboda kaji kwarin jikinka" khalipa ya kalli farfesun ya hadiyi yawu, ya dubi sidi yace "waye ya dafa" sidi yayi dariya
To dama waye keyin girkin ai dole milana ce ni nawa tayi ne da dan abinda ba'a rasa ba" khalipa ya wangale baki yana wide smile sai lokacin ya ji yana jin yunwa ya sa hannu sai da ya shanye farfesun tass dukkuwa da yajin kayan kamshi daake ciki, ya kuma cinye tsokar kifin ya taune kayar kifin da tayi laushi sosai...
Milana tayi shirinta tace "sidi kayi azama dan Allah lokaci na kurewa in muka makara zamu tadda mutane".... Khalipa yaa dubi sidi da sauri, kaya yake tattarawa da alama fita zasuyi yace cikin low voice "sidi ina zakuje?" Sidi batareda ya juyo ba yace "kamun kifi, yanxu lokacin su ne sosai"
Khalipa ya miqe da sauri dukda jikin nashi babu dadi yace "zan biku nima" sidi ya girgiza kai "ai baze yu ba"
Yasa kai ya fita, khalipa ya biyoshi da sauri... Milana ta bata rai ganin yadda yake kallonta yana murmushi ta dubi sidi "shikuma pa?"
"Wai dole sai ya bimu" sidi ya fadi cikin halin ko in kula, milana taji wani haushi ya turnike ta kapin tayi magana sukaji muryar mama dake can gefe zaune tana cewa "sidi waye ze biku ne?"
Dukka su ukun sai da gabansu ya fadi, sidi ya fara in in na cikin rashin gaskiya "dama eh imm mama dan gidan malan yunusa ne wannan abokin nawa"
Mama tace "to ku tapi dashi mana" milana tace eh mama dashi zamuje dama ganin da nai ya baro cikin gari yazo har nan yasa na tambaya....
"Idan kun fita ku biya gidan su shamsiyya naga har yanxu bata shigo ba zaman haka ni daya ba dadi,,, milana ta amsa ta da to mama... Sannan ta kalli khalipa ta galla mishi harara tayi mishi alamar ya juya ya koma daki

Idan ya kalli idanunta tabbas baya ganin digon sonshi a ciki, hakan ne yasa yakeji baze barta ba, he will not give up on her, saboda yana sonta, kuma zaiyi duk abinda zai sa ta soshi zaibi abinda zuciyarshi ke so ne, koda duka duniya zasuce milana tana da aibu koda kullun zata dinga yankar naman jikinshi koda zata dinga azabatar dashi baze barta ba baze iya barinta ba, he's so obsessed with her so obsessed with every single thing about her, her voice, her looks, her perfect shape, her shiny sparkling skin colour, ohh ya Allah help me..
Khalipa ya furta sanda yaji kanshi na neman fashewa saboda qualities na milana dayake tunowa wanda bai taba gani ko jin labarinsu ba a tunaninshi wasu ma basu bayyana gareshi ba he's so sure

Ya nemi fararen sutura kamar yadda yaga yawancin suturar mutanen garin daga fari sai baki, ya saka ya nemi takalmi cikin takalman sidi irin na kaba ya daure a kafarshi kamar yadda yaga sidi yayi, ya nemi wata rigar ya nada a kanshi sannan ya rufe fuskarshi da sauran jikin rigar idanunshi kadai ya bari a bude ya fito yana tafiya kamar bayason taka kasa, Allah ya taimakeshi har ya wuce mama bataji shi.... Yana dan barin bukkar ya hangi shamsiyya na tahowa tana ta wasa tasha damara a kugu, ya dubi gabas da yamma babu dan gurin buya sai yayi hanyar cikin duwatsu da dukkan gudunshi,
Kasar gurin a bushe take amma ba duka ba hakan yasa ya dan tada kura amma bamai yawa ba, har shamsiyya ta kai hankalinta gurin kurar tana tunanin ko iska akeyi a garin amma bataji iska ba, bata damu ba ta cigaba da tafiyartaa,
Bayan ta wuce ne khalipa ya sauke numfashi, hankalinshi ya kwanta ya fara tunanin ina su milana sukai to
Bin cikin duwatsun ya dinga yi, yana boye kanshi,, ya danyi tafiya mai nisa dayaji ya gaji sai ya tuna da sultan a ranshi ya ayyana "sultan i will be back soon with my wife" yaji kalmar tayi tsananin mishi dadi har saida ya kyalkyala dariya, gurin masu kamun kifin ya hango, da mutane ba laifi ana ta kamowa, masu kama kifin suna amfani da abubuwan kama kifi daban daban, wasunsu da basket ne wasu hook wasu trap wadanda sukapi bawa khalipa mamaki sune masu kamowa da hannu..... sidi ya fara hanga cikin jama'ar sannan yaga milana daga gefen sidin, yayi dariyar ganinta, babu abinda takeyi tana zaune tana kallon su sidi sunata aiki, sai yaji inama yaje ya rungumeta burinshi kenan a yanxu yaji dumin jikin milana amma anya hakan is possible? Domin duk wata dama taqi badawa.... Har saida su sidi suka kammala milana ta tayashi da rike wasu kayan suka kama hanya wasu jama'ar sukai cikin gari su milana kuma sukayo inda nasu bukkar suke, sai sanann khalipa shima ya miqe yana binsu ta cikin duwatsun a tare a tare yanayi yana kallan milana, indai yana kallonta to baya gajiya sam ko mene zaiyi,
Sai da suka karaso tare ya fito yana musu murmushi, milana tana ganinshi ta ganeshi dukda fuskarshi a rufe take, yasa hannu ya cire abinda ya rufe fuskar tashi murmushinshi ya bayyana, milana tayi kamar batamasan dashi ba ta juya abinta ta wuce sidi kuma ya dan maida mishi martanin murmushin shima ya wuce domin suna da ayyuka,

Duk inda milana tai sai khalipa ya bita, idan ta dakko aiki zata fara sai ya karba, itakuma sai ta sakar mishi kuma sai ya kasa sai ya nemi taimkon sidi, ta dakko ita ce zata hada wuta ya karaso da sauri yace barshi ai na iya, milana ta guada kai ta miqe ta barshi a nan, sidi ya sa tafin hannunshi ya rufe fuskarshi cikin jin takaici dan yasan khalipa baze taba iya wa ba daga karshe kuma shi yake bari da aikin... Ile kuwa haka akayi, yayi iya yinshi ya kunna itacen nan amma sam har gumi yake yarfewa, lokaci zuwa lokaci kuma sai ya juya ya kalli inda milana take sai yaga kamar bata ma san da existence dinshi ba domin kuwa aikinta kawai takeyi.. Yapi awa guda yana abu daya daga karshe ya nemi taimakon sidi duk ya jigata sai kace wanda ya shiga filin daga...

Milana tana tsugunne tana harhada aikin kifin data gama, khalipa ya tsugunna kusa da ita yace "milana" ta shareshi kamar bataji shi ba, ya kuma maimaitawa ta sake shareshi, ya dan yi shiru ya dade baiji muryarta ba, kuma yana tsananin son jin muryarta, milana ta miqe hannunta rike  da kwandon kaba da ke cike da kifaye gyararru, yayi saurin tashi ya dan riko hannunta yana kokarin magana, saidai lafiyayyan marin daya sauka kan kuncinshi ne yasa shi kasa furta komi ta wuce yana kallonta yanajin azabar marin data mishi, amma zapin da zuciyarshi ke mishi na rashin jin muryarta har yapi zapin marin

Bukka milana ta shige da dan sauri, batason yadda take mishi, she's too harsh on him, amma bata da wani zabi, dole yayi haquri da soyayyarta wannan ita ce mafita a gareshi, in kuwa ba haka ba to zaiyi nadama, soyayyarshi a gareta bata da wani amfani, gashi kuma ya zurfafa....

Khalipa ya koma ta chan bayan bukkokin yana kallon yadda rana tayi jaa tana kokarin faduwa, ji yake kamar shima tashi zuciyar haka tayi jaa saboda ciwon datake mishi, yana son milana and that will never change koda zata gididdiba shi ne, amma kuma yana jin zapi yanajin zapin yadda take nuna tsana karara a gareshi, ai koda bata sonshi da sai ta kyautata mishi, yadda zai samu sassauci
Sai yaji wani kara mara dadi a cikin kwakwalwarshi, yayi azamar toshe kunnenshi ya tsugunna duk dan ya dena jin karan dake barazanar fasamishi kwakwalwa
Muryar sultan ce mai dadi ta ratso kunneshi ta hana karan cutar da kwakwalwarshi tana fadin

"Ita kyautatawa anayinta ne koda babu soyayya dan zaman tare kuma karka mnta akwae haqqinta dake wuyanka naci sha, sutura, muhalli dss dan haka a matsayi na na dan uwanka kuma abokinka kuma mai qaunarka, inaso ka sauke haqqinta dake kanka kadda hakkin yarinyar nan ya farauceka, karka manta marainiya ce uwarta bata duniya"....

Khalipa yaji hawaye haka nan sun zubo mishi wacece sultan yake mishi magana akai?, wace ce ita? Dagaske haqqin nata ke bibiyata kamar yadda naji muryar sultan na fada?


Sultan ya tapi hanya yana tunanin sahiba, "all he sees in her eyes is fears, bawai batason shi bane, tana buqatar assurance ne assurance na cewar abinda ya faru da ita a baya baze sake faruwa da ita ba, he can read it in her eyes that she's afraid of surutun mutane kuma tana matuqar jin tsoron komawa palace, palace is her worst nightmare, bazataso komawa ba that is why she reject me, shiyasa taqi amincewa dani, especially abu ne da bazata taba kawowa a cikin ranta ba, me confessing my love to her....
Sahiba needs assurance and nikuma im ready to fight the world for the love i have for her, im never giving up on my one and only first love, with Allah we shall handle all the obstacles and pass perfectly okay... Bai bukatar kowa yanxu, tunda yaga yadda momy ma tayi reacting gara yayi abinshi da kanshi ya kwatar wa kanshi 'yanci,

Gurin mai martaba straight sultan ya wuce, ya taddashi yana ta Amsa calls saboda wasu da ya tutturawa IV sunata mishi Allah ya sanya Alkhairi, sultan ya goge gumin fuskarshi domin yanajinshi ne kamar cikin ruwan dake tafasa, amma indai kan sahiba ne he's ready
Mai martaba ya ajiye wayar gefenshi sai sultan yaji confidence dinshi ya gudu, tayaya zaizo gaban mahaifi yace bayason diyarshi wata yakeso? Mahaifi irin mai martaba, wanda ya dauki nauyin shi ya kula dashi ya kaunace shi yake kuma kan kaunar tashi, taya zai buda baki yace a fasa aurenshi da Amira a maida kan sahiba bayan dubban manyan mutanen da mai martaba ya gayyata, wannan ai ya kunya tashi ne, bayan kuma kapin ya shirya bikin saboda Adalci saida ya bashi chance ya fidda wadda yakeso... He's sure idan ya fadamishi abinda ya niyyata wannan wide smile dake kan fuskar mai martaba sai tayi vanishing dole duk adalcinshi sai ya dandani dacin kalaman da sultan yake niyyar fada... sam Mai martaba bai cancanci hakan daga gareshi ba, amma ya zaiyi da tashi zuciyar....

"Kayi shiru kuma" mai martaba ya katse tunanin sultan,
Sultan ya ji zuciyarshi na mishi rashin dadi yace cikin wayancewa "dama nazo gaisheka ne ranka ya dade Allah ya kara lafiya da tsawon rai mai Albarka" mai martaba yayi irin nasu murmushin sannan yace masha Allah

Bai iya fadan komai a gaban mai martaba ba haka ya fito jikin shi a sanyaye, mai martaba yana ganin mutuncin sultan, yana sonshi a cikin 'ya'yanshi, so na hakika wanda babu Algus ko son zuciya, yasani indai ya furta bayason Amira to mai martaba zai iya haqura saboda farincikinshi yakeso ba komai ba....  Kiran mai girma kaka galadima ya iske sultan....

WANI YANKIOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz