💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.*NASIHA*
_Sallah tana maganin duk cututtukan da suke samun zuciya. Ita ce haske mai kawar da duhu da zunubai. Abu Huraira ya ce, "Na ji Manzon Allah yana cewa:_
_"Ku duba nan; idan ɗaya daga cikin ku yana da rafi a bakin ƙofar sa kuma yana wanka cikin sa sau biyar kullum, shin wata ƙazanta tasa za ta yi saura?" Sai suka ce, "Ba wata ƙazantar sa da za tayi saura". Sai ya ce, "Wannan kamar salloli biyar ɗin nan ne waɗanda da su ne Allah yake wanke zunuban mu"._
_A sallah ne ake ganin tahƙiƙanin daidaituwa da adalci. Lokacin da Ladan ya yi kira da cewa: "ku yi gaggawa zuwa Sallah, ku yi gaggawa zuwa ga falala. Duk waɗanda sallar ta rataya a kansu, masu arziƙi da faƙirai, manya da yara, sarakuna da talakawa - dukan su za su taru a sahu guda ba wani bambanci tsakanin su, dukan su bayin Allah ne. Za su taru a bisa aƙida guda a ɗakin Allah, suna tuna Allah kaɗai, suna tawali'u gare shi._.
*EPISODE Twenty Two*
Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.
Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan "su tafi gida," sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but jefi-jefi suna kewayo wa ko Kaka ya farka.
Har dare be farka ba, haka ilayan Doctor Al'ameen suka kwana a cikin wani hali a wannan ranan, sai washe gari aka samu ya farka, sai dai sosai suka shiga farin ciki a ranan, sabida Kaka ya samu sauƙi tamkar ba shi ba, babu wanda yayi tunanin zai tashi da lafiya haka, sai ga shi har magana yana iya yi, kuma yana iya yin sallan sa, domin tunda ya tashi ya buƙaci a kai sa yayi alwala, sai da ya gabatar da sallolin da ake bin sa, sannan ya samu yaci abinci daƙyar, aka ba shi magani ya sake komawa barci, sakamakon alluran da aka sake mishi, sabida ana son ya sake samun hutu sosai.
A ranan haka mutane sukai ta zuwa duba sa, gaskiya Kaka na mutane ne, ba ga talakawan ba; ba ga attajiran ba, manyan mutane kama daga ko wani gari duk ana ta zuwa gaishe shi, har mutanen Maiduguri dangin su duk sun zo wasu daga ciki duba sa, su Hajiya Ikram, Hajiya Laila tun a ranan suka shigo Kaduna.
Kwanan sa biyar a asibitin yana samun kulawa daga ƴaƴan sa da jikokin sa, ya samu sauƙi sosai, sai dai sun hana a mayar dashi gida dole sai ya ƙara samun sauƙi
Shi da kansa ya matsa musu dole suka sallame sa ya koma gida, a ranan sun ga mutanen anguwa, suna ta ɓulɓulowa gaishe da Kaka, da waɗanda suka je asibiti, da waɗanda ma basu je ba duk sun biyo sa gida.
![](https://img.wattpad.com/cover/262673222-288-k158926.jpg)
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasyFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...