💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Sixty Two*
*AFTER TWO WEEKS*
Yana cikin ɗaura agogon sa daga hannun sa na hagu, sai yaji wayan sa ta soma ƙara, sai da ya ɗan leƙa ya tabbatar da wanda yake tsimaye ne kafin ya ɗauka yana karawa a kunne
Daga can mutumin yace, "ranka ya daɗe! gani tare da su na gama aikin".
"Ok turo min address ɗin". Daga haka ya kashe wayan yana ajiye wa
Ci gaba yayi da ɗaura wrest watch ɗin, bayan ya gama sai ya miƙe daga bakin gadon shi da yake zaune, takalman sa ya zira cover shoes baƙi sannan ya ɗauki wayan sa ya zira a aljihun gaban rigan shi ya fito ya rufe gidan ya fice, kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, yana shiga da sallama ciki-ciki
Hajiya ta amsa mishi da ke zaune a kan dainning tana yin kari
Wajen ta ya nufa ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun, sannan ya gaishe ta a miskilancen da ya saba
Amsa mishi tayi tana bin shi da kallo, sai kuma dai tace, "ina zaka je da safen nan?"
Hannu ya saka yana haɗa tea yana bata amsa, "zan je wani wuri ne".
Bata sake mishi magana ba haka suka zauna Kamar kurame
Sai kuma can yace, "Dady ya tafi ne?"
"Eh ya fita tun ƙarfe 06:30am. Amma kai ya batun maganar ku da Ɗahira? Ka san cewa ya zura maka ido ne yaga iya gudun ruwan ka da ya neme ka kaƙi kazo, ya kamata tun wuri ka kawo mishi takardan yarinyan nan kafin haɗuwar ku, idan kuma ka ce baza ka sake ta ba kamar yanda kace ɗin ne, to, tun wuri ka neme shi ka ba shi haƙuri, don na san shi ne yafi ɗaukan zafi, idan kuma ba son zama da ita kake yi ba gwara ka sake ta ka dena cutan ƴar mutane da auren ka a kanta".
Shiru yayi be ce komi ba, illa shan tea ɗin shi da yake yi, amma kuma abaɗini juya kalaman Hajiyan yake yi
Ganin be kula ta ba itama sai ta tashi ta wucewar ta ta bar shi nan
Be ƙara mintuna biyu cikakku ba shima ya tashi ya fice, kai tsaye gidan su ya koma ya ɗauki mota ya fice, a lokacin ne ya duba wayan sa yaga address ɗin hotel ɗin da aka turo mishi, sai ya wuce can.
Har ciki ya shiga da motan shi yayi parking, kafin ya fito sai da ya saka baƙin glasses a fuskar sa sannan ya fita ya nufi room ɗin da aka turo mishi, yana zuwa dai-dai ɗakin yayi Nocking
Sai ga wani saurayi ya buɗe mishi ƙofan
Ya shiga yana bin ko ina da kallo ta cikin glasses ɗin sa yana yatsina
"Suna cikin wancan ɗakin". Cewar saurayin kanshi a ƙasa
"Ka tabbatar su ne?" Yayi maganar yana kallon sa fuska a ɗaure

YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasíaFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...