💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Forty Eight*
Kai tsaye Police station suka wuce gaba ɗaya, inda a can ne Hajja Fatu tayi bayani dalla-dalla, ta yanda ƙwayar suka kasance a asibitin, ta taimaka wa Dr. Zubairu ne wajen shigo da su tare da magungunan asibitin
Nan Abba yayi kamar zai make ta sabida faɗa, sosai ya zuciya ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba
Sai da Big Dady da Abbu suka yi ta tausan sa kafin ya haƙura
Nan aka tura ƴan sanda domin su je su kamo Dr. Zubairu, amma sai dai ba'a same sa ba tuni ya gudu, illa ƙwayoyin da aka kwaso a Office ɗin sa.
ASP yace musu, "za'a kama Hajja Fatu a matsayin wacce ta taimaka domin yin safaran ƙwayoyi, wanda yayi sanadin kisan kai, ita kuma Safna an sake ta domin bata da laifi". Sai dai sosai suka ja mata kunne a kan sakacin ta ne duk da haka ya ja wannan abun, tana a matsayin likita amma ba ta lura da abinda zata iya ba Patients ɗin ta
Shi Abba tunda ya ga abun ya zo da sauƙi tunda an sasanta baza a kulle asibitin ba, ya wucewar sa ya tafi, be damu a saki Hajja ko kar a sake ta ba
Inda su Big Dady su suka tsaya kai da fata suka yi ta cukui-cukui har suka shawo kan matsalan, to, abin ka da akwai kuɗi, komi a ƙasar mu idan kana da kuɗi to zaka iya yi, nan suka samu aka ce za'a saki Hajja tunda ba ita ce asalin wacce ta shigo da ƙwayoyin ba, kawai da taimakon ta ne hakan ya faru.
Kafin ma a sallame su har an kamo Dr. Zubairu, sosai yaji kunya sanda suka haɗu da su Abbu, musamman ma Big Dady tunda shi ne abokin sa ƙwarai, haka yake ta sissinne kai kamar muna-fuki
Su kuwa basu bi ta kansa ba suka ficewar su. Kai tsaye gida suka wuce, sai da suka koma ne suka sanar da Kaka duk abinda ya faru
Gaskiya be ji daɗi ba, domin ya nuna ɓacin ran sa matuƙa a kan Hajja, wanda su kansu sun sha mamaki, duba da yanda Kaka yake son Hajja Fatu sosai, kasancewar ta ɗiyar abokin sa kuma ɗiyar ƙanwar sa, amma kuma sun san yanda yake matuƙar ƙaunar asibitin sa ba ya son ko kaɗan wani abu ya faru, yanzu idan duniya suka ji shikenan za'a fara ma asibitin baƙin fenti. Sosai yayi mata faɗa daga baya ya haɗa su yayi musu nasiha sosai ganin Abba yana ta kumbura da shirin ya aikata wani abun
Abba dai be bar wajen ba sai da ya kafa mata sharaɗi, domin yace "dole sai ta bar aiki," amma Kaka ya hana sa, shi kuma yace, "to idan haka ya sake faruwa wlh dole ba ita ba aiki a ko wani asibiti ba Asibitin su kaɗai ba, idan kuma tace a'a sai dai ba a ƙarƙashin sa take ba, tunda da sa hannun ta ake son ganin bayan asibitin su, da goyan bayan ta ake shigowa da ƙwayoyi tare da maganin asibiti, nan gaba ma da ita za'a haɗa baki da maƙiyan su don ganin bayan asibitin".
Abba fa ya shaƙa sosai, ba don Kaka ba babu me tanƙwara shi, sai dai su rabu da Hajja Fatu. Tunda shi Abba duk a cikin su ya fi su zafi, yana da sauƙin kai matuƙa, amma idan ya tashi faɗa ba ya ji ba ya gani, duk wani rashin son raini irin na mahaifiyar su shi ya biyo ta, ba ya shiga harkan mutum, to, kaima kar ka shiga nasa, yanzu zaka ga haukan sa matuƙa, shi kuwa Abbu sak Kaka ne babu ruwan sa, yana da sauƙin kai, haka ma Big Dady, shi kam ya fi su haƙuri, duk da shi ne babba yana da haƙuri matuƙa, idan ka ga yana faɗa kawai yana yi ne domin gyaran ƴaƴan sa, amma duk abinda zai faɗa zai yi wuya ya aikata shi a zahiri, idan ma kayi masa abu kafin zuwa anjima ya manta ransa yayi sanyi, sai dai idan zai ɗaure maka fuska domin ka koki gaba, shima sak halin Ummin sa ya biyo babu ruwan sa.
![](https://img.wattpad.com/cover/262673222-288-k158926.jpg)
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasiaFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...