💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Sixty Five*
Usman dai tunda ya fita gidan shi ya wuce kai tsaye, gaba ɗaya duniyar tayi mishi zafi ransa duk ya gama ɓaci, shi a ganin shi don yace "bazai sake ta ba ne". Suke mishi haka, to su riƙe ta kar su barta ta dawo, shi kuma wlh bazai sake ta ba har sai sun gaji sun kawo ta da ƙafafuwan su, barin ma ƙasar zai yi tunda don suna ganin shi ne shiyasa suke mishi haka, tunda ya basu haƙuri ya ce zai zauna da ita meye kuma laifin shi a nan? Ko albarkacin cikin shi ai be kamata su raba auren ba. Wani zuciyar tashi tace, "amma ai kaima baka kyauta ba, ko kai ne a madadin ta zaka guje wannan auren, tabbas ka bata wahalan da in dai tana da hankali dole ta guje ka gaba ɗaya".
"Amma to ai na bata haƙuri, kuma na gane kuskure na bazan sake ba". Yayi maganar a fili yana hawaye. Sai ya mirgina kwanciyar sa yaci gaba da tunanin zucin shi dake ƙara mishi ƙunci da raɗaɗi, duk tunanin Ɗahira ya addabe shi ya rasa ya zai yi
Yau dai rana ɗaya ya tashi domin neman agaji a wurin Allah, abin da be taɓa yi ba, domin idan har ka ga Usman ya tashi da dare yana Sallah to tabbas yana cikin ƙunci ne sosai, yau dai ga shi haka ya tashi yayi ta jero salloli yana neman biyan buƙata wajen Allah, da kuma neman ya yaye mishi duk damuwar shi, Allah ya gani yanzu yana ƙaunar Ɗahira, yana jin son ta kamar ya kashe shi yanzu, be san ya aka yi ya faɗa wannan mugun son nata ba, shiyasa gaba ɗaya sallan duk a kanta yayi
Be dena ba sai da kusan uku tayi, sai ya jira har aka yi sallan asuba yayi a wurin don bazai iya zuwa Masallaci ba, yanzu ɗin barci yake ji sosai, shiyasa yana gama wa ya kwanta.
Be tashi ba sai wajen goma na safe, wanka yayi ya shiga kichen daga shi sai gajeren wando ya haɗa tea ya zauna a Parlour Yana sha, duk gaba ɗaya tunanin sa ya tafi ga hukuncin da zai yanke
Bayan ya gama ya tashi ya mayar da kofin kichen, ya wanke kafin ya koma ɗaki, kayan shi ya soma haɗa wa a Trolly har ya gama, sannan ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga me wuyan V da gajeren hannu, sai wando jeans blue colour crazy, gaban mirror yaje ya gyara gashin kansa kafin ya feshe ko ina na jikin sa da turare, ya ɗauki agogo ya ɗaura a hannun sa sannan ya zira takalman sa sandal da ya zaro su daga ƙasan gadon shi, ya ɗan share kasancewar da akwai ƙura yaja Trolly ɗin sa ya fito, sai da ya kashe komi kafin ya fice, kai tsaye wajen motan shi ya nufa yana shirin saka wa a Boot
Hajiya da ta fito ta ƙaramin ƙofan gidan su ta hange shi, kwaɗa mishi kira tayi tana nufo shi
Sai ya juyo yana kallon ta fuska babu fara'a, gajeren tsaki yaja yana ƙarisa tusa Trollyn cikin Boot ɗin sannan ya rufe, ya nufe ta ba tare da ya amsa kiran nata ba
"Ina zaka je haka da kaya? Ba dai tafiya zaka yi ba a kan maganar nan?"
Sai da ya ƙumshe baki ya saki iska kaɗan tare da sake haɗe fuska yace, "tafiya zan yi Mom, idan sun gaji da jira na sai su aiko min ita".
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasyFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...