💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Sixty Four*
Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta wanke idanuwan ta ta fito, a hankali ta taka ta isa kan gadon ta hannayen ta a saman fuskar ta, kwanciya tayi tana sake cusa kanta a jikin gadon, gaba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi, Usman yana son zame mata matsala a Rayuwa, shin me yake nema da ita ne yanzu? Ada ba ya ƙaunar ta amma yanzu yana nuna wa duniya yana son zama da ita? Shin ko dai wani abun ne yake son sake aikata mata? Shi ne ta kasa gane wa
"Allah ya fi ka Usman baza ka taɓa cin nasara a kaina ba, duk yanda zan yi sai na bi domin rabuwa da kai". Tayi maganar a fili tana share hawayen da suka soma sintiri a fuskar ta.
Tana nan kwance sai ga Aunty Amarya ta shigo jin ta shiru da tayi
"Lafiyan ki kuwa Ɗahira?"
Ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta gyaɗa mata kai tana cewa, "eh Mama".
Ɗan ƙura mata ido tayi ganin yanda fuskar ta duk ta sauya idanun ta suka kumbura, kowa ya ganta ya san tayi kuka, amma ta san cewa hakan na da alaƙa da zuwan Usman ɗin, ba dai tace mata komi game dashi ɗin ba, sai cewa tayi, "ta fito ta yi Breakfast". Sannan ta fice
Itama tashi tayi tabi bayan ta, saman dainning ta zauna ta zuba arish da egg ɗin dake wajen a cikin Plate, sai dai gaba ɗaya ta gaza kaiwa baki saboda kawai ƙamshin be mata ba, gajeren tsaki taja tana miƙe wa
A lokacin Aunty Amarya ta fito ɗaki tana kallon ta tace, "ina kuma zaki je baki ci ba kin zuba zaki tafi?"
"Mama bazan iya cin komi a wurin ba".
"Saboda me? Ko tea ɗin baza ki haɗa ki sha ba?"
"Mama bazan iya sha ba wlh, na san ina sha zai saka Ni amai".
Da kallo kawai Aunty Amaryan take bin ta, sai kuma tace, "to me zaki ci sai na dafa miki tunda baza ki zauna da yunwa ba?"
"A'a Mama bari zan yi da kaina".
"To ki kula". Tayi maganar tana juya wa ɗaki
Ita kuma Ɗahiran ta wuce kichen, kai tsaye inda suke ajiye ƙullun koko ta wuce ta ɗiba kaɗan, sai ta ɗaura ruwan zafi. Wake ta samu ta sirfe ta zuba kayan miya ta markaɗa a blender, lokacin har ta dama kokon ta ta sake a jug sannan ta gama haɗa ƙullun ƙosan ta, sai ta ɗaura mai a wuta ta soma soya ƙosan, tun a wutan tana tsame wa take haɗiye shi da zafi-zafin shi. Kafin ma ta gama ta cinye sai ɗan kaɗan da ta bari, ta zuba kokon a Cup ta zauna nan ta cinye sauran da kokon
Umma ce ta shigo ta same ta a kichen ɗin, sai ta dube ta tana murmushi tace, "a'a yau kuma kwaɗayin koko da ƙosai ake ne babu tayi?"
Murmushi Ɗahiran itama tayi tace, "eyya ai ban san zaki ci bane shiyasa na cinye, amma akwai raguwan kokon".

YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasyFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...