💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖*
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
'''An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani'imcin sarki jalla Ta'ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku'u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
"Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah".
Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la'asar, lokacin faɗuwar rana da na isha'i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al'umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
Allah ya sa mu dace.'''.
*EPISODE Twenty Six*
*SUNDAY*
Gaba ɗaya sun taru a General Parlour kamar yanda al'adan gidan yake, sai da suka gama raha da nishaɗin su, sannan Kaka ya soma magana da cewa, "Kai Fadil ki rawo Fodio tunda ya ƙi zuwa"."To Kaka". Fadil ya amsa mishi da sauri yana tashi ya fita
Babu jima wa sai ga Fadil ya dawo, ya isar da saƙon zuwan Usman
Kamar mintuna biyar da shigowar sa ne, Usman ya shigo yana ciccin magani, fuskar nan ko alamun fara'a babu, babu wanda yayi masa magana sai Big Dady dake faman hararan sa, sai dai shi ɗin be ma san yana yi ba, tunda be kalli kowa ba, ya samu wuri ya zauna gefen Baffa, sannan ya gaishe su yana latsa wayan sa
Kowa ya amsa, banda Big Dady da hakan ya ƙular da shi, a fusace ya ce, "kai Usman wannan wani irin ɗabi'ar banza ce? Ina ce gaishe mu kake yi amma kanka a waya?"
Sai a lokacin Usman ya ɗago kansa, sai dai be ce komi ba, illa jikin sa da yayi sanyi ya zame hannayen sa daga wayan ya bar sa a saman cinyan sa
Zai sake magana Big Dady, sai Kaka ya tare shi da faɗin, "bar wannan maganar Noor, mu Yi abunda ya tara mu, kasan halin wannan yaron meyasa kake son ɗaukan zafi da shi ne?"
"Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu".

YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasiFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...