💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_*NATSUWA A SALLAH*
_Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman._
_A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu'uminun ana faɗa mana cewa:_
_"Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali'u ne."_
_Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa. Allah yasa mu dace._.
*EPISODE Thirty Eight*
*WASHE GARI*
Tunda aka yi sallan asuba Usman be dawo gidan ba, be kuma bari kowa ya gansa ba ya bar masallacin.
Ita kuwa Ɗahira tunda ta tashi tayi sallan asuba itama, ta sake komawa barcin, dayake akwai zazzaɓi a jikin ta shiyasa har gari yayi haske bata farka ba, sai da taji hayaniyan ƴan biki da wasu suka zo su sake ganin ɗakin nata, kasancewar a lokacin za su tafi, shi ne ta farka, lokacin 12:00pm.
Har ciki suka shiga suna ta mata tsiya, ganin ta da suka yi tana ta barci
Ita dai bata ce musu kanzil ba, illa murmushi da take tayi, sai kuma daga baya ta gaishe su.
Ba su wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi.
Sake koma wa tayi ta kwanta, don sosai kanta yake sara mata sakamakon tashin ta da suka yi, ta rufe ido kenan taji an hankaɗo mata ƙofan ɗaki, da sauri ta buɗe idanun ta tana bin Yusra da ta shigo da kallo
Ita kuwa sai faman taɓe baki take yi tana girgiza jiki, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Ɗahiran tace, "baƙar munafuka! burin ki ya cika kin auran min Yaya, to wlh ki saka a ranki, kamar auren nan ya rabu ne, ba ke ba zama a gidan Yaya Usman, domin ba ya ƙaunar ki, ba kuma zai taɓa ƙaunar ki ba, wlh dani dake yanzu ma muka soma ƴar tsama".
Yanda ka san t.v haka Ɗahira take bin ta da idanu, har sai da ta dire Aya kafin ta tashi zaune tana bin ta da kallo sosai, ko kaɗan ba ta jin daɗin Jikin ta, kuma har ga Allah ba ta son ta biye mata, amma kuma gani take yi idan har ta bar ta ta tafi bata mayar mata da martani ba, to, tabbas nan gaba ma zata dawo tayi mata irin wannan cin mutuncin, kuma zata ga kamar tsoron ta take ji, don haka ta saki guntun murmushi tana kallon ta tace, "wa kike da suna? Yusra ko? Ni ba sa'an yin wasan ki bane, tun wuri ki kama kanki, domin shiru-shiru ba hauka bane, wlh ina ƙyale ki ne kawai don Ni ba Kaza bace da zan zauna kullum ina sa'insa da ke, na san mutuncin kaina; na kuma san kima ta, amma wlh muddin kika sake shigo min gida na, kika yi min irin wannan halin karnukan, zan baki mamaki Yusra, zan nuna miki Ni ba'a sha na a warke, domin zan nuna miki ainihin hauka na wlh".
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasiFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...