Episode Sixty Three

152 13 8
                                    

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

*EPISODE Sixty Three*

Ta san cewa wannan watan ne kawai bata ga period ɗin ta ba, amma bata ɗau abun da wani tunani ba tunda wani time ɗin tana tsallaken wata. amma taya har tana da cikin wata uku ba tare da ta sani ba?

"Ya ilahi... Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba". Tayi maganar tana zubar da hawaye sosai daga fuskar sa

Sai kuma ta lumshe idanun ta lokaci ɗaya abinda ya faru a wancan ranan ya dawo mata, tabbas ranan na ɗaya daga cikin ranakun da baza su taɓa gushe wa a duniyar rayuwar ta ba...

A ranan Baba Jaure ya tafi jeji da yammacin ranan wanda yace musu "sai zuwa gobe zai dawo"

Zuwa dare sai ga hadari ya haɗu. Tana zaune tana ɗan matsa ƙafafun ta tana bin su da magani

Sai ga Usman ya shigo ɗakin. Zama yayi yana bin ta da kallo wanda ita tuni ta kawar da nata idanun tunda tayi mishi kallo ɗaya tana sake haɗe rai

Kamar ta tambaye shi abinda ya shigo dashi ɗakin, sai kuma taga wahalar da kanta zata yi kawai

Kamar shuɗewar mintuna biyu duk idanun sa na kanta, sai kuma ya buɗi baki yace, "kawo in taya ki".

Shiru tayi masa bata kalle shi ba bare ya sa ran zata tanka shi

Sai ya taɓe baki yace, "don ma kin samu ina kula ki shiyasa kike min abinda kika ga dama ko? Yayi kyau". Yafaɗa yana ɗauke kai

Duk bata kula shi ba, domin yi ma tayi kamar babu shi a ɗakin.

Ruwan ne ya sake kece wa kamar da bakin ƙwarya, sai ta ɗaga kai ta kalli ƙofan, sannan ta mayar da idanun ta kanshi tace, "Malam ka fita zan kulle ƙofa".

"To na hana ki ne?" Yayi maganar ba tare da ya kalle ta ba

A fusace tace, "ka san dai bazan iya kwana da kai a ɗakin nan ba ko? Ko ka fita ko in fice in bar maka".

Ɗan kallon ta yayi yaga alamun fa a sama take, sai be ce komi ba ya tashi ya fice

Taja tsaki tana raka shi da harara wanda be san ma tana yi ba, lallaɓa wa tayi ta tashi a hankali ta isa ƙofan ta tura shi, kana ta koma ta kwanta a shimfiɗar ta, ta ɗan jima tana tunanin da ya zame mata jiki, wanda ba komi bane sai tunanin mutanen gidan su, sai kuma daga baya tayi addu'a ta shafa ta juya kwanciya tare da rufe idanun ta, babu jima wa kuwa barcin ya fizge ta.




******

Fannin Usman kuwa tunda ya fita sai yayi tsayuwar sa a tsakar gidan ruwa na ta dakan shi, sai da yayi sharkaf wanda ya ɗau kusan mintuna goma a cikin ruwan, kafin ya samu ya wuce ɗakin kwanan shi, kayan jikin shi ya cire ya sauya da wani riga da wando farare na Fulani, sai kuma ya kwanta yana ta faman tunani, gaba ɗaya zuciyar sa ta hana shi sukuni babu abinda yake tuna wa sai Ɗahira, da sanda lokacin bata farfaɗo ba yana wanke mata jiki, har tunanin sanda ya ganta babu riga a can Turkay sai da ya faɗo mishi, shi kansa be san yana murmushi ba tsaban nishaɗin da yake ji a ranshi.

DOCTOR'S FAMILYWhere stories live. Discover now