💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*HADHISI *
_Aisha (may Allah be pleased with her) was quoted as saying, "The Messenger of Allah (may peace be upon him) married her when she was six years old, and she was nine years old with him, and Allah took her life when she was eighteen years old." Reported by Muslim._
.
*EPISODE Thirty Seven*
K.B ne da Aunty Amarya a Parlour'n zaune, ita kuma Umma tana kichen tana shirya abincin ranan da bata kammala ba
"Ƙanwa ta ashe kina ciki kin maƙale ina ta tambayar ki?" Cewar K.B yana kallon Ɗahira da suka ƙariso wajen tare da Fadila
Dariya tayi tace, "Yayana anya baka neme Ni ba dai, Tunda ai Mama ta san ina ɗaki".
"Aff to ai yanzu ne na soma maganar taki".
"To magana ta fito fili kenan". Tafaɗa tana dariya
Zama Fadila tayi gefen sa, don ita Aunty Amarya har ta tashi ta shige ɗaki ma
Gaishe sa Ɗahira tayi
Ya amsa yana cewa, "wai ƙanwa ta ciwo kika yi kika rame haka? Ko dai zullumin auren ne?" Yayi maganar cikin barkwanci
Murmushi kawai tayi
While Fadila tace, "Nima haka na gani yaya, wai ciwo tayi".
Tashi Ɗahira tayi tace, "bari dai inje in dawo Kaka na kira na sai muyi magana, I have something to talk to you about. yaushe Shamsiyya zata zo ne?"
Taɓe baki yayi yace, "to ki dai kira mijin ta ki tambaye sa, amma bani ba, tunda Ni ga nawa tazo".
Dariya kawai tayi ta wuce ta bar su nan. Ta san halin K.B idan ta biye mishi babu inda zata je
Part ɗin Kaka ta wuce kai tsaye, tana shiga ɗakin sa da sallama
Ya amsa mata yana zaune kan gadon sa yana duba wani ƙaton littafi na addini
"Taho Mata ta". Yayi maganar yana kallon ta da murmushi a kyakykyawar face ɗin sa
Taho wa tayi ta zauna gefen sa tace, "Kakus nayi kewar ka". Ta ƙare maganar da jan gemun sa
"Me too My wife, bayan ma yanzu kin dena nema na, har sai na aika a kira ki kike zuwa, yanzu kenan idan kinyi auren ma haka zaki guje Ni ko?"
"Eyya Kaka wlh No, I will never run away from you, idan ba ka a rayuwa ta ai kamar babu Ni ce". Tayi maganar tana langaɓe kai
"To amma ciwo kika sake yi ne bani da labari, naga duk kin sake rame wa ne sosai?".
"kai Kakus, sai dai idanun ka ne suka gane maka haka, amma ai dama can haka nake". Tayi maganar tana dariya
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantastikFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...
