💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_*TUNATARWA*
'''Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, "Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba." Abin da yasa haka kuwa shi ne rashin nutsuwa cikin sallah.
Allah yasa mu dace.'''.
*EPISODE Forty Two*
Kyakykyawar parlor'n tabi da kallo, a ranta tana ayyana tsantsan kyawun sa da tsaruwan sa, duk da ba kaya ne me yawa a ciki ba, saboda kun san yanayin tsarin tura wa, basu cika saka karikitai kamar mu a gida ba, amma haɗuwar sa sai kin yi kamar zaki zubar da yawu tsaban kallo. Hotunan sa ne har guda uku a ƙusurwa-ƙusurwa na ɗakin, babu me cewa shi ne sai idan ka yi masa kallon tsab, sabida mugun haɗuwar da yayi, tamkar dai ɗan ƙasan; ba ɗan Nigeria ba, uwa uba ga shi da skin irin nasu, ga kyawu da ya haɗa, ga kuma kayan da ya saka duk nasu ne.
Ɗahira ta saki baki tana kallon Parlor tamkar wata ƴar ƙauye. Sai jin takun takalman sa tayi daga bayan ta, da sauri ta waiga tana kallon sa
Ba ita yake kallo ba, da alamu ma har ya shiga ɗakin sa, duba da har ya cire rigan saman Jikin sa; yana sanye da Singlet da dogon wandon da ya zo da shi, fuska babu walwala ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin tsararrun kujerun parlor'n
Ɗauke kai tayi tana haɗiyar yawu a hankali sabida jin maƙoshin ta ya bushe, tsayuwan taci gaba da yi a inda take, tunda be ce mata ga inda zata shiga ba, sabida ba wani ɗakuna ne da yawa a gidan ba, daga ɗakin sa sai irin sa na baƙi, sai kuma kichen me haɗe da store har biyu da ƙofa ta baya da zai kai ka Garden ɗin gidan, sai kuma Toilet a parlor'n guda biyu shima.
Tana nan tsaye ya ƙi ya ce mata komi, dole ta ajiye wani ƙyaliya nata ta kalle sa tace, "ina ne ɗakin da zan zauna?"
Uffan be ce mata ba, ya ci gaba da latsa wayan sa, har sai da ta cire rai da zai yi magana, sannan ya ce, "baki da muhallin zama a gidan nan, taimako ɗaya zan miki". Sai ya ɗago kai yana kallon ta, hakan yasa suka haɗa idanu, kallon kallo kawai suke wa juna, ko wanne na cike da juriyan kallon ɗan uwan sa, domin yanda gaban su ke wani irin bugawa a tare sai ka ɗauka suna jin bugun zuciyar junan su, shi nashi har da wani tsoro ne ya mamaye sa, wanda duk idan dai ya kalli ƙwayan idanun ta masu Colour'n nan, to sai hakan ya ziyarce shi
Wani irin ɗaure fuska ya sake yi, sai tayi saurin sad da kanta ƙasa, domin itama ta kasa ci gaba da kallon sa
"Ga lungu can, nan zaki riƙa kwana". Ya nuna mata wajen kichen da hannun sa, sannan ya ci gaba da magana, "ko a parlor'n nan ban yarda in ga ƙafafun ki ba".
Sosai zuciyar Ɗahira ke suya da maganar nan nasa, sai dai ta kasa cewa komi illa sake duƙar da kanta da tayi, take hawaye suka soma sintiri a saman kyakykyawar fuskar ta sabida jin rainin hankalin sa da baza ta iya ɗauka ba, "wai me yake nufi ne? Ni ce zan riƙa kwana a can kamar almajira?"

YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
ФэнтезиFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...