Episode Thirty Three

193 9 1
                                        

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:_
_"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
_Allah yasa mu dace._

.

*EPISODE Thirty Three*

"Kina da kuɗi a tare da ke? Domin kai tsaye wajen Malami na za mu wuce".

Kallon ta Ayush tayi, sai kuma ta girgiza mata kai alamun "A'a" kafin tace, "Malami kuma Safra? Wanne irin Malami? Me kuma zamu yi a can?"

Dariya tayi still tana taunan cwhengum ɗin ta tace, "neman biyan buƙata mana Ƙawata, Ai dole sai da haka, don wlh bari kiji, irin waɗannan Guy ɗin ba naki bane, kee wlh bazan yi kaffara ba, idan har kika ce ta haka zaki jawo hankalin sa, babu taimakon Malamai, to, zaki dauwama baki yi aure ba, domin wlh sai kin ruɓe a gidan ku. Yanzu dai za mu wuce wajen Malam, inyaso zan ranta miki kuɗi idan muka dawo ki bani".

Ayush dai ta kasa cewa komi illa kallon titi da take yi, tana me tunani a zuciyar ta, "anya wannan hanyar da ta ɓullo wa kanta me ɓulle wa ne? Domin tasha jin yanda mutanen da suke zuwa wurin boka suke ƙare wa, to amma dogon burin ta fa? Hakan na nufin muddin bata nemi taimako wajen su ba, to, har abada baza ta taɓa auren Usman ba?..".

Kai tsaye hanyar Zaria suka nufa, sun kusa shiga Zarian, sai suka karya kwana suka bi wata hanya, tafiya miƙaƙƙa suka yi a cikin hanyar me kama da jeji, domin ko kaɗan babu gida gaba bare baya. Sun yi tafiya sosai kafin suka soma hango ƙauyaku, inda suka sauka a wani ƙaramin gida da aka zagaye shi da kara, sai bukka da aka yi su da yawa a wajen, shiga suka yi gidan, inda Ayush sai kalle-kalle take yi tana biye da Safra dake tafiyan ta kai tsaye, ba tare da wata fargaba ba, ga duk kan alamu ta saba da zuwa

A bakin wani bukka dogo suka dakata, inda Safra ta hau faɗin, "an gaishe ka Malam, an gaishe ka Malam".

Daga ciki dariya ne ya biyo baya, inda yace, "Hajjaju Safra da baƙuwar ta, maraba da zuwa, za ku iya shigo wa".

Shiga Safra tayi, inda Ayush ke biye da ita

Yana da faɗi cikin bukkan, babban mutum ne fari sol yake zaune a gaban wani ƙaton ƙwarya baƙi, yana ɗaure da zanin atamfa a jikin sa yayi tamkar yanda ƴan Saudiya suke yi idan za su yi aikin hajji, sai gashin kansa me yawan gaske tamkar na mace, ya zubo masa har kafaɗun shi

Da kallo ya bi su dashi har suka zauna, kafin yace, "an sanar min da zuwan ku tun kuna hanya, kuma na san abinda ya kawo ku".

Ayush ce kawai tayi mamaki da kalaman sa, ban da Safra da ba yau ta soma zuwa ba

DOCTOR'S FAMILYStories to obsess over. Discover now