💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Fifty Two*
Bayan ya tashi daga barcin alwala yayi ya gabatar da sallan la'asar da ake kira a lokacin, bayan ya idar sai ya shirya cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba ko yaushe, riga baƙa da blue ɗin wando jeans, kayan sun haska shi sosai domin sosai suka yi masa kyau, komin sa yana yi ne a natse a kuma sanyin yanayin sa, turare ya feshe jikin sa dashi kana ya ɗauki wayan sa ya saka a aljihun bayan wandon sa ya fito daga gidan, hannayen sa zube cikin aljihu yana bin yanayin garin da kallo, da alamu hadari ne ke son haɗuwa domin har an fara yayyafi kaɗan-kaɗan duk da akwai rana be gama shige wa ba, murmushi kawai yake saki wanda samun ka ga yayi sa aiki ne, yana bala'in son wannan yanayin na damina, a ransa yana jin daɗin dawowar sa a dai-dai, ya san yanzu can kafin daminan su tayi nisa nan sun sha ruwa sosai
Tafiyan sa a natse yake yi har ya isa cikin babban gidan su, kai tsaye Part ɗin su ya wuce, yana tura ƙofan da sallama a bakin sa
Hajiya dake ƙoƙarin zama a kan kujera domin fitowar ta kenan daga ɗaki ta idar da sallah, da zummar idan ta huta ta tashi ta ɗaura girkin dare, sai jin sallaman ɗan nata tayi kamar a mafarki, hakan yasa tabi sa da kallo don ta kasa amsa mishi sallaman ma
Shi kuwa murmushi ya sake saki, sabida haka kawai yake jin sa cikin farin ciki, duk da a wani ɓangare na zuciyar sa yana jin wani irin buga wa da take yi tamkar wani abu na shirin samun sa, amma hakan ya ɗaura dalilin ne kan dawowar sa da gamuwar sa da iyayen nasa, amma kuma duk abinda za su yi shi dai a shirye yake
Muryan Hajiyan ne ya dawo dashi hayyacin sa
"Usman idon ka kenan?"
Takowa yayi ya zauna a kan kujeran dake kallon inda take tsaye
Hakan yasa itama ta zauna tana shirin magana
Sai ya riga ta ya gaishe ta
Amsa wa tayi fuskar ta babu wani walwala tace, "yanzu ka kyauta kenan? Abun da ka aikata ka kyauta mana kenan Usman ina tambayar ka?".
Shiru yayi kawai be ce mata komi ba, illa shafa ƙeyan sa da yake yi, sai dai ya rage walwalan dake fuskar sa
Cike da takaicin halin sa tace, "wlh kai da Dadyn ka tunda irin tarbiyyan da muka baka kenan, ka jira shi ya dawo zaka ka hukuncin da za su yanke a kanka". Tana faɗa ta tashi tayi hanyar kichen
Shi kuwa da kallo ya bi ta har ta shige, kana ya miƙe ya nufi kan dainning ganin cololi da yayi a jere, sai da ya buɗe yaga akwai abinci kafin ya zauna bayan ya zaro wayan sa daga aljihu, zuba abincin yayi a Plate ya soma ci, latsa wayan yake yi yana faman zira abincin kaɗan-kaɗan a bakin sa, duk da yunwa sosai yake gallabar sa amma hakan be sa ya ƙi wa abincin cin yanga ba.
Be gama cin abincin ba Big Dady ya shigo parlour'n da sallama, babu inda idanun sa ya sauka sai kan Usman dake shirin kai abinci bakin sa a wannan lokacin, ido kawai Big Dady ya zuba masa
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantasíaFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...