Wani farin mutum ne ya dan manyanta don Akalla zai kai sa'an Abbah ya nufosu ganin yadda Ahmad da drivern suke ta musu ya dafa kafadar Ahmad din "Samari yi hkr a kaika ko Chemist ne a duba sbd kaga kafar tana jini kuma zasuyi dressing su rufe at least wani cutan bazai shiga ba ai ko?" Gyada kai Ahmad yy don mutumin ya masa kwarjini bazai iya musa mai ba tsallaken titin da akwai Chemist don haka suka tsallaka har da mutumin aka gama mai dressing ya biya suka fito ledan maganin dake hanun drivern ya karba tare da musu godia har zai wuce mutumin nan yace "tsaya yarona ina ne gidanku?" Kara hade rai yy mutumin ya takura masa kuma shi sauri yake gashi baison mgn ga mutumin ya masa kwarjini shiyasa ya kasa tafia Alhajin ya lura da hakan yy murmushi don yana da irinshi hanya y nuna kafin da kyar yace "nan Na'ibawa nake" Alhajin ya dubi drivern shi "Mal Bala bari mu koma dayar motan kai ka maidashi gida kaga Kafan ya riga ya kumbura bai dace yy tafia da nisa haka b"
Bb yadda Ahmad ya iya don ba'a bashi daman musu ba Alhajin ya riko hannunshi suka dawo inda motoci biyun suke a fake bude bayan motar Alhajin yy wata farar mace dake dauke da ciki ta fito da kyar don saida ma ya taimaka mata tana tmbyr yaya fatan yaron da suka kade baiji ciwo sosai ba don kasa fita tayi ta duba Alhajin ne ya bata amsa yana nuna mata Ahmad gaidata yy ta amsa da fara'a tana masa sannu dayan motan Alhaji y bude yara ne guda guda uku Namijin zai kai sa'an Fatima sai 'yan biyu mata suma zasu kai shekaru Hudu gefensu Matar ta shiga ta zauna Alhajin ne ya shigar mata da Kafafun ta tare da rufewa ya bude gaban motar Zaune wani yaron yake a tsaye yakai Ahmad ko ma yadan Zarta shi fari ne sosai yana sanye da Glasses da suka fi kama da Na karawa ido karfin gani ya jingina bayanshi da kujeran yana ta shakan barci dan bubbuga kafadunshi Alhajin yy "kai Sadiq tashi mana" da kyar ya bude idanunsa da sukayi jawur alamun bacci yace "Papa an iso ne?" Kamo hannunshi yy ya fito dashi ba tare da ya bashi amsa ba ya shige gaban motan inda ya fiddashi sannan yace "je shiga wajen Mal Bala ku tafi" bai jira cewanshi ba yy wa Ahmad Allah y sawwaka ya rufe motar driver yaja sukayi gaba sai kuma suka tsaya aka bude motar Karamin yaron dake bayan motan ne ya fito da gudu yazo ya rugume mai gilashin yace "daman zaka tafi ka barni ne Yaayaa?" Shafa kanshi yy baice komi b Mal Bala ya bude musu bayan motar suka shiga ya rufe budewa Ahmad gaba yy shima ya shiga bayan sun fara tafia ne Mai gilashin yace "Baba Bala ina zamuje ne wannan kuma waye ne?" Mal Bala ne ya bashi amasa yana tukin sa "Baban Baba wlh kadesa mukayi kana ta bacci abinka shine Alhaji yace a kaishi gida sbd kaga yana sauri ya isa gidan Baba Malam wajen bazai isa bane yace ka dawo nan in yaso idan na saukeshi sai mu samesu chan" ajiyar zucia ya sauke tare da kallon Ahmad da idanunshi ke lumshe yana tunanin don ya fito daga 'yan lemo ne bayan yayi dakonsa yana sauri yaje kada a tashi Fatima a Schl tayi ta jira taboshi mai gilashin yy "sannu kaji ciwon yana zafi ne?" Dan murmushi Ahmad yayi jin yadda ya masa mgn kaman wani yaro ya girgiza kai "a'a ba komi" karamin yaron ne yace "Yaayaa ai kana bacci Baba ya tureshi da mota ya fadi ina kallo kuma" "to naji ai na gani ynx Saleem" ganin yadda Ahmad yake kulle idanu ne Sadiq yace "kaga Baba Bala a kaishi asibiti wlh zafi yakeji kaga yadda yakeyi" juyowa Mal Bala yy ya kalli Ahmad yana dan daria "kai Baba Sadiqu wannan fa ba irinka bane don dakyar ma ya yadda aka kaishi Kyamis a cewarshi ba komi don baisan ma yaji ciwon ba sai da naga jini na zuba" zaro idanunshi dake cikin gilashin yy "chabdi ai ni wallahi ko kwarzane nayi ina sani bare ciwo mai jini sannu to meye kake ta rufe ido ko bacci kk ji" Saleem yy saurin cewa "Yaaya ko shima yy Video Game ne baiyi bacci ba irin naka" Ahmad ya dan juyo "a'a tunani nake ne kada Kanwata su tashi makaranta zanje daukarta daman abinda ya fito dani daga kasuwa kenan" "Okay to Baba ka kara sauri kar ya makara" dai2 isowarsu Unguwar Ahmad ne ke nuna wa Baba hanya har dai suka iso wajen SILVER PEN yace wa Baba "Baba barni a nan kawai ya isa" dakatawa Baba yy bayan ya fita ya musu godia ya nufi kofar Makarantar daidai fitowar Fatima tana dube dube da sauri Ahmad ya buya a bayan bishiyan dake kofar makarantar saida ta giftashi kafin ya fito cikin sanda ya rufe mata idanu ta baya kama hannun nashi tayi tana daria "ai nasan kaine Yayana budeni kawai" murmushi yy ya bude mata idanu sai kuma yace "ni gaskia nayi fushi kullum sai kiita ganeni bb halin in miki basaja kenan" ya karisa yana juya wa zagayowa ta gabanshi tayi tace "yi hkr gobe kamin to bazan gane ka ba kaji Yayana" daria ya mata ya amshi jakanta sai lkcn ta lura da Bandage a kafarshi da sauri ta tsugunna tana kallon kafan sai tayi rau2 da ido tana shirin kuka tace "Yayan me ya sami kafar ka?" Dagota yy "ke bb komi dan kujewa ne nayi a hanya kinga kuma ai ansa mgn ynx zai warke bana ma jin zafi" ita dai bata yadda ba sai ga hawaye Shaa Ahmad ya dafe kai "haba Bby meye abin kukan kuma nafa cemiki banjin zafi ko wuce mu tafi gida" mika hannu tayi "to bani jakana ai baka da lafia" nokewa yy "muje ko in hada dake in dauka kinsan ni ai" kama hanya tayi tana share hawaye ya riko hannunta suka fara tafia Motar su Baba ya gani Sadiq jingine ya zuba misu ido yana ta murmushi tabbass yana son kannenshi amma soyayyar dake tsakanin Ahmad da Kanwar shi ya matukar burgeshi kallon mamaki Ahmad ya masa yace "yaa baku wuce bane?" Sadiq ya bude masa bayan motar "ai Papa cewa yy mu kaika gida don haka dole mu kaika in ba haka ba yaji fada Zai mana don wlh sai ya tmby kuma in mutum yy karya ganewa yake nd kaga wannan Akun na bayan mota shi za'a tmby don haka kawai kayi hkr mu kaiku" "haba bb komi fa nan kasan layi muke" Sadiq ya amshi Bag din Fatima yasa a bayan motan itama ya kama hannunta suka shiga babu yadda ya iya shima ya shiga gaban motan Baba yaja Ahmad na nuna musu hanya Sadiq ya dubi Fatima "yy sunanki kanwata?" Juyowa Ahmad yy ya banka mata harara "ke Baby baki iya gaisuwa b ko?" Girgiza kai tayi da sauri don koda Ahmad ke wasa da ita tana matukar tsoron shi domin yana bata tarbiyya tamkar yadda Ummy ta bashi Gaida Baba tayi sannan Sadiq dake gefenta murmushi yy shidai lamarin su yana birgesa sosai yace "Baby sunanki?" "A'a Yaya ne yake cemin ni sunana Fatima" zaro ido yayi "waiwaiwai! Sunan Momma to nikam sedai in canza miki wani kin yadda" Gyada kai tayi yace "to ni banison wanda Yaya yake ce miki zan dinga cewa Princess ko" daria tayi tace "inaso da dadi Princess" Ahmad dake gaba yy murmushi don bayan Halima Sadiq ne mutum na biyu da yaga ta sake dashi cikin sauri Salim yace "Yaya ni shine baka cemin Prince ai nima Baban Momma ne" hararanshi yy "ai kai Kaka ne shiyasa" Gwalo Fatima ta masa ya kuwa hade fuska Ahmad yace "rabu dasu kai kafi Prince ma ai kyau" yace "yauwa nima ynx kaine Yaya na na canza wannan" ya fada yana nuna Sadiq Fatima ta murguda mai baki "ai de Ya fika kyau shine ma me kama da Prince din ko" ta tmby Sadiq yace "yes Princess na fisu kyau duk gidansu" daria duk sukayi "yauwa Baba mun iso" cewar Ahmad yana nuna kofar gidan su Parking Baba yy suka fito gaba dayansu godia Ahmad yy musu ya karbi jakan Fatima dake hannun Sadiq ya mika mishi hannu sukayi musabaha sannan ya shafa kan Salim yace "Kanina Bye ko" daga mishi kai yy yana kallonsu Baba ne ya ciro Kudi zasu kai 10k ya mikawa Ahmad "gashi inji Alhaji yace kasai magani Allah ya kara sauki" girgiza kai Ahmad yy da sauri yace "Don girman Allah Baba kuyi hkr amma Wlh bazan karbi komi ba hakan ma ngd sosai ai tsautsayi ne badan kun matsa ba ma da wlh Ko Chemist din ban zuwa kace wa Alhajin ngd kawai" yaja hannun Fatima bb yadda Baba Bala ya iya haka ya maida kudin tunda Ahmad din ya hadasa da Allah kuma yy rantsuwar bazai karba ba shikam Sadiq murmushi yy don yanayin Ahmad na Burgeshi daga murya yy don sun kusa shiga gida yace "My Princess babu sallama ne?" Juyowa sukayi ta daga masa hannu "Bye Yaya" yace "No ai kince nine Prince so ni banason Yaya" ta sake dago hannun "to Bye My Prince" yace "yauwa Bye kanwata, Abokina sai mun sake haduwa" to kawai Ahmad yace suka shige gidan suma su Sadiq suka shiga mota suka tafi yana jin dadin yy aboki don tunda suka dawo garin baida abokai sbd Babansu Sojane na Sama kuma ba anan Kano yake ba suna Lagos ne basu jima da dawowa b don saida yayi NECO ma shi kuma kaninsa ya gama Primary shine Momma tace ita tafi son su dawo sbd su san 'yan Uwa kuma su koyi al'adun Hausawa don so suke su zama 'yan Kudu ta gaji da halinsu ko Hausa basa son yi yaran nan kuma sun iya sarai tayi tayi har ta hakura shiyasa kawai ta sami Papa da maganar to da yike shima mai kishin asalinshi ne yasa ya yadda ynx watanninsu biyu da dawowa inda daman Papan nada gida a nan din sannan iyayenshi ma a Kanon suke zaune
Tunda suka je lbrn Abokinshi yake baiwa Momma tana ta masa daria wai sarkin zumudi tun ba'a zama abokan ba y fara rawan kafa saida Kakarsu ta korashi waje tana cewa "ka barta taji da kanta kazo kana damunta ko su Afrah dake kankana basu manne mata kamar kai fice daga nan" tashi yy ya fita yana cewa "ba'a sonki ma barinje wajen Ummu Amarya ta" tace "oho ita ai ta iya wa fitinar taka ku karata"
Koda Baba Bala ya maidawa Papa kudinshi yy mamaki yadda yaran yanzu suka baci dason kudi amma yaron nan yaki karba gaskia nutsuwa da hankalin yaron ya burgeshi sosai daga gani ya fito daga gidan tarbiyya
#Smarty💞

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...