Suna zaune suna ta shirmensu ita da Sadiq yayinda Ahmad ke gefe yana kallon TV jifa2 yakan juya ya kallesu yy murmushi yana matukar son Fatima fiye da kanshi hakan yasa duk wanda ya nuna mata so shime yake sonshi don haka yaji ya aminta da Sadiq yana kuma kaunarshi shima
Sallamar Mai gadi ne ta katse su nan ya sanar dasu wai Baba Bala yana jiran Sadiq sam baiji dadin tafiar ba amma bb yadda ya iya sbd dare yy kuma bayaso nan gaba in yace zaizo a hanasa hakan yasa ya mike bayan ya tattara takardun Fatima yasa mata cikin jakar ta tare suka fito itama duk tayi wani iri har bakin motar suka rakashi tana tmbyr shi ko gobe ma zai xo? Yace "a'a nima sai Yaya yaxo gidanmu kafin na sake zuwa" ganin ta bata rai yasa yy daria "to shikenan zanxo kar kiyi kuka My Princess" ta gyada kai ya bude bayan motar ya dauko ledan da daxu yaxo da ita ya mika mata kin karba tayi tana kallon Ahmad karba yy ya bata cikin murna tace "nagode My Prince" yace "b komi amma daga yau idan na baki abu ki karba nima ai Yayanki ne kar ki sake min haka indai kina so in sake zuwa" to tace sukayi sallama da Ahmad har ya kusa shiga mota tace "ka gaisheda wannan yaron" daria yy don yasan Salim take nufi yace "to wannan yaron zaiji" ya shige mota suka tafiHaka rayuwa taci gaba da tafia Sadiq yana yawan zuwa gidan su Ahmad idan sunkai Fatima makaranta su wuce yawon su shakuwa mai karfi ya shiga tsakanin su tun Momma tana hanasa har dai ta hakura tunda tana matukar son shi cikin yaran kuma taga yadda ya damu da su Ahmad din kullum cikin lbrn su duk miskilancin da ake ganin yana dashi indai wajen lbrn Princess ne da Yayanta to sai dai ka gaji da surutun shi da farko tayi complain wa Papa amma yace ta rabu dashi yy bincike Ahmad din baida wani matsala kuma shima ya yaba da hankalin yaron don haka indai ba wasu canjin dabi'u ta gani wajenshi Sadiq din b ta kyale su hakan yasa ta saka mishi ido tare da musu Addu'a kawai daman ita ba mai yawan fada bane ga kuma yadda take fama da kanta bata taba ciki mai wuya haka b don hakane ma Papa yace daga wannan ta hakura kawai wadanda suka samu ma Allah ya basu ikon tarbiyyantarwa
An dauki tsawon watanni uku da fara abotar su Sadiq da Ahmad kuma ko yaushe Sadiq yaje gidan yana ganin abubuwan dake faruwa tsakanin Ahmad din da Mama Indo har ma wani lkcn da Abban su shi tunda yake bai taba ganin maganar kirki ya shiga tsakanin Ahmad da Baban nasu ba saidai idan wannan matar ta sakoshi gaba yazo ya zazzageshi su tafi babu kuma wanda ya damu da ganin Sadiq din a gidan don dayawan lokuta ma idan ya hadu da Abban shi kadai yakan gaidashi kuma abin mamaki yana amsawa abinda ya lura dashi shine kamar Abban yana tsoron matarshi in suna tare sai yaita abu kamar yaro gaban uwatai
Zuwa ynx Sadiq ya fahimci Babarsu Ahmad bata gidan amma bai taba tambaya b sbd shi wani irin mutum ne da in har abu babu ruwanshi to bai nuna alamar ya sani ma don haka bai taba maganar b ya bar Ahmad din har sai ranar da yaji yana bukatar sanar masa kafin duk da yana tausaya musu musamman idan yaga yadda Momma keyi dasu sai yaji hawaye yaxo mai in ya tuna duk kankantar Fatima ita bata samun wannan gatan duk da dai Ahmad na mata komi amma ai uwa dabance musamman ga ita dake diya mace ma hakan yasa ya daina yawan tadin Momma a gidansu sedai kawai yace tana gaida takwararta da Babanta daga haka baya karawa gudun kada suji babu dadi
Kullum cikin mita yake Ahmad yaki zuwa gidansu shikam sedai yy murmushi kawai don bawai baya son zuwa bane baya dai samun lkc ne sbd ynx ba kullum yake zuwa sana'a ba duk ranar da suke tare da Sadiq baya ko fita gudun kada ya fahimci halinda yake ciki
Ana cikin haka Momma ta haihu bayan wuyar da tasha wanda daga karshe saida akai mata C.S kuma nan ne Papa yace a juya mahaifar kawai itama ta huta hakan ko akayi kuma Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara aka ciro mata sankaceciyar diyarta mace ana mikawa Papa yace "Maa Shaa Allah yadda kika baiwa matata wahala to dole ai mata takwara" daga nan yai mata huduba da suna Fatima cike da farin ciki bayan an sallamota Sadiq yaxo ya sanar da Ahmad lkcn yana zauna yana jimami tun jiya suna zaune Baba Bala yaxo daukan Sadiq cewar Mamarshi tana asibiti yaso binsu amma lkcn dawowar Fatima daga makaranta yy don haka Sadiq yace ya zauna kawai gashi har ynx shiru sai yaune yake danasanin rashin tmbyr adireshin gidansu Sadiq kuma In Shaa Allah lkcn neman gidansu yy
Yana ta jimami yaji bude kofar falon su yana dagowa yaga Sadiq da saurinshi ya taso ya nufeshi "Bro ya Momma? Jikinta da sauki ko? Duk hankalina ya tashi wlh" daria Sadiq yy ya jawoshi zuwa kan kujera "kwantar da hankalin ka Momma jikinta da sauki daman haihuwa ce amma saida akai mata CS kuma komi yy daidai ynx ma haka an dawo da ita gida sbd bata son asibiti kwatakwata shine akwai Kanwar Papa Gynecologists ce ynx ma tana hanya zata zo ta zauna da ita" ajiyar zuciya ya sauke "to Alhmdlh Allah ya bata lafia amma wlh yau zaka kaini gidanku don kadan ya rage hawan jini ya kama ni sbd tunani" daria sosai Sadiq keyi yace "maganinka kenan tunda baka da kirki ai daman kaine kaki zuwa kuma wlh bb nisa nan bakin hanya ne fa farkon shigowa layin nan ana cewa gidan mu gidan Soja" tsaki Ahmad yy "amma dai kai dan iska ne Wlh daman nan ne gidan ku shine baka taba fadamin b to duk unguwar nan waye baisan gidan ba tun ma lkcn da ake ginawa" Sadiq dake shiga kitchen yace "Oho ai baka nemi ka sani bane" ya dauko ruwa ya fito ya zauna Ahmad na hararan shi yace "kanka ake ji ni tashi muje mu dauko Princess in mata albishir ta sami takwara" dafe kai Ahmad yy "Oh ko tmbyr me aka samu fa ashe banyi ba ashe Baby na ce" suka fita suna tafe suna hira har bakin Schl din sun tarar ma ba'a tashesu b Ahmad yace "ina dai ga irinta time baiyi ba ma shegen zumudinka yasa zamuyi jira" bai tanka ba ya masa shiru suna nan tsaye har aka buga kararrawa students suka fara fitowa chan suka hangosu Halima na rike da hannun ta tana ta magana Halimar tana daria bata lura dasu ba Sadiq ne yaje ta bayansu ya rufe mata idanu yanda yaga rannan Ahmad yy Halima ta razana da sauri ta matsa tana dafe kirji ganin namiji kusa da ita kuma bata gan zuwanshi b rike hannun Sadiq Fatima tayi "My Prince naji kamshin ka ai" yy murmushi tare da zare hanunshi Ahmad kam daria yake sosai ganin yadda Halima ke zare ido sabida tsoritan da tayi sai kuwa ta shagala da kallonshi don yaune rana ta farko da taga yana daria sosai don kullum sedai yy murmushi shima ba sosai ba sai in yana magana da kanwarshi ne
Fatima ta katse yanayin nasu da cewa "Yaya yau da wuri kazo tun ban dawo b?" Jakarta ya karba yana fadin "My Princess albishirinki" tace "goro Yaya menene?" Cikin jin dadi yace "Momma ta haihu kuma kin sami Namesake" da murna tace "da gaske Yaya mai suna na naji dadi zaka kaini in ganta?" "Sosai ma ai kece First din ganinta ma ynx zamuje ki shirya" daria take sosai don tana da matukar son yara sai kuma ta bata rai "Yaya wannan yaron ma ya ganta ko hala ma ya rigani" daria yy "Princess sunanshi Salim fa wai meysa bakwa shiri ne kuma fa Ya girmeki kike ce masa wannan yaron" "nidai bana sonshi hararata yakeyi ni kai kadai da Yaya nake so" juyawa tayi "Aunty kinga Prince dina da nake gaya miki?" Ajiyar zucia tayi ta juyo daga kallon Ahmad tace "na ganshi Faty sannu ina yini Yaya" dan murmushi ya mata "ya kike Auntyn Princess?" Da lafia ta amsa sannan ta dubi Ahmad da murmushi tace "Yaya an yini lafia?" Ya dan kalleta "lafia lau Aunty matsoraciya" rufe fuskarta tayi da karamin Hijab din dake jikinta tana murmushi Sadiq yaje kusa da kunnen Ahmad yace "am I missing something?" Ya mai kallon rashin fahimta alamar kamar ya? Sigina ya mai cikin salonshi na tsokana yana nuna masa Halima da gefen baki ynx kam ya fahimci inda ya dosa ya talle mai keya "tafi da Allah ka tsorata yar mutane" daria Sadiq yy yaja hannun Fatima sukayi gaba suka bar Halima da Ahmad na binsu a baya duk da basa cewa komi har akaxo kofar gidan su ta masa sallama ta shige dan waigawa yy ya kalli gidan nasu ya juyo sai yaga Sadiq tsaye yana kallon shi daria yy sosai yace "wlh something is cooking b/w u two in tayi wari maaji" bai bashi amsa b yayi gaba
Suna xuwa fida sukaci abinci kafin Ahmad yace Fatima tayi wanka zasuje gidansu Sadiq da murna ta shige dakinta don shiryawa daman ranan Thursday ne bb Islamiyya dakin Ahmad suka shiga Sadiq ya kwanta a gadon shi shi kuma ya shige wanka kan bedside drawern shi ya duba yaga takaddu dauka yy yana dubawa wasu tarin plainsheets ya gani kowanne dauke da zane don haka ya fara kallonsu daya bayan daya yana mamaki in ba don asalin zanen yake kallo ba zaice hoto ne sbd yadda zanen ya tsaru tabbas duk wanda yy ya iya zane abubuwa ne kamar su motoci gidaje bishiyoyi da sauransu fisge takardun yaji anyi ya dago yaga Ahmad sanye da dogon wando yana hararansa daga hannu yy "kawae ina neman abun karantawa ne na gansu ina k samosu don Allah wlh sunyi sosai waye ya zana?" Banxa Ahmad yamai yana saka riga har ya gama shiryawa Sadiq bai daina tmbyr shi b bai kuma amsa b sai ma fita da yy yana cewar "in ka gama zuban kazo mu tafi" tasowa yy ya biyo bayanshi a falo suka tarar da Fatima cikin riga da skirt din atamfa gogaggu tayi chas abinta sedai fauda kawai ta shafa don Fatima tun tana karama bata da son shafeshafen su Jambaki su Eyeshadow barta da saka kwalli, fauda da man lebe shikenan tana rike da mayafinta ta tunxuro baki Ahmad ya kwashe da daria ya ture kanta "bakauya kawai to wani ya saki ki dauko ne?" Sadiq yace "My Princess ya kike bata rai bayan kinyi kyau me ya faru?" Mayafin hannunta Ahmad ya nuna masa "bata iya saka mayafi bane kuma tanaso tayi gaye" ya karisa da daria Sadiq yace "rabu dashi Mamana jeki dauko Hijab abinki yafi ma kyau kinji" da saurinta taje ta dauko well ironed black Hijab dinta ta saka suka fito Ahmad ya rufe dakin suka kama hanya
#Smartie💞
![](https://img.wattpad.com/cover/202269501-288-k308204.jpg)
YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...