12

14 0 0
                                    

Tafe suke a motar da Sameer Bhai ya turo drivern da ya dauko su a Airport ranan wanda kuma a cikinta ne jiya aka kaisu mkaranta duk da cewa department dinsu ba daya da Saleem ba amman tare aka kaisu sannan da suka rigashi gama lectures ma tunda yake b jimawa zaiyi b koda aka zo daukarsu sai suka jirasa don tun d suka hadu wajen cin abinci ya sanar dazu yana d lecture daya bayan sun tashi a dan kwana dayan shakuwa ce sosai ta shiga tsakanin su dashi duk kuwa da rashin jituwarsu d Deela san a cewarsa ta cika hantara amman hakan bai hanashi kaiwa har wajen karfe tara a gidan nasu b duk da a waje suka fito suka shimfida carpet sbd yadda suka ga mafi yawancin mazauna arean sunyi wasu kuma bisa kujerun roba da yake kaso tamanin na mazauna unguwar dalibai ne sai daidaikun iyalai da suke da sauran gidajen Tee ce kasancewarta masoyiyar girki tai musu abincin dare jallop din talia da Kifi tunda da rana da kyar ta iya cin Chips a Cafeteria din sbd sam t kasa cin abubuwan nasu coz d safe ma Pancakes din da Ram y siyo musu kasa ci tayi don sam bata d appetite tun tashin ta daga bacci

"Ke bari kiji Wallahi ko kina so ko bakya so ke idn kinga dama ki kashe kanki amma ko gawar ki ce sai an kaita gidan Lawan kinji rantsuwar Dan musulmi"

"Yo innar Talatu ai yarinyar nan fitowa ce kiri² batai ba tace miki kece bata kauna amma fa komi ya nuna a zahiri sam bata sonki da arziki"

"Maganarki gaskia ce Lanto in banda haka ana nuna ma yarinya annabi tana rintse ido duk banda Lawan ma yadda yake farin nan ga kyau uwa uba ga gayu mai zaiyi da wannan abar ga 'yan mata a garin nan kyawawa amma ya nace mata wlh ko uku yace yana so za'a bashi ne a take bb musu"

"Mai kuwa ya gani banda kasancewar ta 'yar binni da iya yaren nasara yaro dan Babban gida duu garin nan ubansa ke mulki sannan bayan ni dake da dangi a Binni na tabbata bb wanda ya taba zuwa inda yaje"

"Yo ai ko itan dake takamar 'yar binnin ce ai bata taba zuwa inda yake b tunda ance a Ikko yake neman kudinsa kinsan ko ai tafi Habuja ballanta wata Kanon banza"

"An daura auren Fadimatu Adamu da Lawan Kabiru Maigari akan sadaki naira dubu takwas lakadan ba ajalan ba"

"A yarinya tayi goshi"

"Kai wai har dubu takwas ya biya lallai Lawal yayi kudi a Legas din nan"

"Hmm kekam Innar Talatu Kakar ki ta yanke saka wlh kin dangwalo arziki"

"Ke ko mutuwa kike kina dawowa aradu sai na karbi hakki na gara ma kawai ki tsaya"

"Fyade aka mata ne?

"Wace iriyar fyade kuma malama da Mijinta"

"Mtsww ku mutanen karkara kuna daukar fyade kalma ce a wajen aure to koda mijin macce ne yai mata wannan danyar aikin sunanta fyade kuma da za'a sako hukumar Human Rights wlh mummunan hukunci za'ai masa"

"Ke kika san wani Homan rais in kina dubata ki duba don ni ko mutuwa tayi banda asara Yauwa"

"Ai wlh ba zamu karbi shege a gidan nan b don haka zuwa zatayi ta bar mana gida"

"Daman yadda take idanu a tsaitsaye ai ansan zata rina wanda ma yafi hakan"

"Wlh to sedai ki bar min gida nima bazan iya ba da abin kunya"

Wadannan sune kalolin kalaman da sukaita maimaita kawunan su a mafarkinta tare da hotunan su tamkar wanda aka kunna a Majigi haka a ynx ma da idanun ta ke a lumshe yayinda take zaune ta jingina bayanta da kujerar motar abinda ke faruwa kenan don hotunan abinda ya faru a Shekaru sha daya da suka wuce ke dawo mata

Muryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu

Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta

Muryar Nurse da aka kaita asibiti lkcn da take shirin fita hayyacinta bayan farfadowa daga sumanta na uku

Muryar Lami Yayar Lawan Babbar diyar Mai gari yayinda take baiwa Nurse din amsa

Da wasu muryoyi tare da hotunan mamallakan su a wancan lkcn da RAYUWAR ta tayi rugujewa ta Uku wanda faruwar shi ya cigaba da jagorantar duk wasu kalubale da matsaloli da ta fuskanta a bayanshi sannan ya kasance silar rugujewar RAYUWAR ta a karo na Hudu wanda yy silar faruwar halinda ta tsinci kanta a karo na biyar na rugujewar RAYUWAR tata kuma shine dai silar fadowanta cikin kaddararta ta ynx da take ciki

Tsayuwar motar ta dawo da ita duniyar da take ciki a ynx amma bata bude idanun ta ba sbd tasan Saleem dake gaban motar ne zai sauka tana jin fitarshi da kuma sanda yake fadin "Momcy tayi bacci D sai kun fito" da "Yauwa" Deela ta amsa Ram yaja motar sukayi gaba hakan ya bata damar tuna abinda ya janyo mata tuna abinda tun bayan wani lkc da ya shude baiwa kanta daman tunawa d kuma alkawarin d ta daukar wa Yayanta na cewar ba zata bari abinda ya wuce ya dameta b sedai abinda ya faru shine

A lkcn da Jirgin su ke shirin tashi sanda ta gama rungumar yaran yayinda idanun ta suka sauka kan karamin yaron da akullum ta gaza baiwa zuciarta hkr da dangana tare da fahimtar cewa yana cikin kaddararta da samuwar sa shine dalilin da ya sanya RAYUWAR ta tayi rugujewa ta farko duk da cewa tasan ko ta halin kaka hakan rubutaccen al'amari ne da yake tabbatacce a cikin littafin kaddararta dole sai ya faru kuma tasan bb laifin yaron ko na sakan daya amma laifin wasu majibantan shi ya shafi alakarta dashi a lkcn da kallon ta yakai kanshi ta hango wani irin kadaici da damuwa wanda yy kankanta ace ya sansu inda abinda ya riga ya faru bai faru ba sedai mai aukuwa ta auku a lkcn da Buwayi gagara misali ya nuna ikon shi da karfin mulkinsa tare da tabbatar da kalmar nan tashi ta ^KUN FA YAKUUN^ a kansu

Tunanin ta yakai sanda ta bude mishi hannuwan ta d yanda ya fado jikinta a guje daga inda yake rakube kamar marayan da ya rasa uwa ta san kuma kusan hakan ne don gurbin ido ba ido bane kalan Kukan da yaron ya saka na alhinin rabuwa da ita wanda ko Amaan da take baiwa dukkan kulawanta baiyi irinsa b duk da cewar shima yana hawayen

Wannan abin ne ya tsaya mata a rai da tun sanda ta juya musu baya tayi kokarin koreshi daga zuciarta har sanda ta iso kasar da duk wani abu da ta aiwatar a ranan al'amarin na makale cikin ranta har zuwa kwanciyarta duk da yadda taso yaki da zuciarta ku wajen ganin batayi tunani ba to tayi nasarar hakan sedai daga lkcn da bacci ya dauketa zuwa wasu awanni da suka biyo baya bccinta take hankali kwance kafin abinda tayi gudu ido bude ya faru a mafarkinta tamkar almara wanda shi yy sanadiyyar tashinta daga baccin bb shiri don tayi tunanin a ynx abin ke faruwa tun kuma tashinta dawa biyu kafin Sallar asuba bata sake rintsawa b har ladanin masallacin dake unguwar ya kirayi assalatu don unguwar akwai yawaitar musulmai wannan shine abinda ya hanata cin abinci jiya har sai da dare da ta daure zuciarta tai musu girki bb laifi kuma barkwancin Saleem, fadarsu da Deela da kuma shisshigin da yakewa daliban dake zazzaune kamarsu a wajen ya taimaka kwarai wajen lightening mood dinta har ta dan manta sannan baccin da ke idonta ya sanya tana kwanciya bata tuna komi b tayi baccin ta

Parking din Ram daidai inda zasuyi lecture yasa ta bude idanu godia suka masa bayan sun sauka ya ja motar yy gaba su kuma suka shige ajin

NIGERIA

Cikin sauri Husna ta gama Test din ba tare da ta fahimci mai ta rubuta b yayinda ita kam Salma tayi abinda ya dace kafin ta fito a kuma lkcn ne drivern Company yazo ya dauki su Afrah don maidasu gida

Janyo hanun Salma tayi zuwa cikin motan nata ta ce "ina jinki kin kuma san na kagara inji lbrn nan"

Salma ta gyara zama "kwantar d hankali 'yan mata ynx zakiji waye ABUBAKAR SADIQ IBRAHIM BUKAR kuma Mamallakin ASIB Group of Companies dake a fadin NIGERIA da kawaye

#Smarty💞

RAYUWAR FATIMA Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin