Suna zaune gaba daya har da BB suna breakfast bayan driver ya wuce da Little School BB ya kalle twins "ke Afrah yau bakuda lectures ne naga har wajen 9 kuna zaune?"
Afrah tace "yau daman Class daya zamu yi kuma Class Rep ya sanar Dr. Muhsad ba zai shigo ba yau" kafin BB yai magana Momma tace "ni wannan Malamin naku sunan shi kamar na mata yake min in kuka fada wlh" duk dariya suka kwashe dashi Afreen tace "Kai Momma to ai ba asalin sunan kenan ba ya gajarta duka sunayen na amma asalin sunan shine Muhammad Musa Muhammad shine ya harhaɗa suka bada Muhsad ɗin" gyada kai tayi alamun fahimta tace "koda naji nifa ince menene kuma Muhsad kamar mace" sukayi dariya gabadaya Papa yace "yaran zamani kenan da iyayi" su Afrah suka kalli juna suka kwashe da dariya Afreen tace "ai sai ma ka ganshi Papa wlh jin kai ne dashi sam bai kula kowa abinda ya kawo shi yakeyi yai ficewarsa" BB dake mikewa yace "daidai kenan ai in ya biye Students rainashi zasuyi musamman ma matan nan"
Kafin wani yai magana wayar Afreen ta shiga ringing alamar shigowar kira ganin Class Rep ne sai tayi gaggawar dauka tare da sallama ko me ya fada mata take fuskarta ta chanza ta sauke wayar tana mikewa ta dubi Afrah "sai ki taso ai wlh ɗan jaraban nan yai fixing 1hour lecture 30ms Test" tsaki Afrah tayi "gaskiya Allah ya shiga tsakanin mu da Mr. Jibo wlh" harara Momma ta watsa musu "malaman ku kukewa haka ta ina karatun naku zaiyi albarka" Afreen tace "Momma ynx ya zamuyi har fa Mal Ado ya koma munce mai bamuda aji yau" BB yace "Oya ku shirya in ajeku Ina da baƙi by 12:00" da sauri sukayi dakin su daman sunyi wanka so kaya kawai suka chanza suka fito nan sukaiwa iyayen sallama suka fita
Motar BB suka shige yayin da sauran motocin ke take musu baya wasu kuma suna gaba a haka suka isa har department dinsu Afrah dai dai inda zasuyi lecture sukayi parking yayinda idanun kafatanin daliban dake tare kofar hall din ya dawo kan motocin kowa nason ganin wanda zai fito ciki suma basu tsaya ɓata lokaci ba ganin ana shiga ciki sukayi saurin fitowa suna wa BB Allah ya tsare har sunyi kusa isa ya bude motar cikin hanzari ya fito yana kiran Afreen cikin zazzakar muryar nan tasa mai daukar hankalin mai sauraro cikin takun nan nasa mai cike da kuzari ya isa inda take ya mika mata wayarta da ta baro cikin motar sbd rudewa don ita akwai tsoro tasan in lecturern ya riga su shiga to sun rasa gwajin nan ta amshi wayar tana fadin "Thank you Habiby" ya kamo kafadun ta cikin kulawa yace "Ki nutsu Afreen kar kije ki rubuta shirme kinji ko" ta gyada kai ya mata murmushi sannan ya saketa ta wuce ya daga wa Afrah dake kofar hall din hannu sannan ya isa ga motar shi aka bude ya shige suka bar wajen
Banda Maa Shaa Allah babu abinda 'yan matan dake wajen suke ambata don sunga kyau wanda ya hadu da aji komi yaji ga Naira wanda ba sai an tambaya ba ma dukkan alamu sun tabbatar
"Kam bala'in nan jar uba" cewar wata budurwa dake cikin 'yan mata biyu dake zaune gefe a gaban hall din ta kusa da ita ta ɗago daga duba littafin da take tace "ke banza meye kike kiran mana bala'i ne a wajen nan" da sauri ta matso kusa da ita "ke Salama wai bakiga abinda idanuna suka gane min bane saurayin daya daga cikin wadannan tagwayen masu shegen rainin tsiya"
Wacce aka kira da Salma tace "to me yayi saurayin nata mayyar maza" haɗe rai tayi "ke wlh wannan ba kalan waɗanda nake bi bane wannan zazzafan ai na aure ne"
Salma ta kwashe da daria "kutumar U*a ynx Husna kece kike maganar aure ko kinsha wani abu da safen nan ne?" Husna ta harareta "ke kike maganar shan wani abu idan na sami guy dinnan ai wallahi na daina shan komi na daina duk wani iskanci a duniyar nan amma matsalar bansan ya zanyi inja hankalinsa daga kan waccar zabiyar ba"Salma tayi murmushi "kwantar da hankali ƙawata ba saurayinta bane wansu ne ke wai kina cikin Kano amma baki san C.E.O A.S.I.B group of companies ba?" da sauri Husna ta zaro idanu "kar kice min wannan haɗaɗɗen shine ya mallaki waɗannan kamfanonin kuma wai twins din dama arzikin su yakai har haka"
Salma tace "Hmm kedai ynx ki bari muyi Test din nan zan sanar dake wanene ya sace zuciyar ki a yau ba gobe ba Sister"
Zatayi magana suka hango tahowar malamin nasu don haka suka mike suka shiga cikin hall din da hanzariA/N : Please kuyi hakuri da gajartan wannan page din nayi typing da dadewa ne sai nazo na rasa wannan shafin shine dalilin da yasa wlh na rasa mai zan rubuta don yakai shekara sedai abinda na rubuta din shine ya faru a page na bayan amma na rasa meye da meye na rubuta (lol) so ayi manage....
#Smart💞

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...