Okay I know that it's been more than a year baku ji daga gareni ba hakan ya faru ne saboda wasu dalilai Alhamdulillah yanzu ina da more than 20 chapters a draft so duk lokacin da na samu dama zan muku updating idan har naga kuna da bukata kenan saboda rubutu idan ba'a comments kamar baida amfani ne.
A wannan yanayin dai ake kwanci tashi asaran mai rai yayinda kamar yanxu-ynx har diyar Ummy ta shekara takwas ita kuma Mama Indo nata diyar nada shekaru bakwai da watanni sedai Alhamdulillah ynx ana dan samun sauki don yarinyar takan fito tsakar gidan sabanin da kuma Imran kan daukota zuwa bangaren Ummy idan bb idanun Uwar suyi wasa da kannen nasu don a lkcn sun zama samari sbd Ahmad yana da shekaru goma Sha tara shi kuma Imran sha takwas wataran idan suka Imran ya dauko Husna Maman har dakin take shigowa ta dauketa tana kananun maganganu cewar ya kawo mata 'ya a karisa ta tunda tun tana ciki aka so ganin bayanta Allah baiyi ba ita dai Ummy sedai tayi murmushi bata ko tankawa tunda Allah yasan meke cikin zuciarta
Fatima tana primary 4 Ahmad kuma yana SS2 shi kuma Imran yana SS1 lkcn Husna ta warke sarai sbd Abbah kullum cikin sadaka yake da kuma sanyawa ana sauke Alkurani har dai Allah ya rabata da cutar da shi kadai yasan menene amman kuma bata son shiga cikin mutane dakyar dai bayan an saka ta Schl ta yarda take zama sbd tsoron Jama'a duk yadda Fatima ke sonta haka yarinyar bata kulata koda a makarantar ne sbd Mamanta ta hanata a cewarta sedai su rike wancan Salllamammen wato Imran tunda sun shanye sa amman shima ta kusa tayi maganin sa dan lkc kankani take jira
To fa a wannan lkcn ne kawar Hajia Indo Mai suna Karima Dollar ta bayyana bayan tsawon shekaru tara da barinta kasar baki daya tun kafin Auren Indo da Abbah kuma a wannan lkcn Kaddarar RAYUWAR wannan Ahali ta fara domin daga isowarta bata kwana ba saida ta nemi lbrn tsohuwar Aminiyarta Indo bayan kwana biyu kuwa ta fako gidan bayan gaisuwa ta nemi jin yadda akayi Indo ta kwashe komi tsaff ta sanar mata daria tayi da fadin "Kakar ki ta yanke saka Indo don kuwa nayi samuwa kwanan nan shiyasa ma kk ga na dawo 9ja" nan ta bata lbrn abinda ya rabata da gida Kamata akayi tana safarar yara da kuma muggan kwayoyi hakan yasa bayan an yanke mata hukunci taje gidan yari duk a garin Kaduna bayan kwanaki kadan aka fiddota sbd daman sunyi deal da masu gidanta cewar kar ta fadi sunansu su kuma sunyi alkawarin fitar da ita wannan yasa tana fitowa suka fitar da ita waje gaba daya tabar kasan ta koma kular musu da harkokinsu na waje na tsawon shekarun nan to fa a yawace yawacen ta ne ta sauka kasar China nan kuma tayi katari da wata kwararriyar bokanya da kawarta 'yar kasar Ghana ta mata bayanin tayi mata aiki Babba bayan ganin wannan aikin yaci ne yasanya itama tace ta raka ta nan ta gabatar mata bukatar ta na son komawa kasarta kuma wannan Bokanya ta tabbatar mata cewar taje bayan aiki ya kammala bb mai sake tunawa da komi a kanta
Kuma hakan akayi tazo ta sauka Airport a Kano ita da har shekarar da ta gabata ake nemanta Wanted sai bata ga koda kallon zargi wani ya mata ba har izuwa wannan ranar.Ba karamin farin ciki Indo tayi ba nan kuwa suka shirya zuwa China da kawarta nan da sati daya
Bayan ta tuntubi Abba ya kuma amince sbd a ynx shima kudi sun kara zama sosai koda ya tmby dalilin sai ta masa karya a cewarta sarin kaya zataje kasuwanci take son farawa tunda ynx Husna ta warke haka kuwa akayi sati na zagayowa suka chale to fa wannan ne Kaddara ta farko da ta fara watangaririya da RAYUWAR FATIMA.A ranar da Indo ta dawo komi ya canza a gidan don kuwa Ahmad sun dawo makaranta suka tarar da wani mummunan abu wato Abbah ne ke dukan Ummy matar da ko kallon banza basu taba ganin ya mata ba koda Ahmad da Imran suka nemi jin ba'asi sai Abbah ya hada dasu Indo dake ganin abinda ke faruwa ta shigo kallo daya taiwa Abbah ya bar abinda yake ta karisa ta janye hannun danta sannan tace "kana iya dukan uban kowa a gidan nan amman banda 'ya'ya na" ga mamakinsu kuwa hakuri ya bata ta juya ta fita daga ranan komi ya dawo sabo a gidan ba'a aikata komi saida Umarnin Indo a gidan Ahmad ga dan banzan zucia haka idan abu ya ishesa zai gaggaya mata magana idan Abbah ya dawo ya dakashi inda Fatima zatai ta kuka don ita sam bata saba ganin haka ba gidansu gidane dake cike sa soyayya da kulawa Abbanta na matukar kaunarta fiye ma da Ummy haka take gani amma ynx komi ya tabarbare Idan Ahmad ya tarda Ummy na Kuka zaita bata baki da rokon ta tafi gidansu tare da Fatima shi zai zauna a haka amman taki ita kuma Indo ta hana kowa zuwa gidan kama daga dangin Abbah da kuma na Ummy din daga ita sai kawayenta 'yan bariki shikam Imran da taso rabashi da Ahmad abu ya gagara sai tasa Abbah ya fiddashi karatu waje wannan ne mafarin barinshi kasar Nigeria da har yau yaki dawowa.
Duk wannan bai ishi Indo ba saida tasa Abbah ya cire su Ahmad a Private Schl ya maidasu ta gwamnati shima a cewarta sbd kada a zageshi ne a haka aka debi shekara guda suna cikin wannan kuncin Ummy kam ciwo take amma haka bai hana Abbah bugunta da zaran tayi motsin da bai masa ba a gidan Ahmad ya rasa yadda zaiyi gashi komi nasu ya dawo kanshi domin ko kayan abinci sai anyi wata uku kafin a jefesu da wanda bazai kai wata ko daya ba maganar sutura kuma babu shi balle makarantar Islamiyya dole shike fafutukar nemo musu idan ya tashi makaranta ya wuce Kasuwa yy dako a haka dai har wata rana da Allah ya kawo karshen abin Ahmad yazo ya tarar Abbah ya mata mummunan duka ta suma ga Fatima zaune gefenta sai kuka take tana kiranshi baiyi wata wata ba ya fita ya nemo taxi ya dauke Ummy duk da kasancewar shi dan shekaru sha tara amma yana da kirar karfi ya kuma sako Fatima a gaba suka nufi asibiti Bayan dogon bincike Likita ya nemi ganin wanda ya kawota Ahmad yace shine kallo ya kare masa yace ina mahaifinku budan bakin Ahmad yace "ya mutu" likita ya niisa sannan yace yana son ganin wani Babba Ahmad yasan number wan Ummy dake Zaune a Jos sbd yanda yake sonsu kullum cikin kiransu yake ta Landline din gidan duk da cewar Ummy ta hanashi fadar halin da suke ciki amma ynx kam dole zasu ji dan haka ya roki likitan cewar zai kira kawunshi ya kuwa bashi wayar dake aje a Office dinshi direct number Office din Uncle Musa ya kira bayan ya masa bayani a takaice cikin fillanci yace ya baiwa likitan wayan nan ya nemi Alfarmar da likitan yayi duk abinda ya dace kafin ya iso daga Jos ynx zai kamo hanya yace to.
Uncle Musa bai ko koma gida ba illa sako da ya tura wa matarshi na tafiar gaggawa ta sameshi amma In Sha Allah gobe zai dawo kafin ya kamo hanyar kano kai tsaye zuwa Asibitin ya wuce yana isa ya nemi ofishin likita Ahmad ne ya rakashi bayan sun gaisa sai likitan ya nemi Ahmad da ya fita ya fita amma bai bar kofar Office din ba abinda likitan ya sanar da Kawun shi ya matukar tada hankalin shi wato dai ciwon zucia ne ya kama Ummy amma tana stage din farko so in aka kiyaye tare da shan magunguna yadda suka dace to fa akwai yiwuwar zata sami lafia
Shi kanshi Uncle Musa hankalinsa ya tashi amma bb yanda ya iya haka ya fito jiki sanyaye ya sami Ahmad zaune akan bencin dake kofar dakin da aka kwnatar da Ummyn Fatima na gefenshi tayi bacci kanta na kwance bisa cinyarshi.Uncle ya tmby shi mai ke faruwa bai boye komi ba ya sanar dashi halin da suke ciki na tsawon shekara guda da wasu watannin ran Uncle ya baci sosai da rashin sanar dasu da Ummy tayi amma ba wannan bane lkcn bacin rai don hka washegari da safe yace Ahmad ya kamata suje gida suyi shirin makaranta ga Fatima yarinya ce bai kamata a barta ta zauna asibiti ba Ahmad yaso yaqi amma Uncle yamai jann ido don fa shi yana da wasa amma idan ya canza dole kaji tsoro da kanshi ya kaisu gidan bayan an bude musu gate sun shiga yace su shirya suzo ya saukesu daman already sun karya a hsptl Abbah dake fito daga bangaren Indo ne ya tsaya kallon su Indo ma da ta fito rike da hannun Husna dake cikin Uniform tayi turus ganinsu da mai mota ta kariso tana fadin "Mlm lafia kai kuma wanene da zaka shigo wa mutane cikin gida bb excuse kuma ina ka samo wadannan" bai ko kalli inda take ba yana ta tausar zuciar sa don tabbas idan ya kulasu sai ya hada daga ita har Abbah din ya musu duka Abbah ta kalla sai nan da nan ya daburce "Mal baka ji ne tana tmbyr ka daga ina kuma meye hadinka da yara na ina matata take" gaban Indo ya fadi wato dai har ynx da Maryama a zuciar sa to dole ayi ta ta kare tace "dangin mayu ana kinsu suna nacewa ni idan ina da zucia wlh bazan zauna inda ba'a sona ba" ynx kam ya kulu don haka ya dubi Ahmad yace "Kai jeka ka tattaro kayanku mu tafi ku bar musu gidan"
Indo ce ta nisa tana tunani tabbas zata so a tafi dasu ko dan su waala ita da 'ya'yanta amma in akayi hakan ribar me ta tsinta ai yadda adaa Ummy ke mata kallon kaskanci idan bata wulakanta rayuwar 'ya'yanta ba to fa bataci riba ba hakan yasa ta rada wa Abbah wata mgn nan da nan kuwa ya fara masifa yana zage zage cewar babu wanda ya isa ya daukar mai 'ya'ya ai basu gagaresa ba don haka shi zai kula da abunshi bai ko dubi cewar Uncle Musa ya girmeshi ba don ko Ummy kanwarsa ce ta kusan Hudu ma haka yaita fadan maganar banza da cin fuska gareshiShikam Uncle yakai makura don haka ya dubi Ahmad da nufin rarrashin su amma yaron sai yy murmushi tare da gyada mai kai alamar yaje bb komi yaja hannun kanwarshi suka koma cikin gida Uncle ya dubi Abbah "kaje indai zalunci ne zaka gani" bai kuma jira cewarsa ba ya shiga motarshi ya bar gidan asibiti yaje take a lkcn ya nemi sallama cewar zai maidata JUTH likitan ya sallammesu ya kuwa dauketa suka tafi ya kira wayar dake bangaren su Fatima ya sanar da Ahmad din tare da masa nasihohi bai damu b daman fatanshi kenan Ummy tabar wannan gidan
Wannan shine dalilin barin Ummy gidan Abbah...
JE LEEST
RAYUWAR FATIMA
Kort verhaalMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...