Barin su Airport direct gida suka dawo har shi BB din bayan sunci abinci ne yana kwance a doguwar kujera a falon Momma suna hirarrakin su da kannensa kira ya shigo wayar shi "subhanallah" yace don gaba daya ya manta sunyi da Ahmad zasu hadu a Company sallama yy daga daya bangaren Ya Ahmad ya amsa yana fadin"Boss to shanyar da kayi fa ta bushe kana iya zuwa ka nace" dafe kai yy yasan Ahmad daman da korafi "wlh na manta gaba daya munyi zamu hadu naxo gidan Momma kawai na kwanta" "ah lallai kam kana jin dadi Boss ynx ya za'ayi ne?" BB yace "bani minti biyar gani nan zuwa" Ya Ahmad yace "anya kuwa zan jiraka Boss" BB yace "to ka karaso mana kawai gidan daman ma ka dade baka zo ba" "a'a kam kawai ka fito ina jiranka" tsaki BB yy "kai fa baka d mutunci wlh Boss din naka kk rainawa hankali to wlh barin hadaka da Momma ince wai baza kazo gidanta b" yasan sarai BB zai rina don haka yace "rufa min asiri nikam gani nan zuwa" daria BB yy tare da katse wayar daman yasan haka ne kawai zaiwa Ahmad din ya yarda yazo gidan ba afi mintuna 6 ba kuwa sai gashi ya iso shi b bako bane sbd haka bai jira komi ba ya nufi falon Momma da sallamar shi BB dake zaune shi kadaj ya amsa yana fadin "Dan dunia chaa nike bazaka zo din ba ai" tabe baki yy tare da zama gefenshi "sannu dan lahira kuma kasan ba wajenka nazo b ai ko" Momma da fitowarta kenan ta ganshi ta rike baki "yau a gari inji mak'i bak'o? Baba na ashe kana Nigeria ka bata shiru" sosai kai Ahmad yy "aimin afuwa Momma wlh gaba daya ban samu shigowa garin bane" BB yace "kar ki yarda Sweetheart ko last month ya shigo kawai yaqi zuwa ne" galla mai harara Ahmad yy "wlh Momma karya yake rabo na da Kano tun auren Princess yau ma maganar makarantar ta ce ta kawo ni" Momma tace "rabu dashi nasan ai Uba bai kin diyarshi da kazo zaka shigo ne" BB yy daria a ransa yace don baki san yadda akai yazo din b ynx ma Ahmad yasan me dariar ke nufi shiyasa ma yaki tnka masa Momma tace "kai Baba na kanaji da takwarar nan tawa fa da gashi ban ma sami zuwa gidan nata b rabo na da ita tun tana kamar Little fa kasan muna Umarah akayi bikin nata su Habiby ne kawai da Salim sukaje daurin auren" "wlh bb komi Momma ai komai sai Allah y nufa" daga waya Momma tayi ta kira kitchen aka kawo wa Ahmad abinci yana ci suna hirar su har ya gama yace "Momma ina 'yan matan gidan ne naji shiru?" Tace "wlh sunyi Bacci" yace "takwara na fa?" Tace "ai dazu muka rakashi ya wuce makarantar" zai sake mgn BB y mike"kai tashi muje nasan Momma ba zata bari muyi abinda y kawo ka b da hirar ku da bata karewa" sallama Ahmad yy wa Momma suka fito zuwa wajen motar shi BB y dafa kafadar shi "Aboki na ni kuwa baka ganin mijin Princess bazai ji rashin dadi b yadda kace mgnr karatun ta kazo ai naga yaron baida matsala zai barta da kanshi tunda mahaifiyar sa ma Lecturer ce anan Bayero" murmushi kawai Ahmad yy "ynx dai ba wannan ba zamuyi mgn kanshi ya Madam da yaro na?" BB bai ja ba yace "lafia lau" tunda yasan Ahmad bayason zancen ne a ynx so zai barshi sai daga baya
"Ina fatan ynx dai bb wani matsala ko?" "Hmm kadai ayi sha'ani kawai wai na gari y cuci na kauye amman abin ba'a cewa komai Meenah ta kaini bango Ahmad ina dab da daukan mataki" cewar BB girgiza kai Ahmad yy "Aboki na sha'anin matan ynx fa sai hkr please kar kace zakayi wani abu mai muni a kanta nasan ka da zucia" BB yace "Hmm Ahmad don baka san abinda Meenah keyi bane shiyasa" "kana nufin banda wanda na sani a baya akwai wani kuma"BB yy murmushin takaici "wlh Aboki na indai wancan ne zan hkr in zauna d Meenah har karshen numfashi na kodan darajar son da nake mata da kuma yaron nan Khaleel amma abin ya zarta kaina ya koma kan 'yan uwana har ma dai mahaifiyata sbd Allah" jinjina kai Ahmad yy don yasan ankai inda Boss din nashi bazai iya jurewa b don shi shaida ne kan kalar kaunar d BB kewa ahalinshi "to ina da shawara Boss" already BB yasan maganar Ahmad bata wuce karin aure yace "amma dai Bro kasan banda ra'ayin tara mace fiye da daya ko" daria Ahmad yy "sbd kai raggon maza ne ko?" "Mtsw banxa kai da ba raggon b ai naga matan ka hudu" "Hhhh saurin me kk suna nan tafe ai" duka BB yakai mishi "amma da naci maka Uwa wlh yadda Madam ke kyautata maka ka isa mata kishiya ina raye ne" "to ubana idan naxo yi sai k hana ni" sannan y hade fuska cikin murya mai nuna alamun d gaske yake yace "Sadeeq ba mgnr wasa b sam bai kamata ka rabu d Meenah b kana sonta kuma itama haka sannan a da ba haka kuke zaune b sharrin kawaye ne da rashin Ilimi both addini d bokon sai kuma tarbiyar gidansu da sam bb tsawatar wa sa'annan in ma ka duba yaron nan Khaleel bai kamata ka raba shi d Babarsa b kasan illar hakan ba kuma kasan kalar wacce zaka dauko b ko zata iya rike maka shi da amana kasan matan yau so inaga kawai auren shine ya dace ka daure kayi tho ma banga abun ki wajen raya sunnah ba" murmushi BB yy irin wanda ya saba yi a duk sanda ya tuno ta aranshi kuma yace bana jin zata qi riqe min Da ganin yadda take son yara kuma tabbas in zata soni shirye nake d karin aure to amma ina zai fara neman ta ma ta hannuwa Ahmad yy "Hey! Malam yadai ina ta mgn? In gudun fitina kk kana da damar d zaka raba musu gida so banga abin tashin hnkl ba sam a nan"
Gyada kai yy "hakane na gode da shawarin ka Aboki zanyi tunani" nan suka tattauna mgnr Company kafin sukayi sallama Ahmad ya wuce gidan surukan shi don dauko iyalinsa sannan su dauko Ummy sai su wuce gidaShi kam BB ciki ya koma ya tarar d Momma dake zaune tana kallon Sunnah TV daukar remote yy ya rage volume bayan y zauna kusa d ita nan y kwashe duk yadda sukayi da Ahmad y fada mata tayi murmushi tabbas tasan Ahmad Aboki ne nagari shiyasa take matukar jin dadin tarayyarshi da Dan nata tace "tabbas Babana yy tunani mai kyau kuma hakan ne ya dace kayi Allah ya shige maka gaba" da Ameen ya amsa kafin ya mike yace mata zaije gida sai zuwa gobe don yau kam ya gaji Allah bamu Alheri tace ya tafi tun a hanya ya kira Ahmad y sanar mai ya amince da batun nan hakan kawai za'ayi daria Ahmad yy "Allah Habiby an zanta da Momma kenan tabi baya na" shima dariar yy yasan Ahmad in yaso tsokanar shi sai ya kirasa Habiby "ya akayi kasan da ita mukayi mgn?" BB ya tmby daga daya bangaren Ahmad yace "Haba Bukar ai tunda kace zakayi tunani nasan ka amince duba da yadda ada ko tanka min bakayi in nayi mk mgnr sedai nasan cewar d kayi zakayi tunani nasan shawara zakayi d Momma don nasan baka taba yanke hukunci ba tare da kayi mgn da ita ba kuma ina jin dadin hkan" murmushi BB yy tabbas Abokin nashi ya gama sanin halayyar shi kamar yadda shima zai iya bugan kirji ya fadi komi game da Ahmad din sallama sukayi da Ahmad yana fadin zaije ya dauki Ummy daga unguwa "amma kai munafuki ne guy din nan ynx daman da Ummy kuka zo shine baka sanar min b inje mu gaisa? To wlh zamu hadu be dan Air kawai kuma ina nan shigowa da daddare saina jibgeka gaban su Amrah tunda ka raina ni" daria sosai Ahmad keyi da kyar ya tsaida dariar yace "ai min afuwa Boss aradu ban kuma wa" BB ma dake tashi dariar don shi kanshi yasan in aka hadashi da Ahmad tatse shi zaiyi yace "kaci sa'a na yafe da yau kaga halin sojoji" Ahmad yace "wa ya fadi maka dan soja shima soja ne?" "Oho mka dai" ya kashe wayar don driving yake shi kuma Ahmad sai ya canza shawara jin BB zai zo sai ya fara daukar su Madam ya kaisu gida don ta hada musu dinner kafin ya tafi daukar Ummy
Bayan sallar Isha suna zaune sai ga sallamar su Little suka shigo falon zama sukayi suna gaida Madam don Ummy bata nan tana cikin daki Ahmad ya budewa Lil Pa hannu kowa yy mamaki duk d dadewar d yy bai ganshi b amma ya ganeshi don d gudu yaje yana fadin Daddy dagashi sama yy yana cewa "ina Abba B" yace "yna Mota" fita Ahmad yy suka shigo tare Ayman dake zaune shiru ya isa tare da rungumeshi yana fadin "Uncle" shafa kanshi yy "My Boy I missed u daman Daddy so yake ka tafi ban ganka b ko" murmushi kawai yaron yy nan BB ya zuba mishi idanu don gani yy yasan wannan murmushin amma bai tuna b bayan sun gaisa da Madam yaran ma suka gaidashi wato Amrah da Airah mika musu hannu yy alamun suzo a hankali suka taho wajensa don basu sanshi b wasa ya fara musu nan da nan suka sake dashi tmbyr su yy ina wansu Amrah da tafi surutu tace "dazu yy Kuka a gidan Big Daddy wai Mam ta tafi ta barshi kuma fa kato dashi inji Mama tace zamu masa daria ko Airah" gyada kai Airah tayi don itama bata cika hayaniya b wani lkcn kamar Ayman take baisan wace Mam din b amma tuna cewa kanwar Ahmad ta tafi mkrnt yau sai y fahimta daga murya yy yana fadin "Ummy na ki fito danki ya iso" Ummy da hayaniya yasa ta gane sune suka zo ta taso jin mgnr shi ta kariso tana daria "aa lallai wannan Dan da sai anxo garin su ake ganinsa ai saura kiris ayi fishi dashi kullum ka shigo gari sedai muji sakon gaisuwa" sauka yy kan kafet yana fadin "ayi hkr Ummun mu ai Uwa in tayi fushi d danta ya shiga tamanin wlh Ummy abubuwan ne sai hkr kullum na shiga Abuja a ranar nake juyowa sam banda lkcn kaina wlh" tayi murmushi "bb komi wlh ai kuna kokarin kira a waya ma" nan suka shiga gaisawa tana tmbyr shi mutan gida da Salim yace mata yana mkrnt su Afreen da suka sami Amrah sai surutu take zuba musu suma suka gaidata Ummy takai dubanta kan Ayman dake makale jikin BB tace "yau su miskili anga farin Uncle da aka ishemu da zancen shi hnkli ya kwanta ko" turo baki yy don baya son ta kira shi miskili sam BB da ya fahimta yy daria "Ummy gaskia kibar kiran Yarona miskili bamu yarda b" tayi murmushi "to ai gaskia aka fada yaro sai wanda yaga dama yake kulawa sbd miskilanci" "Ummy ni dai Babban mai gidan ki rabon da ingan shi tun yana rarrafe fa gashi naxo yy bacci" tace "to ba ga irinta nan b sbd rashin zuwan naka na tabbata su Airah ma basu sanka b shima Ayman sbd ganinka da yayi a Office ne shiyasa ma ya sanka" sosa kai yy "wlh kam dole mu gyara hali ai ynx dai ya kamata idan anyi hutu kai 3ple A ka kawo min yarana suyi hutu" Madam ce da Afrah ta tayata suka gama shirya table ta karaso take sanar dasu Food is ready kowa ya taso tare suka ci abinci za'a tashi Amaan Ummy tace a barshi kar ya cigaba da kunci da safe yaci abincin
Hira sosai sukayi sai wajejen goma suka musu sallama suka tafi Khaleel kam tuni yy bacci sai daukarsa Afreen tayi shikam Ayman da kyar aka rabashi da BB wai binsa zaiyi saida ya ce zaizo Abj ya daukesa da zaran anyi hutu kafin ya yarda Kyauta sosai yai musu gaba daya har da Zannuwa da ya kawo wa su Ummy da Madam yaran kuwa kayan wasa ne dasu Chocolate da sauran abubuwa
#Smarty
YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...