Duk sanda Maryam wacce Ahmad ke kira Ummy taje garin Rano sai suyi ta mata kananan maganganu amma sam bata tankawa sbd ita akwai hakuri kuma sam bata taba fadawa Abban Ahmad ba kamar yadda take kiran Alh Isma'il din a haka aka sake diban wasu shekaru biyun ya zama shekaru tara kenan a wannan karon kam mahaifiyar Abban da kanta ta mata masa kan lallai sai fa yy aure sbd ita ma tana bukatar jikoki da yawa
Abba yana matukar kaunar Iya wato mahifiyarsa sbd haka bb yadda ya iya ya amince mata akan Zaiyi din baisha wahala ba wajen sanar da Ummy tunda tare sukazo kuma bb ko kara a gabanta Iya ta bada wannan umarnin haka kuma daman itama Ummyn tasha fada masa yy auren yana ki don haka taji dadin yadda ya amince akan zaiyi din wala'alla zata sami saukin tsangwamar da danginsa ke mataHajia Indo Customer Abba ce a kasuwar Kwari ta dade tana nuna masa soyayya amma yana basarwa tamkar dai bai gani ba kuma har ynx bata gaji ba wajen bin sawun abokanshi amma yayi biris dasu
Iya taso Abba ya auri diyar kanwarta amma yaki sam sbd yasan tabbas ba sbd yana sane da cewar ba don Allah suke sonshi ba sai don abinda ya tara shi kuma bazaiyi wannan gangancin ba dalilin hakan yasa ya amince da soyayyar Indo ba tare da yasan cewar ita din ma Kura ce lullube da fatar akuya ba sbd Hajia Indo irin cikakkun 'yan duniyan nan ne ta taba aure tana kuma da da dan wajen shekaru shida sedai tun fitowar ta tafi Saudia Takari amma bata wani dade ba aka maidota Nigeria bayan kamata da akayi
Ba'a dauki wani dogon lkc ba akayi bikinsu da farko suna zamansu lfy har zuwa wani lkc musamman yadda Indo taga Ummy na son yaronta da tazo dashi mai suna Imran duk abinda taiwa Ahmad zata masa sedai tun sanda ta fahimci irin sonda Abba kewa Ummy ta fara tsanarta ana tafe dai har Indo ta gaza jurewa ta fara fiddo halayyarta ta asali amma kasantuwar Ummy mace mai hkr ya sanya sam bata tanka mata balle har ajisu tun tanayi a boye har dai Abba ya gano ta sbd wani rana da ta kama Ahmad tai masa bugun gaske sbd danta Imran ya zagesa shi kuma Ahmad baida hakuri Ummy ta hanasa amman saida ya bi yaron waje ya bugeshi
Wannan dalilin yasanya Abbah yai mata wankin babban bargo kan cewar bai aureta don bayason matar shi ba sbd haka bazai taba lamuntar aci mutuncinta ba ta kiyaye ba karamin zafi hakan yaiwa Indo ba ta kuma kuduri aniyar daukar mataki kwatsam sai ta fara laulayin ciki wannan yasa ta manta da batun wani kishi ma sbd laulayin bai mata da wasa sosai take shan wahala haka yasa aka samar mata mai aiki tunda Ummy taki ita da kanta take komi nata sai fa Ahmad dan shekaru Tara dake tayata dasu shara da wanke2 hatta Socks dinshi na Schl shi ke wankewa
Lbrn ciki yakai kunnen 'yan uwan Abbah zo kuga marna tamkar uwarsu ce zata haihu nan habaice2 suka karu kullum suna hanyar zuwa wai duba mai jiki suita fade2 itadai bata ko cewa ci kanku sedai ma tayi murmurshi don ta kanta take sbd itama dai a boye cikin ne da ita har na watanni bakwai kasancewarta doguwar mace kuma tana dan kiba kadan yasa sam ba'a gane ba kuma gata daman ma'abociyar saka Hijab ce (kunsan 'yan Bauchi ba daga baya ba wajen Hijabi LOL su Anty Binta Josawa maida wukar ga kuma Kanawa mutanen mu Hhhh) tun kafin Bikin Abbah tasan da cikin sedai tayi tunanin in ta fada za'ace bataso yy auren ne shiyasa tayi shiru da bakinta in ya fito sa gani kuma wani ikon Allah ko Abbah bai lura ba sbd sam sedai kayi tsammanin dan tumbi ne da ita tun da ta taba haihuwa ai kuma a 'yan watannin yana yawan fita sarin kaya Baya China ba Dubai shiyasa sam bai zauna ba
Alhamdulillah Ummy ta tsare mutuncinta na kasancewarta ta Babba kuma ko a shekaru ta girmewa Indo yasa bata kulata sam
Lkcn da cikin Indo yake wata na Biyu lkcn ne Ummy take watan haihuwarta don haka a sannan idan ka mata kallon kurell zaka fahimci tana dauke da ciki duk da yawan zama da Hijab da take faman yi
A ranar da Abbah ya dawo daga Dubai suna isowarshi kenan bayan yy wanka Ummy tazo tana hada mashi abinci binta yy da kallo take a gurin ya fahimci ciki take dashi bai ko saurari ruwan da take miki masa ba na wanke hannu ya kama hannunta ya zaunar yana mata kallon tuhuma murmushi tayi don daman tasan za'ayi hakan ganin irin kallon da yake mata yasa ta gyada masa kai Hamdala yy tare da fadada fara'arshi kafin yace "Maryama wata nawa?" Ta bude baki da shirin bashi amsa kenan bayanta yy mugun rikewa don dama tun daren jiya take jin yana dan tsunkulin ta kawai daurewa take
Cikin hanzari ta rike bayan tare da zamewa daga kujerar ta duka bisa kafet din dake shimfide a falon "Subhanallah lafia dai Maryam me ya faru?" Bayanta take nuna mai sai zufa dake kwarara ganin ta kasa mgn ya sanya ya daga ta tare da daukar Hijab dinta ya saka mata ya fito da ita zuwa mota cikin hanzari yaja suka nufi asibitin da suke ganin likita suna isa kuwa bayan an shigar da ita Doctor take sanar dashi Haihuwace baiyi tsammanin ma cikin yakai hakan ba duk da cewar Cikin Ahmad ma haka yake amma ana danganta hakan da na faari ne shiyasa komawa gida yy ya duba dakinta nan kuwa ya tarar da Jakar da ta hada kayan haihuwar ciki sbd daman Jibi EDD dinta ke cika da hanzari ya dauka ya koma hospital din yana isa kuwa basu wani Jima ba ta haifo diyarta Mace tunda bb matsala bayan 2hrs aka sallame su
Duk abinda ake Indo bata sani ba tana bangaren ta tana fama da kanta domin dai har ynx cikin na bata wahala bayan isowar su ne Ummy tace Ahmad yaje ya sanar mata shikam cikin murna ya tafi sbd matukar farin ciki yake Ummyn shi ta haifa mishi Lil Sis bai sameta falo ba sai mai aikinta dake ta goge-goge nan ya fada mata ta cewa Mama Ummyn sa ta haihu ya fito abinsa a kuma kofar bangaren nata yaci karo da Imran abunku da Yara sam ya manta basa shiri yace "yaro in fada maka Ummy na ta haihu na sami kanwa" Imran ma dai cikin Murna yace "Laa don Allah Ahmad da gaske nima Mama tace zata haifa min kani ai" Ahmad na daria ya kama hannun shi "wlh da gaske ne zo muje ma ka ganta" suka rankaya a guje kuwa har zuwa dakin Ummy inda Abbah ke zaune yana ta kiran 'yan uwa yana sanar musu ita kuma Ummy na zaune tana shan Tea direct bakin gadon suka isa suna leka fuskar yarinyar Imran yace "Laa wlh Ahmad kanwar ka fara zaka bani ita nima muyi wasa ko" "a'a ai kaima Mama zata haifa muku naku" cewar Ahmad kalar tausayi yy "Nidai wannan nake so ai Mama tace Kani zata aifa ni kuma wannan nake so" nan fa musu ya kaure Ummy suna musu daria ganin abin zai dawo musu fada ne yasa Ummy tace "kunga duk kuzo ai dukan ku Kanwar ku ce tare zaku dinga wasa ina zaku kawo mata alawa daga School ko" ahaka dai tai musu wayo suka hkr amman fa suna nanuke da ita bb inda suka fita
Mama Indo kuwa Mai aikinta na sanar da ita sakon Ummy taji gabanta ya fadi don tabbas da a tsaye take sai ta fadi tayi ta mamaki wato daman wannan uban Hijab din da matar ke sawa boyon ciki take amma lallai ta shammace ta sedai bb komi bari ta samu lafia zatai maganin munafurcin matar haka kuma tayi mirsisi taki zuwa sedai ta aika mai aikinta a cewarta bata da lafia da tazo ta sanar mata mace aka haifa ne hankalinta ya dan kwanta duk kuwa da cewar bata so Ummy ta sake haihuwa a gidan ba
Haka ma bangaren dangin Abbah da sukaji haihuwar sunyi mamaki a haka dai suka tattaro washegari suka taho cike da kunya sukayi barka suka koma
Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Abbah wato Fatima kuma bb wanda ya canza mata suna haka ake kiranta
Gaba daya dangin Abbah sunyi sanyi musamman yadda Mama Indo take nuna musu bakin hali duk da cewar har zuwa ynx bata samu lafia ba sbd haka suka fara ja baya da ita wasun su kam sun dawo daga rakiyar shedan har suka nemi gafararar Ummy kan cin mutuncin da sukai ta mata amma wasun su suna nan kan bakansu na kinta a cewarsu ta shanye musu dan uwa
Fatima ta taso cikin soyayya ta kowane bangare babu kamar Ahmad da Imran suna matukar sonta duk da Mama Indo tayi tayi ta rabashi dasu abu ya gagara don haka take faman cin Alwashin duk lkcn da ta haihu to ta Ummy ta kare domin kuwa ta gama zaman gidan sbd a ynx tana ganin lkc yy da zata karbi shawaran Kawarta da tun wancan lkcn ta bata kan nemo soyayyar Abbah ta karfi amma taki sbd bata bukatar ya mata son bogi amma ynx ta yadda bb soyayyar gaskia tunda zata iya rantsuwa Ummyn ma ta wannan hanyar tabi to kuwa su zuba su gani
MAN PROPOSED GOD DISPOSED (mutum yana nashi Allah na nashi ta Allah kuma itace gaskiar)
Domin kuwa a daidai lkcn da Mama Indo ke ganin burinta ya kusa cika a wannan dai lkcn ne Allah yayi ikonshi domin gashi dai ta haifi diyarta mace mai kyau Maa Sha Allah sedai kuma babu lafia kuma likitoci sunyi iyakar binciken su basu gano komi ba abu dai tun ana fama har suka bata shawarin ayi na gida su kuma cigaba da Addu'a don koda sunje waje ne bb abinda za'ayi sai fa cin kudinsu wannan yasanya hankalinta tashi kullum cikin kuka da fadin asiri akai mata bb mai kulata a gidan su kansu dangin Abban sun fita sabgarta sai suyi zuwa nawa gidan bb mai lekata to fa wannan ne yasa tayi sanyi har ta manta da mgnr zuwa wajen wani Boka don bata ko fita daga gidan don gani take kamar kowa na yi da ita ne sbd abinda ta haifa
#Smarty💞

BẠN ĐANG ĐỌC
RAYUWAR FATIMA
Truyện NgắnMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...