Motoci ne cike a kofar gidan su Amarya ana jiran fitowar ta bayan kawayen ta sun gama fitowa ne sai Aunties dinta guda biyu suka fito rike da ita cikin lullubi banda kuka babu abinda take sanadin rabuwa da gida
Bayan shigan amarya motan da aka tanada dominta ne aka dauki hanyar Gwammaja gidan iyayen Angon domin a chan zata kwana kafin gobe a kaita asalin gidan mijin da zasu zauna wanda ke Hotoro T/Boka.
Isar su keda wuya aka wuce da ita bangaren Surukar ta wato Uwar Mijin ta bayan 'yan gaishe gaishe na Manya suka damkata tare da tafiya suka barta da kawayen ta guda Hudu.
Mahaifiyar Angon ne ta matso tare da dago fuskar ta sannan ta yaye mayafin da aka rufe fuskar dashi don ganin amaryar Nurain da bata taba gani ba sbd sam taki zuwa wai kunya take ji kuma ita sam ba mai yin hoto bane wayar ma bata da babba sai fa yau Ummyn ta ta bata da za'a kawo ta nan, idanuwan ta na kasa sbd kunya yayin da Uwar Ango kirjinta yayi wani mugun bugawa take nan taji tsanar Amaryan mai tsanani ya shiga zuciyan ta, da sauri ta mike ta bar wurin zuwa cikin dakin ta.
Kanwar Maman shi ce ta musu jagora zuwa dakin da zasu kwana nan kuma aka gabatar musu abubuwan ci da sha, ita dai amarya tana kwance gefe sbd ciwon da kanta yake sanadin kukan da tun safe take yinshi a yau.
Waya Momy ta dauka ta danna kiran danta wato Angon har ya kusa katsewa kafin ya dauka yana fadin "Momy barka da dare "
"Kai Usman kana ina?"
"Ina Dakata gidan su Aliyu"
"To duk abinda ake ciki gobe da sassafe ina son ganinka" cewar Momy
Usman cikin tashin hankali yace "Momy ina fatan dai Lafiya ko?"
Momy ta amsa a dakile "Lafiyar kenan sai na ganka" ta kashe wayar ta...
A bangaren Amarya kuwa sam zuciyarta babu dadi haka take ji bawai don bata son auren ba sedai tun da aka shaida mata an daura auren take kuka don wani irin bugawa da zuciyarta keyi wanda bata taba jin irinsa ba sbd haka ma duk wadanda sukai mata nasiha ba wani fahimtar su take ba yayin da akasarin mutane sun dauka kukan rabuwa da gida take amma sam ita ba haka bane a wajenta domin babu wanda ya kaita farin cikin barin gidan da aka haifeta ta girma ciki wanda yake mallakin mahaifinta ta wani fannin kuma ya kasance tamkar kurkuku gareta
Cikin wadannan tunane²n ta gagara bacci don haka ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta tada sallah tayi yakai raka'a takwas kafin ciki sujjadar karshe ta fara jero addu'o'i tana fadin Ya ubangiji! Kai ka halicceni kaine kuma mafi sani kan halin da na tsinci kaina a rayuwa ya Allah! bana bakin ciki da dukkan jarabawar ka gareni sedai ina fata ka bani ikon cinyesu,ya Rabbi! duk abinda ke tunkaroni wanda yake sabanin alkhairi ya Allah ka kareni idan kuma kaddarata ne ya Allah ka saukaka mini shi ka bani ikon jurewa
Haka dai Fatima tayi ta jero addu'o'inta cikin sujjada kafin ta tashi bayan ta sallame ta janyo wayarta ta fara karanta suratul bakara a hankali gudun kar ta tashi kawayen nata daga bacci har wajajen karfe 2:00am kafin tayi addu'a ta kwanta
Washegari tun tashin ta sallar asuba taji zuciyarta tayi wasai bata jin wani faduwar gaba ko damuwa bata koma bacci ba don ba al'adarta bane hakan tayi karatun alqur'aan tare da azkar har wajen karfe bakwai na safe sauran kawayenta kam tuni suka koma baccin su

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...