Fadila tana isa gida batayi kasa a guiwa ba ta sanar da Ummanta cewar zata raka Fatima Abuja wajen Ummyn ta Umma tace "wanne irin Abuja kuma duka² wata uku da aure har ta fara fita?" Dee tadan yi yake "eh Umma ai Ya Nurain din yana Germany shiyasa ma yace taje kafin ya dawo zaman bazai mata dadi ba yaso ma ya kaita to amma tafiyarce tazo maza ta gaggawa"
Umma tace "Auu to shikenan daga nan ma kinyi wa ita Rukayyar Sallaman tafiya Schl sai kije har gidan Baffanki Hamid kuyi bankwana ko" cikin farinciki Dee ta rungume Umma tana daria Umma ta ture ta "ni kada ki karyani yauwa ke da Fatiman nan taki zamuga yadda za'a rabu ai" Dee ta mike tna fadin "Kika sani ko mu tafi tare ma" Umma tayi murmushi tace "mijin nata an fada miki wawa ne daga aure sai tafia" tace eh tana shigewa dakinta nan ta kira Tee ta sanar mata taji dadi sosai da har Umma ta amince sbd haka ta fara shiri don jibi zasu tafi kawai
Washe gari Tee ta shirya tsaf cikin atamfarta Riga da skirt ta dauko hijab dinta babba har kasa ta saka ta rufe falon bayan sun gaisa da Baba me gadi ta fice yana mamakin yau kuma Hajia ta fita amma sai ya danganta hakan da kila sbd bata dade bane sai yau zata fara fitan
Yau ce rana ta farko da ta fita tun kawota Unguwar sbd ita ba mai shige² bace tun ainahinta kuma bata son hayaniya shiyasa ko makota bata taba shiga ba ta layinsu babu wani hayaniya sosai kowa yana cikin gidanshi sai 'yan tsirarun matasa da baza'a rasa b dake zazzaune kofar shaguna ko majalisa haka sbd da yamma ne kanta a sunkuye take tafia yadda dai take iya ganin gabanta tayi tafia mai dan nisa kafin ta fito Bus stop inda ta tsaida dan sahu ta fada mishi inda zai kaita tare da shigewa dai² wani Babban waje ya tsaya by Babba ina nufin kayatacce kuma hadadde mai daukar idanu wanda a sama akwai Babban tambarin SMS wato Sufi Mart & Stores kudinsa ta bashi tare da nufar kofar wajen ta shige abinta b tare da tsayawa kauyanci ba alamar dai wajen ba bakonta bane tana tafia taji an jawo hijab dinta juyowa tayi da mamakin waye haka sai taga yaro ne Mamanshi ta rabashi a kafada tana duba abu murmushi tayi tare da kama hanun tana masa wasa don haka Allah yayita da son yara Mamar ta juyo tace "sannu baiwar Allah kema ya riko ki ko?" Tayi daria "wlh kila ya sanni ne" sukayi daria ta karbeshi tare da dagashi sama tana mishi wasa dakyar ya koma wajen babarshi bayan ta gama abinda take sukayi sallama ta wuce bb bata lkc ta gama kwasar duk abinda zata siya har ta kamo hanyar zuwa ta biya sai ta tuna da turare wajen turarukan ta nufa tana dubawa "Maa Shaa Allah " shine abinda ta furta a lkcn da ta ga abinda take nema hannunta takai dai dai kan wani kwalin turare da aka rubuta Dior Addict a kuma lkcn wani hanu ya iso kan turaren suka rike a tare saurin janyewa tayi tana fadin "sorry" tare da yin gaba bata ko kalleshi ba illa hanun nashi da ta gani fari tas mai dauke da wani kyakkyawan zoben azurfa da aka kawata samanshi da bakin dutse cikin sauri ta dauki Si Giorgio Armani tayi tafiarta zuwa wajen biya garin ciro ATM dinta jakarta ta fadi sakamakon bigeta da akayi ta duka ta dauka ta basu suka cire tare da packaging mata tayi gaba abinta dan sahun dai ta kara tsarewa ta shige ta nufi gidansu Fadeela a falo ta tarar da Umma da kanwarta da suke kira Anna bayan sun gaisa ta wuce dakin Dee itama kayanta take ta faman shiryawa sbd da ta dawo daga Abuja sai tafia India cikin farin ciki ta tarbeta nan da nan ta cika mata gabanta da kayan ciye² bata wani jima b suna hira ta mike bayan ta ajiyewa Umma tsarabar da tayo mata suka fito Dee zata rakata da yake Unguwarsu daya dasu Nurain nan Tee tace Deela ta rakata gidan zatai sallama wa Momy Dee tace "kut amma dai wlh Tee bakida zucia matar da ta rabaki da danta har akwai wani sauran mutunci tsakanin Ku?" Murmushi Teema tayi "sosai ma sbd ta wanin bangare malama ta ce, matar abokin Abbah sannan kuma My role model kuma har yau Nurain yana matsayin shi na abokina so Momyn shi tawa ce so muje ynx zamu fito" tsaki Deela tayi "banxa mai shegen kalan dangin tsiya" tayi daria "oho dai muje naji" tura get din gidan sukayi suka shiga sukai sallama kofar main falon gidan wata mace ta fito da alamu 'yar aiki ce bayan sun gaisa tace su shigo amma Hajia bata nan Tee tace to shikenan basai sun shiga ba kawai idan tazo ace Fatima ce diyar Alh. Ismail daga T/Boka zata gane kuma ace ta gode sai wata rana suka fito Dee tace "wlh naji dadi da bata nan sbd ynx gaba daya haushi take bani" Tee tace "haba Deela kinfa san matar nan bata da laifi kuma tun lkcn da abin ya faru na sanar dake ta gani kinga kenan ko kece hukuncin da zaki yanke kenan" "Mtsww Allah kiyaye hukunci bb bincike?" Cewar Fadeela "Hmm kema dai Deela zamanin nan fa ba'a gani bama daga wai² sai a yanke maka hukunci balle idanu sun gani" Tee ta fada dai² sanda take tsaida Dan sahu nan sukayi sallama ta wuce da fadin sai sun hadu a tasha da safeFatima ce zaune bayan tayi sallahr Isha tana tattara sauran abinda suka rage mata ta zazzage kayan da ta siyo a SUFI nan take kwalin Dior Addict ya fado tayi mmki kwarai na yadda akayi ya shiga kayanta tunda dai bata dauka ba sai tace may be daman ta dauka ne ta manta ta sake komawa don dai a gabanta aka sanya kayan a Leda kuma ita kadai ce tsaye balle tace kayan wasu ne ya shiga nata din don haka tayi farinciki sbd tasan Ya Ahmad dinta zaiji dadin kyautar don yana matukar son Dior Addict da zuwa ynx kamshin ya zauna a jikinsa sbd sabo da sakawa
Ta gama hada komi da zata bukata kafinta ta kwanta bacciWashegari karfe takwas Dee ta kirata tare da sanar da ita cewar ta shirya ita take jira kawai tace itama saura kiris in ta fito zata kirata sai su hadu tashar nan sukayi sallama number Nurain ta wanda ya taba kiranta bayan tafiarshi ta lalubo don dama ta ajiyeshi ne sbd wannan ranar saida ta gama ringing bai daga tana sauke wayar ya biyo kiran bayan sun gaisa cikin mutunta juna take sanar dashi yau zata wuce tare da mishi godia sosai baiji dadi ba yace "Haba Tee ya zakii min haka sai kuma yau ki sanar dani? gaskia baki kyauta ba amman jira ina zuwa" ya katse wayar shirinta ta karasa sai ga kiranshi ta daga "Assalaamu Alaikum" ya amsa tare da fadin "Yauwa Tee ga driver nan na turo zai kaiki Abujan sannan dan Allah ki bawa su Ummy hkr bb yadda na iya ne wlh bayan Momy bb wanda ya isa yaiwa rayuwata karan tsaye haka" murmushi tayi "Kar ka damu Ya Nurain haka Allah ya tsara banga laifinka ba har ma da ita Momyn sbd tana da dalili so ka daina bada hkr kaddarar mu ce hakan" hkr dai ya sake bata ita kuma tayi godia sukayi bankwana
Tana nan zaune driver ya iso Baba ne yai mata magana ta fito da kayanta yace "Oga ya kirani ynx cewar za'a cigaba da kawo min abinci ke zakiyi tafia ko?"
"Eh Baba" ta fada a takaice yace "to Allah ya tsare a dawo lafia" ta shige motar abinta driver ya gaidata nan ta fada mai zasu biya Gwammaja su dauki wata a kofar gidan suka tsaya taiwa Deela waya ta fito ganin mota tace "kikace mu hadu tasha dan tsiya ashe kaimu za'ayi" tace "wlh Nurain ne wai sedai drivern shi ya kaimu Abujan banson yawan jayayya shiyasa na hkr" drivern ya shigo bayan ya saka kayan Deela a bayan motar ya tadata suka kama hanya to Teema da Deela a sauka lafia.....
#Smarty💞
YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...