13

10 0 0
                                    

ABUBAKAR SADIQ IBRAHIM BUKAR wanda ya kasance Ɗa ga retired Chief of Air Staff Air Marshall Ibrahim Bukar Abdu kuma mamallakin dukkan kamfanonin A.S.I.B dake fadin Najeriya da kewaye don har a India yana da Kamfanoni mahaifinsa ɗane ga Sheikh Bukar Abdu Bamalli babban malamin addini da kasar mu da makotanta ke cin gajiyar ilimin sa da ma wasu daga cikin 'ya'yan shi  asalinsu mallawa ne karatu ya kawo Mahaifinsu Kano inda yake zaune a Dorayi tare da matansa guda biyu matar shi ta fari daga gida ya aurota wato auren dangi ta biyu kuma a nan Kano sedai ita bafulatanar Yola ce kasuwanci ya kawo Mahaifinta Kano a nan ya yaba da addinin Sheikh Bukar yai masa tayin aurenta babu ja ya karba hannu bibbiyu Mahaifiyar su Ibrahim wacce suke kira Maamu tana da yara bakwai maza hudu mata uku sai Ummu wato Amarya tana da yara hudu duka maza don haka ta dauko rukon diyar kanwarta daga Yola mai suna Fatima wacce suke kusan sa'anni da Autar gidan Amina don haka tare suka taso kuma suka zama tamkar 'yan biyu sbd shaƙuwar su.

Tun tasowar Ibrahim yake da sha'awar zama soja kuma cikin ikon Allah a karshe burin shi ya cika, sosai ake zaman lafiya a gidan Sheikh Bukar don haka koda Ibrahim ya taso da maganar son auren Fatima Maamu bata hana ba sai ma farin ciki da tayi don Fatima ai tarbiyyar suce bata haufi kan zamansu tare ba'a dauki wani lokaci ba akayi bikinsu suka tare haihuwar farko ta haifi namiji yaci sunan Sheikh Bukar wato Abubakar Sadiq bayan shi tayi ta haihuwa basu zauna ba sai bayan wani lokaci kafin ta haifi 'yan biyu suka ci sunan Maamu da Ummu ake kiransu Afreen da Afrah sai kuma Ahmad Saleem da Autar su Fatima.

Sadeeq wanda kannen suke kira da BB ma'ana Big Brother kyakkyawa ne ajin farko sannan fari sosai mai yawan barkwanci da son jama'a sannan kudin gidansu bai saka ya zama mai wulakanta na kasa dashi ba yana mutunta duk wani mai mutunci ya taso cikin gata da soyayyar iyaye da kakanni don ko cikin jikokin Sheikh Bukar shi na musamman ne a wajensa sannan kowa yasan ahalin Sheikh Bukar arziki gado sukai ba daga sama suka same shi b sbd haka kudi sam bai rufe musu ido ba..

Lokacin da Sadeeq ya tafi karatu tun a shekarar shi na farko ya fara kasuwanci don haka koda ya gama masters ya tara makudan kudade don ko wajen gina kamfanin shi na farko kadan ne mahaifinsa ya saka mai hannu kuma Allah ya sanya wa abin albarka yai ta ginuwa har izuwa yau dinnan da muke ciki

Sadeeq yana da mace daya mai suna Amina wacce suka hadu wajen bikin wani abokinsa har soyayya ta kullu sunyi aure a yanzu har suna da ɗa guda daya ma.

Salma ta ƙare labarin tana kallon Husna da tayi shiru jin cewar yana da mata har da ɗa da tai wani tunani kuma sai taga hakan ba matsalar ta bane ta gyara zama cikin motar tata tana kallon Salma "yanzu ke ina kika san duk wannan labarin?"

Salma tayi dariya "kin manta gidansu Mum a Ɗorayi yake kuma Kakata ƙawar Maamu ce sosai so watarana naje gidan muna kallon news aka nuna shi Sadeeq ɗin nake maganar yadda matashi kaman shi keda dukiya haka sai take bani tarihin gidansu don makota ne dasu"

Husna ta jinjina kai "to amma kina ganin ta ina zan fara ne wajen haɗuwa dashi ma?"

Salma tace "wannan ba matsala bane kinsan Aunty Seemah a Nasarawa G.R.A take ke in fact ma suna mutunci da matarshi so zamu san yadda zamuyi ko number shi mu samu kin gane ai...."

A haka suka gama ƙulla yadda komi zai kasance kafin sukayi sallama itama Salma ta shige tata motar kowacce ta nufi nasu gidan...

Husna tana isa gida ta zubda komi na hannun ta a falo ta kwanta kan 3-seater tana maida numfashi mahaifiyarta ta fito daga daki ta ganta nan kwance cikin sauri ta karaso ta zauna gefenta tare da kamo hannunta "me ya samu gimbiyata ne haka?" Husna ta yamutsa fuska "bari kawai Momy wlh gamo nayi da wani haɗaɗɗen gaye sedai yafi karfi na kuma yana da mata ma"
Momy ta rangada guɗa "kice nayi suruki kuma maganar matarsa ba matsala bane kinsan muna iya kaudata cikin sauki amma meyesa kk ce yafi karfin ki?"
Ta mike zaune "Momy babban me kudi ne fa har a kasashen waje yake da kamfanoni" Momy tayi dariya "wannan kice babban kamu kikayi to kwantar da hankali Autar Momy ki ƙaddara ma kin sameshi an gama"

"Allah Momy na?" Cewar Husna cikin zumudi "Kwarai kuwa kinsan muna da Nata'ala ai" sukayi dariya tare da tafawa tamkar kawaye sannan Husna ta mike tana tattare komatsan ta "barin watsa ruwa in Kira Yayana yau banji shi ba"
Momy ta tabe baki "kunfi kusa ni ban shiga safgar wannan baudadden yaron"
Dariya kawai Husna tayi don tasan Momyn sarai tana damuwa da Yayan nata kawai bata nunawa ne....


Note: Sorry masu karatu wato abinda ya faru da page 11 ashe harda 13 bansan cewa Wattpad pages biyu suka gogen ba sai daga baya kuyi hakuri da wannan shine kadai abinda na tuna na rubuta a fejin baya......

RAYUWAR FATIMA Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon