Suna shirin jansa ya zauna ne yace "wait ina Momma na?" Tabe baki sukayi Babbar tace "bata nan" kallon rashin fahimta yy musu "as in how ba naga motar ta b da zan shigo?" Dayar tce "eh tayi tafia ne kasan bata tafia d motar sedai driver y kaita a motar gida" a hankali y zauna kodai laifi yy wa Momma ta tafi bb sallama to amma da zai taso ai sunyi waya lafia qlau amman kuma tabbas bata nan coz in tana gidan nan zai dawo zama take t jirasa a main falon gidan sbd yadda take tsananin sonshi sam bata iya boye hakan gaban kowa take jikinsa yy sanyi yace "wai da gaske kuke ne?" ganin suna murmushi Babbar ta sake amsawa "wlh BB Momma bata bangaren nan" tsabar ya rude bai fahimci me taci b a ranshi y raya kodai ta fara fushi dashi ne kan laifin Meenah wanda shi sam baida masaniya inba da Little ta kirasa shekaran jiya b take sanar masa ganin yadda yy kalan tausayi ne yasa suka bushe d daria Auta tace "BB wlh Momma tana site din Papa zuraka suke" kallon su yy yana bata rai "ni kuka mayar abin tsokanar ku koh? Kema Little hada ke koh" kama kunne tayi "sorry BB wlh su sukace idan nayi mgn sai sun Zane ni idan bb kowa" hararta Namijin yy "sai kace ynz ba mgnr tayi b" tashi yy kamar yy fushi suka bisa suna "BB please kayi hkr bazamu sake b" ya musu banza yana nufar falon Papa ta corridor dake falon nasu inda direct ya hada site biyu din har lau dai suna biye dashi suka sake fadin "Please Habibyn Momma" murmushi yy yaran nan sunsan weak point nashi gashi sam baya iya fushi dasu sbd yadda yake matukar sonsu a rayuwar shi kuma daman mutum ne shi mai saukin kai zaka fahimci hakan idan kaga yadda yake mu'amala da na kasa dashi
Sallama sukayi gaba daya a kofan falon aka amsa yna rike da hannun Little suka shiga Papa zaune yana shan fruit salad yayinda Momma ke matsa masa kafarsa murmushi yayi shidai yana yaba kalar soyayyar da ke tsakanin iyayen nasu da har ynx ta kasa tsufa a kullum fatanshi shima ya sami irin wannan soyayyar daga macen da zai aura tun yna matashi sedai Allah bai nufeshi da hakan ba amma wai ance mai rai baya fidda tsammani wala'alla zai sami sauyi watarana
Hangame baki Momma tayi tana kallon su Afreen yadda suke mata daria ta mike da sauri tana fadin "amma yaran nan zakuci gidanku Habiby ashe kana hanya yau din?" Dariar su suke shi kuwa karasowa yy ya bata side hug "haba Sweetheart nafa sanar dake harda lkcn da zan sauka ma" ya fada yana sakinta tare da karisawa wajen Papa shima rungumarsa yy "wlh yaran nan cewa sukayi ka kirasu wai an sami matsala sai gobe kuma nayi trying wayarka bai tafi b" yy daria "nima da na iso cemin sukayi wai kinyi tafia" rankwashin Afrah dake kusa da ita tayi "ai kun kyauta gashi ban samar masa komai naci b sbd iya shegen ku" Papa yy daria "nikam naji dadi ko bb komai an kula dani da ynx ta hana kanta sakat da aiyuka nima bazan samu ganinta b mutumin da keda gidanshi a tsaya masa girki baku kyautawa Amina yaci naku yaje ya kasa cin nata" yake kawai yy don yasan ko yaje bb abinda zai taras sai Fara da mai ko taliya aikin kenan tamkar gidan matsiyaci yasan Fara da mai anayinta ne don marmari to amma gidanshi kullum haka ake fama da wannan mai da yajin kamar ibada suma yaran dake sun san kan gidan basuyi mgn ba bayan sun gaisa da iyayenshi ne ya dubi kannensa yace "Papa daman na samarwa Saleem Admission ne a Uni of Delhi da naje "
"Maa Sha Allah!" Papa ya fada yayinda shi kuma Saleem yake washe baki like gonar auduga sbd farin ciki Momma ma cewa tayi "Allah ya sa Albarka ya kuma bada sa'a" da Ameen suka amsa yayinda Little ke turo baki "Ya dai Autar mu?" cewar Saleem dake zaune kusa d ita "BB to ni kuma ina zanje ne?" Daria yy "ai ke mutumiyas kina Korea ba kina son kije kiga Kim Hyun Joong ba? to tare ma zamuje" washe bki tayi sosai tana murna Afreen tace "mudai shikenan mun kare a 9ja koh BB" cewa yy "ai in kunga kunbar gidan nan to aure ne haka kawai ku tafi kubar min Momma ita kadai" gwalo Saleem ya musu yana daria nan yayan nasu ya mike tare d musu sallama kan zai isa gidan ya hutu sai zuwa dare kuma Papa ne yace "kayi zamanka sai gobe kawai Baba" da toh ya amsa suka fita tareda kannensa har ma da Momma din a main falon yake cewa "Sweetheart akwai maganar d zamuyi amma sai da safe idan naxo" "to shikenan Habiby Allah ya kaimu ka gaida ita Aminar da mai katon kan nan" Saleem yace "nidai yaro na baida katon kai kuma dadin abin ma mai sunan Mijin ki ne" daria duka sukayi ta juya su kuma suka rakasa har bakin mota yana rike da hanun Little da yaxo shiga motan ne yace "Mama na ko zamu tafi tare ne?" Tayi murmushi tare da girgiza kai "a'a sai kazo kawai ka gaida Little Pa" "to zaiji Mum dinsa fa?" Juyawa tayi tana tafia tare da masa Bye suma sauran suka daga masa hannu take motocinsa suka fice daga mansion din suka nufi gidansa dake nan still cikin Nassarawan amma layinsu ba daya da gidansu baAbuja
Bayan Sallar Isha'ee ne Fatima ta shigo falon Ya Ahmad wanda yace yana nemanta lkcn da suke dinner kusa da kafafun shi ta zauna tana fadin "Daddy ganin" (da yike a times hka take kiransa wato tana bin bakin 'ya'yan shi" sauke ajiyar zucia yy daga kallon ta dayake tun shigowarta ya sake dago idanu ya kalleta kafin ya fara magana "Princess kalleni nan meke damunki? domin tun zuwanki na fahimci kina da damuwa what happened? Girgiza kai tayi gabanta na faduwa daman karshen alewa kasa " Bb komai Yaya" yy murmushi "Princess kinsan dai cewar haihuwarki ne kawai banyi ba amman ko Ummy da take mahaifiyar mu bata fini saninki ba da fahimtarki in kina cikin damuwa ko akasin haka so feel free to talk kinji" a hankali ta dago tana kallon sa gyada mata kai yy alamar go ahead nan taji wani kwarin guiwa aiko batayi kasa a guiwa ba ta kwashe komi ta fada masa sosai ranshi ya baci ya fara mata fadar meysa bata taho tun a ranar ba me ta zauna musu a gida kamar wata marar galihu tace "Yaya bawai haka bane na tabbata halinda Ummy zata shiga a lkcn sai yafi wanda zata shiga ynx shine dalilin da yasa nabi abin a haka sannan maganar mutane m bazaiyi yawa b kan cewa an saketa tun ranar aure gara ace wata uku da auren" "Hmm Princess kina tunanin ynx ma kin tsira ne daga bakin jama'a? ai dan Adam ba'a iyar masa kedai kawai ki nemi yardar Allah" ta jinjina kai ya dubeta cike da tausayawa "sannu Princess kekam kinga RAYUWA sedai ki godewa Allah sannan kar kisa wata damuwa a ranki Allah yasan dalilin jarabtarki kuma muna fata ya baki ikon cinyewa" da Ameen ta amsa tare da masa godia yace "kar ki damu zan sami Ummy ynx zamuyi maganar kije ki kwanta abinki" tare suka fito ta shige dakin ta inda ta sami Deela dasu Amaan suna tadi yayinda takai dubanta kan Ayman wanda ke zaune gefe daya kamar maraya yaron sam baida hayaniya kamar na sauran 'yan uwansa karasowa tayi tana fadin "Jelana ashe kana nan kana jirana" zumburo baki yy irin na sakaltattun yara "Kema har dake ko Mam" Dee da twins suka fara musu daria tace "manta dasu My Dear zo muyi firar mu kaji"
Sallama Ya Ahmad yy a kofar dakin Ummy ta amsa tare da fadin "Bismillah shigo" shiga yy y zauna gefen ta yana fadin "Ummy sannu da hutawa" tace "Yauwa y dai lafia koh" yace "Lafia lau wata magna ce nazo da ita amma ina rokon ki Ummy ki taimakeni ki kwantar d hankalin ki ba komi bane wannan akan halin da aka shiga a farko don Allah kin dai san lafiarki yafi komi ko" tayi murmushi "Ahmad kenan wane dare ne jemage bai gni ba ai sedai na mutuwarshi kawai kar kaji komai fada min menene?" Nan ya gyara zama ya kwashe komai ya fada mata murmushi mai ciwo tayi sannan tace "Alhamdulillah! Allah shine abin godia ko a bakin kura kk dole ka gode masa Allah mungode da wannan jrabawa daki² da muke gani kasa hakan shine mafi Alkhairi" "Ameen" ya amsa mata tayi shiru sai chan tace "Allah sarki wato RAYUWAR FATIMA tana fuskantar abubuwa daban² cikin kananan shekarunta amma ya za'ayi haka tata Kaddarar take sedai muyi fatan Alheri da addu'ar samun chanji nan gaba" nan dai suka cigaba da tattaunawa har zuwa wani lkc ya mata saida safe ya wuce.....Kano
Zaune suke a falon su Uku biyu kansu daya sai kuma dayar wacce ta zartasu a shekaru tana zaune ansha kwalliya ta kafa daure wane mai shirin zuwa gidan biki yayi sallama ya shigo mikewa sukayi su duka mai kwalliyar ce ta karasa ta amshi Briefcase din dake hanunshi sauran kuma bayan sun gaidashi suka wuce cikin dakin dake nan falon Kama hanunshi tayi suka wuce Upstairs sai wani rangwada take suna shiga ta rungumeshi tare da fadin "nayi kewar ka Abban Khaleel" shafa gefen fuskarta yy "nima haka Meena ta" zama yy bakin gado yana cire maballan rigarshi tare da zare rigan har ma da wandon ya zauna da singlet & boxers yana fadin "Oh na gaji wlh Meenah taimakeni ki hadan ruwa in dan watsa" to tace taje ta hada ya shiga bayan ya fito ne ya saka wata Sleeveless Riga da wando 3quater ya fito falon saman ya sameta zaune tana sana'ar tata ta chatting zama yy a gefenta yace "ya me zan samu ne ina tare da yunwa fa" tashi tayi tana fadin "barin kawo maka" a ranta tace ba'a biya gidan mayyar ba kenan a haka ta debo abincin ta kawo mai ko arzikin a daura a serving tray bb sai Filet din ziqau da aka riko Allah yy dai an rufe ma da wani filet din budewa yy farar shinkafa ce da miya bb ko arzikin coleslaw wai ita a hakan tayi girkin tarban Maigida wanda ya taso daga wata uwa duniyar bb yadda ya iya tunda yana jin yunwa kuma shi Indai ba wani garin yaje ba sam baison siye²n abinci dinnan ya fara ci a ranshi yana fadin gaskia yaran chan sun jamin da ynx na kwashi girkin Momma mai dadi wlh sai da ya kusan cinye abincin kafin ya ajiye yana mikewa zuwa fridge din dake falon ya dauko ruwa yasha tare d zaran tissue din dake kan fridge din cikin kwali ya goge bkinsa ya saka cikin waste bin "Ina Little Pa ne ban ganshi ba?" Ya tambaya yana bude wayarsa "Auu wai Khaleel Umma ce dazu da tazo ta daukesa wai zasu tafi unguwa anjima zata dawo dashi" kai kawai ya gyada cikin takaici baice komi b yace mata zai kwanta yadan huta zuwa anjima da "a fito lfy" ta amsa masa tare da komawa falon kasa inda ta tarar da kannenta suna kallo.....
#Smarty💞

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...