Tun wayewar garin yau Fatima ke ta shiri sbd zumudin tafiar amma karfe tara nayi taji ta fara kewan gida da 'yan uwanta don haka ta zauna tayi shiru a falon tana binsu da ido shima Amaan zama yazo yy a gefenta "ynx Mam tafia zakiyi ki bari?" Ganin ya shiga damuwa sai ta kauda nata ta shafa kanshi "Boy dina kar k damu zamuyi waya fa ga Video call nan ai bazakayi missing dina sosai ba kaji Sweetie" "amma ai zaki zo hutu ko?" Tayi murmushi "yeah In Sha Allahu zan zo kar kaji komi kuma in anyi muku hutun Schl zance Daddy ya kawo ka" "Mam ni kadai kuma banda Ayman kenan" dubanta takai kanshi yy shiru yana wasa da kofin shayin d tuntuni aka basu amma har 'yan uwansa sun gama shi bai ko taba ba zatayi mgn kenan Madam tazo ta karbe kofin ta fara bashi a baki nan ma kadan yasha ya kauda kai wai y koshi Ya Ahmad dake kallon duk abinda yakeyi ne yace "kai Ayman kayi maza kasha ko kuma baka binmu Airport din nan" jin haka yy saurin amsan kofin ya shanye lkcn goma saura nan suka fito gaba dayansu har Ummy suka nufi filin jirgin
"Nikam Saleem saurin me kk ne abinda sai Sha daya ku tashi ma" Saleem da har yakai akwatin shi mota yace "Momma wlh BB yace goma ta mana a Airport din nan kinsan kuma baison jira ko" "to ni alwala nayi fa zanyi walaha" Afrah tace "Momma please idan munje kyayi a chan in ba so kk BB yayi fada ba" daman sanye take d Hijab dinta don haka ta mike suka fito don masa rakiya Papa kam baya nan yana Abuja zasuyi meeting a fadar shugaban kasa
Aminu Kano International Airport
Ganin sun gama komai sai jiran lkcn tashi yy sai Teema tace bari taje tayi sallar walaha ita kam Ummy tun a gida tayi nata masallacin dake Airport din ta nufa don yin sallarta
Suna isowa Saleem ya kira BB a waya wanda ke shiryawa cikin sauri sbd bacci da ya kwashe shi bai tashi b sai 9:30am daukar wayar yy "BB kana ta ina ne bamu ga motar k ba fa"
"Leym ku gama abinda y kamata ina hanya" to kawai yace ya sauke wayar yana fadawa Momma abinda yyn nasu yace ta bude motar t fita tana fadin ku karasa ni barinyi Sallah kafin ya iso kawai ta nufi masallacin abinta
Yana gama waya da Saleem ya dauki agogon shi yana daurawa tazo ta tsaya a gabanshi bb ko gaisuwa b komi ta fara "ni idan zaka dawo ka taho min da Khaleel ko kasa drivern gidan chan ya kawoshi in kaje" bai ko kalleta ba yace "sbd a daji yake ai dole ayi sammakon dauko shi to ba gidan zanje ba Airport zani Saleem zai wuce schl" Kam bala'ee mkrnt wato zai kai kaninsa wata kasar ta raya a zuciarta "eh da yike shi kanin ka ne ai ka samar masa amman nan nace maka Imran nason schl kace ba'a samu b ai ko sbd son kai ko kuma kana tunanin kudin d zaka kashe ne oho" ya juyo da kallon shi gareta "Imran Canada yace yana so kuma ni bansan kowa a chan b shi kuma Saleem India zashi kuma da kk maganar kudi to ko Saleem ba nine zan biya mai krt ba kinsan dai Ubansa ba matsiyaci bane arzikin d yake dashi ko jikokinsa ba zasuyi talauci ba nd daman ina d niyyar nemar wa Imran din kwanan nan amma kinja masa wlh tunda baki da tunani har ni kk maganar ina kyashin kashewa kanin ki kudi na baiwa wadan d ma ban sani b balle shi to kije rashin mutuncin ki ya kaishi kuma Khaleel bazai dawo b in kk yi wasa wlh sai in maidashi gidan na har abada muga ta tsiya don naga so kk ki kaini bango"
Batayi tsammanin zai mata masifa haka b don ta sanshi akwai hkr amma taji zafin mgnrsa ta cewa Ubansu ba matsiyaci bane wato nata uban ne matsiyacin kenan bata daddara ba ta sake fadin "da yake 'yan uwanka basu kaunata basu daukeni d muhimmanci ba shine ko sallama bazai min ba ko dayike kaima ai baka mutunta ni b tunda ko fada min ka kasa yi sai ynx nake ji" kallon banza ya watsa mata "da shike ga uwarsu dole yaxo miki sallama mana ki bashi abinda Allah bai bashi ba bayaga rashin mutuncin da kk musu an fada miki bansan duk abinda kk bane kam? To kedai ki kula kafin ki kaini bango in yanke hukunci karfi da yaji kike son rabani da 'yan uwana bayan ke kullum gidan nan cike yake da naki 'yan uwan" tayi mamaki ynda yake sauke maganganu daman wato haka yake ita tun zamnsu dashi bai taba fita mata a giya irin na yau ba daman ance mai hakuri bai iya fushi b amma tasan uwar nan tasa ce zata kitsa masa duk wadannan maganganu lallai in batayi d gaske ba zasu rabata dashi kamar ynda kawarta Umayma ta fada "to ynx kuma gori kk min kenan don 'yan uwana suna zuwa gidanka?" Bai bata amsa ba ganin tana neman bata masa lkc ya raba ta gefenta ya wuce yayi ficewarsa kwafa tayi tana cewa "ai zaka dawo ne" t tafi dakinta don daukar waya ta kira Babarta ta sanar mata ....
Airport
Tana gama addu'ointa ta mike sai taga waya a gefenta tabbas bb tantama na matar d ta fita ynx ne don ita kadai ta samu cikin masallacin don haka ta dauka cikin sauri ta fita tana dubata ba tasan fuskarta b amma zata gane kalar Hijab dinta hagota tayi ta danyi nisa sai ta kara sauri har ta iskota "sannu Mama nace ko wannan wayar taki ce?" Juyowa tayi tare da zaro idanu "wlh tawa ce halan a hanya na yar ko 'yan mata?" "A'a inda kk yi Sallah kk barota" karba tayi tana fadin "amma nagode kinji yarinya Allah ya miki albarka" da kallo tabi zoben hanun matan tabbas ta taba ganin zobe makamancin wannan amma a ina ne ? Mgnr Momma ya ankarar da ita murmushi tayi tare da fadin "Amin Mama" suka cigaba da tafia Momma tace "tafia zakiyi ne ko kema rakiya kk yi?" "A'a Mama zan tafi mkrnt ne" Momma tace "to Allah ya bada sa'a nima yaro na na rako zai tafi mkrnt India" tayi murmushi "nima chan zanje ai Mama" kafin ta bata amsa suka karaso inda matafiya ke jira Khaleel da y fara ganin su ne ya gane Teema da yake jiya suka hadu nan ya fara taba Little yana nuna mata "Li Aunty Mamma" itama take ta gane ta ta cewa su Afreen"Laaa! kunga Momma tare da Auntyn nan ta jiya a SUFI" duk suka nufosu Afreen iyayen mgn tace "Laa Momma ina kk samota ko daman kin santa ne?" Itama ta ganesu Khaleel kuwa har ya isa kusa d ita ta dagashi tana cewa "Hello Handsome" daria kawai yake mata Momma tace "wlh wayata na manta cikin masallaci shine ta biyoni dashi ku ina kuka santa?" Saleem yace "gaskia kina d kirki wlh Momma ai ita ce jiya muke baki lbr ta kawo mana Little Pa a SUFI" Momma ta jinjina kai lallai yarinyar nada hankali "wanne schl zakije ne India kuma wanne garin?" "Uni of Delhi ne Mama ni da Sister na" Little tace "Wlh Broda ma nan zaije Aunty" tayi murmushi "Allah sarki ashe hanyar mu daya" yace "wlh kam kinga ma ni Momma nayi kawa tun daga nan kenan" sukayi daria a ranta tace ji yaron nan wai nice kawarsa ba ma Aunty b zatayi mgn sallamar Deela ya katse ta "ke Princess daga zuwa Sallah to Yaya na kira kizo an fara shiga" sanna ta gaida Momma sallama ta musu Momma tace "diyata baki fada min sunan ki ba ko Princess din ne?" tayi daria "a'a Mama Fatima suna na" "wai³ ashe takwara ta ce to Allah ya kiyaye mungode sosai" hannu ta daga musu tace wa Khaleel "Bye Handsome" shima ya daga mata yana cewa "Babye" Saleem yace "sai mun hadu karamar Momma" kai ta gyada kawai suka tafi Deela tana gaba kyan Familyn a haka suka iso ta gaida Umman Deela dake magana d Ummy kiransu akayi zasu shiga jirgin ta rungume kowa har Ya Ahmad kamar kar ta wuce take ji Ayman dake jikin Ummy ya lafe ta kalla tsoro yake ji ya kasa zuwa wajenta bude masa hanunta tayi da gudu ya shige jikinta tare d fashewa da kuka sunkai minti guda a haka kafin ta sake shi tayi saurin juyawa tana share hawaye ta nufi shiga jirgin Deela tabi bayanta Ya Ahmad ne ya riko Ayman yana lallashi suka nufi mota don tafia shikam sai waiwayawa yake shima dai Amaan kukan yake Ummy na masa tsiya da katon banza mai kuka gaban kannenshi
Suna barin wajen ya iso hakuri ya baiwa Momma na rashin zuwanshi da wuri sannan kannen suka gaida shi saida kusan kowa ya gama shiga jirgin kafin Saleem ma ya musu sallama ya tafi suna daga mishi hannu da fadin da sunyi hutu BB zai kawosu wajenshi
Allah sarki rabuwa da 'yan uwa ba dadi duk sai jikinsu yy sanyi basu bar Airport din ba saida jirgin su ya tashi
To a sauka lafia mutan India a gaida min Salman Khaan Zarah da fatan basu tafi sun barki b (Lol)
#Smarty💞

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...