Kasancewar kananan kaya ne a jikinta rigan iyakar sa guiwa sai dogon wando yasa ta dauko babban Hijab har kasa ta saka tayi kyau abinta ta fito falon nan ta samu suma sun shirya ita ake jira dan haka tna fitowa Ya Ahmad yace su tafi ta dubi Madam tace "Aunty banda ke ne?nasan Ummy kam dama bata zuwa" girgiza kai tayi "nikam wlh a gajiye nake a dawo lafia" suka fice abinsu Yaya yaja mota suka fito yana tmbyarta ina sukayi ko Ado Bayero Mall tace "a'a Yaya ga SUFI nan kusa basai munje chan ba ai" yace "Okay" suka nufi SMS
Driving yake yi a nutse sbd yau bb Convoy din ko driver bai fito dashi b don guards dinshi sun tashi aiki coz da sun dawo daga office yake sallamarsu kowa yaje ya huta in ka dauke driver dake zaune a BQ din gidanshi
Little ne tace "BB Shoprite zamuje ne?" Yace "a'a Little Sis kinsan dai bana zuwa chan sbd y cika Jama'a so SUFI Mart zamu" to kawai tace yaci gaba d tuki har suka iso fitowa sukayi Afrah, Afreen,Little sai Saleem dake dauke da Khaleel sbd dare ne duk da cewa wajen tarwal yake da haske kamar rana suka shiga ma'aikatan gurin sai gaidashi suke da alamu regular customer ne shi dinKowa yaja kwando sukayi ciki yayinda shi kuma yake dan zagaya gurin yana dan dudduba wa Meenah wasu abubuwa da yasan tana so (Bawan Allah!) Saleem ne yaga wani agogon da suka gani ranan wajen wani Ango sun raka Momma bikin dan kawarta ba shi dake namiji ba har su Afrah sunce agogon ya burgesu don haka yana gani ya kirasu suka zo Afreen tana gani "Wow!!" Tayi exclaiming sbd batayi tsammanin za'a ganshi nan b coz sun duba Ado Bayero ranan d suka fita wai Saleem zai siya amman bb sbd tsabar zumudi har baisan ya ajiye Khaleel ba suna ta surutu da duba sauran designs din
Tana tsaye tana daukan Body spray taga yaro ya taho tsayuwa tayi tana kallonshi sbd yadda Allah ya daura mata son yara ballantana wannan da ya kasance kyakkyawa kuma fari sol zuwa yy ya rike Hijab dinta yana fadin "Aunty" dukawa tayi ta dauko shi tana tambayarshi "Ina Maman ka?" Bayanshi yake nuna mata yana cewa "Uncle Aunty Li chan" ta gane me yake nufi don haka tayi mgn da Aman dake bayanta "Boy zo muje mu duba wanda suka zo d yaron nan" ta hanyar d ya fito suka bi tana daga shi yana daria tare da bata lbrn da wani ta gane wani kuma sai a hankali (kunsan irin yaran nan na masu kudi musamman wadan da ake kullesu gida basu cika wayo b gashi dai shekarun shi uku amma bai wani iya mgn sosai b) su Saleem da saida suka gama abinda sukeyi suka lura bb yaron ne suka taho dubashi suka hango ta rike dashi don haka suka iso wajen da sauri shima yana ganinsu ya fara musu daria yana nuna mata su tace "ka sansu ne?" Ya gyada kai tare da cewa "Uncle da Anty Li" murmushi ta musu Afreen iyayen surutu tace "wayyo mungode Sister yau da mun hadu da BB in yasan mun sake yaron nan" tace "ai kam ya kamata ku dinga kula waje na Jama'a duk cewa zaiyi wuya a iya sace mutum a nan amman sai a kiyaye" Saleem yy murmushi "Thankiu Sister wlh bakiji yadda gabana ke faduwa b da bamu gansa ba Nagode sosai" tace "bb komi Boi muje kar Daddy su neme mu" ta karisa tana kallon Amaan sallama ta musu suna kara mata godia Khaleel kuwa bayan ta juya yace "Aunty babye" hannu ta daga masa tana daria "Bye handsome" suka koma wajen su Ya Ahmad da sauran yaran
Murmushi yy don tun da ya shigo layin turarukan ya hango ta rike da Dan shi a ranshi yace Oh wannan tana son yara don ko wancan ranan ma da yaron wata mata y ganta gata da alamu ma'abociyar kamshi ce don yauma wajen turare ya ganta sedai ganin tana tafia da yaron yasa ya fara bin bayansu har sanda ta hadu da kannen shi dakuma barinta wajen kafin ya isko su yana fadin "wai me kuka tsaya yi ne har ynx?" Su Afrah da ko nasu kayan basu diba ba sun tsaya biyewa Saleem suka ce "Sorry BB mintuna kadan ynx zamu gama" baiyi mgn ba yabi hanyar da tabi ya koma wajen turarukan daukan abinda yazo dubawa yy ya tafi wajen Cashier ya zauna suna dan taba hira hangota da yy suna zuwa ya saka shi juya baya yau ma kamar dai ranan sbd Ya Ahmad na bayansu yasa ya miko mata katin shi zata mika kenan wani yazo wucewa ya bigeta katin ya fadi bayan t duka ta dauko ne ta bayar suka cire kudin aka musu packaging kayan Amaan ne ya rike nata da nashi sauran yaran kowa na rike da nasa suka fita daga wajen su Saleem ma da suka gama suka kariso suka same shi katinshi ya mika aka cira kudin sukayi gaba
Bayan sun dawo ne ta shige daki don gabatar da Sallan Isha da ya kubuce musu suna hanya bayan ta idar ne ta jawo ledan da Amaan ya shigo mata dashi tana sallah juye kayan tayi don ta cirewa su Ummy nasu da Madam sai ta adana nata din sbd bata son sai gobe ta tsaya harhada kaya so take ya zama komai is ready amma me kwalin Dior Addict ta gani cikin kayan da mamaki ta dago tana dubawa don kam ta tabbayar yau bata dauka ba tunda ta saiwa Yaya ranan ita me zatayi dashi kuma coz ko dazu da taga turaren saida ta tuna ranan da suka kai hannu tare da mai zoben nan to kodai ta dauka ne bata sani b oho koma dai yaya ne ynx kam ai ya wuce so bb yadda zatayi sakawa tayi cikin kayan ta tana cewa "nidai tunda turaren nan yana sona kuma gashi favorite din Yayana ne barin zo in fara amfani dashi kawai shikenan ma idan naje zan dinga tunawa da Yaya idan naji kamshin" kwashe nasu Ummy tayi ta fito falon nan ta samu su Ayman suna ta faman shan Ice cream da suka siyo itama bude fridge din dake falon tayi ta dauko nata tazo tana sha bayan ta baiwa su Madam kayansu suna 'yan hirarrakin su har wajen goma lkcn kam yaran duk sunyi bacci itama Ya Ahmad yace taje ta kwanta tunda gobe bb baccin safe don 10 a Airport zatai musu don haka ta musu saida safe ta wuce bayan tayi wanka da alwalar bacci ne tadau wayarta ta kira Deela suka danyi mgn kafin suyi sallama sai sun hadu a Airport goben tayi addu'ointa na bacci ta kwanta .......
Sauke su kawai yy a gida yadauki abinci da Momma ta zuba masa a food flask ya kama hanyar gida don Khaleel yace wajen Aunty Li zai kwana
Yana fita Afreen tace "Hmm Momma yau da mun bani a wajen BB fa" tayi daria tasan Afreen da zuzuta abu "mai kuka yi?" Afrah ta karbe "Momma ina agogon da muka gani wajen yaron Hajian Dorayi ranar bikinshi?to shine muka ganshi a SUFI sai muka tsaya mgn ashe Broda ya sauke Little Pa bai sani b shine kawai yaron nan ya kama hanya yy gaba" Momma ta zaro idanu "kuce d kun batar min da dan jikalle na yau da kunci gidanku a garin Kano" Saleem yace "Hmm ai nine ma abin tausayin wlh don ni za'a fi ganin laifi tunda ni na ajesa" "to ya akayi har kuka sameshi Habiby bai sani ba?" Little tace "Wlh Momma wata Aunty mai kirki ce ta kawo mana shi" Momma tace "kai to ta kyauta an kuwa gode mata don da watace barinsa zatayi ta cigaba d abinda ya kawota" suka cigaba da tattaunawa kan batun
Yana shiga falon bata ko amsa masa Sallama ba bare sannu da zuwa ta fara fadin "Ina Khaleel?" Don tabbatar da abinda take tunani cikin takaici yace "yana gida yace chan zai kwana" ta wani bata rai "to kuma sai ka barshi kasan dai banson yana yawon yawace²n nan fa gaskia" sarai ya gane cewa gidansun ne bata son yana zuwa shiyasa take hakan lallai matar nan tana shirin kaishi bango ta maidashi wani sakarai sbd yana mata shiru ga duk abubuwan da take yiwa 'yan uwansa wanda sai bayan ya dawo yaji su kaff wajen Momma don daa batayi niyyar fada masa b amma da y takura shine ta sanar dashi wanda shi sam bai taba sanin ma tana hakan b
Matsowa ta sake yi "kana fa ji ina mgn amma kamin banza ko?"
"To Meenah duk fitan da su Zeenat(kannenta) sukeyi dashi da kuma Umma dake daukar shi har zuwa Kasuwa wato ba yawo bane gidanmu ne kawae yawo ko" ganin ya ganota sai tadan sassauta murya tare d sakin fuskar ta "ni fa Honey b haka nake nufi b ya zaka chanza min mgn kuma nifa gani nayi kwana biyu baijin dadi shiyasa nayi mgn fa" baice komi ba ya zauna ya bude abincin shi ya fara ci ji tayi tana son ci amma bakin hali da kuma kin wanda ta girka yasa ba zataci ba taci gaba da hadiyar yawu a haka har ya gama abinda yake ya mike y shige bayi d kanshi y hada ma kansa ruwa yy wanka ya fito sai d ya gama daily routine dinshi kafin ya kwantaAsuba ta gari BB Honeyn Meenah(Lol)
Saura inji bakin wata kan Meenah ta
#Smarty💞

YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...